Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
2 / total: 22

Bangare Na I - Karyata Darwiniyanci

Gabatarwa - Menene yasa akayi Ka'idar Halitta?

Ga wasu mutane, zatonsu ka’idar juyin halitta ko ‘Darwiniyanci’ yana dauke ne da wasu ma`anoni da suka shafi kimiyya ne kawai, suna ganin bashi da wata alaka ko dangantaka da rayuwarsu ta yau da kullum. Hakika wannan shine fahimta karkatacciya wadda tafi shahara.Ya zarce duk inda tunani ya kai akan cewa ya shafi kimiyya ne, sai dai ita ka`idar tana kunshe da dabaibayin mayaudaran falsafawa wadanda suka tafi da tunanin mutane da yawa: wato akan jari-hujja.

Falsafawan jari-hujja, wadanda suka yarda da samuwar tarin kwayoyin halitta, kuma suka fadi cewar wai mutum ya samo asali ne daga tarin wadannan kwayoyi,har ma suka shelanta cewa,mutum ba komai bane illa dabba,tare da rikicin da shine ma sanadiyyar samuwarsa .Koda yake sun yada cewar wata hanyar ilmantarwa ce ta zamani akan falsafar kimiyya,alhali ari-hujja wani abu dadadde da bashi da asali a kimiyya. Fahimtar Girkawan Da, da imaninsu akai shine yasa maguzawan falsafawa na karni goma sha takwas suka farfado da ita kuma suka raya ta.Daga baya aka sake dasa ta a cikin karni na goma sha tara,ta bangarorin kimiyya daga wasu masu bautar tunani,kamarsu Karl Marx, Charles Darwin, da Sigmund Freud.Ma iya cewa kimiyya,an hargitsa tane don a samu kafar da za`a shigo da jari-hujja.

das kapital, marks karl marks, das kapital

Karl Marx ya fada a bayyane cewa ka`idar Darwin itace ta bawa jari-hujja da Kwaminisanci DAS KAPITAL gindin zama.Ya kuma nuna tausayawa ga Darwin KARL MARX da ya sadaukar da Das Kapital a matsayin shine mafi girman aiki a wajensa. A cikin littafinsa da aka rubuta shi a harshen Jamusanci, yace:"Daga masoyi mai kaskantar da kai zuwa Charles Darwin.”

Karni na biyun da suka wuce,wani zamani ne na jari-hujja.Tafarkai daban-daban da aka kafa akan jari-hujja.Tafarkai dabam-daban da aka kafa akan jari-hujja(wadanda suke karawa da juna,duk da cewa sun samo asali guda)sun kawowa duniya dawwamamman yaki,rigingimu,rudani,da hayaniya.Gurguzu kuwa ya jawo sanadiyyar kisan mutane miliyan dari da ashirin,dama shine ribar kusa-kusa da ake samu ko falsafar jari-hujja ke haifarwa.Mulkin kama karya kuwa,duk da cewar suna fakewa da cewa ai shine kadai zai kawo canji a duniyar jari-hujja,amma a ganinsu,zai samu karbuwa duk da halin dar-dar da ake ciki,wanda yake fitowa daga mulkin zalunci,kisan kiyashi da sauran ta`addanci da yakin duniya da ya haifar.

Bayan wadannan kazaman tafarkan nasu, rayuwar mutane dai-daikunsu da haduwar zamantakewarsu, ta gurbace da taimakon jari-hujja.

Gurbataccen sakon jari-hujja,da rage darajar mutum zuwa matsayin dabba da kasancewarsa kwasam kuma ba tare da danganta halittarsa izuwa wani abu ba,ya rushe dukkanin ginshikai na dabi`a kamar soyayya, jinkai, gafara sadaukar da kai, tausayi, gaskiya da adalci.Bayan `yan jari-hujja sun batar da mutane da takensu "rayuwa dai kwazo ce" mutane suka zo suka ga rayuwarsu ba komai bace illa karo da ra`ayoyi wanda shine ya jawo rayuwa ta zamo kamar rayuwar dabbobi,wato mai karfi ya danne mara karfi.

Gano asalin wannan falsafar, wadda take da tambayoyi da yawa da zata amsa dangane da annobar da dan Adam ya jawo a karni biyun da suka wuce, za`a iya gani a cikin kowace akida da kuma fahimta a cikin al`umomi, a matsayin dalili ga rikici ko sabani.Ya hada har da `yan ta`adda na yau wadanda suke cewar wai riko da addini suke, kuma suke aikata babban zunubi, wajen kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Ka`idar juyin halitta ko Darwiniyanci, yazo ne a yanzu don ya cike gurbin almara.Ya bayyanar da cewa jari-hujja wata fahimta ce a kimiyya.Shine yasa Karl Marx, uban kwaminisanci da tsantsar jari-hujja ya rubuta cewar Darwinism shine "asali mai tabbataccen tarihi akan ra`ayoyinsa."1

Babu shakka, wannan asali rubabbe ne. Domin bincike na kimiyyar zamani ya tabbatar, lokaci bayan lokaci cewar shahararriyar yarda dake da alaka da darwinism da kimiyya karya ce.Kuma hujjojin kimiyya sunci karo da Darwinsm da bayyana cewa asalin halittarmu ba wai juyin halitta ba ne, sai dai Ubangiji shine ya halicci duniya, dukkan wani mai rai da kuma mutum.

An rubuta wannan littafi ne don a tabbatarwa da mutane akan sanin haka.Tun lokacin da aka rubuta shi,asalinsa a harshen Turkawa ne, sannan a kasashe da dama ,miliyoyin mutane sun gamsu da littafin.Kari akan harshen Turkawa,an fassara shi da Turanci, Italiyanci, Sifananci, Rashanci, Bosniyanci, Larabci, harshen Malay da Indonesia. (Wannan littafi yana nan a wadace, kuma kyauta a kowane harshe da aka ambata a hanyar sadarwa ta internet,www.evolutiondeceit .com).

Tasirin littafin 'The Evolution Deceit' wato 'Rudun Juyin Halittai' ya bayyana a cikin ra`ayoyin ma`abota yaki da sabani cikin wannan ra`ayi. Harun Yahya ya zamo wani abin tattaunawa a tsarar rubuce-rubucen sabuwar kimiyya wadda ake kira "Burning Darwin"-"Rushe Darwin".Wannan shararran jagoranci akan dakusar da ra`ayin Darwin, lokaci bayan lokaci da ya bayyana a ranar 22 ga watan Afrilu 2000 cewar dai Harun Yahya "wani gwarzo ne na duniya" wanda littattafansa sun yadu ko`ina a duniyar musulunci.

Kimiyya, itace ke jan ragamar dukkan wata al`umma mai tafiya da tsarin kimiyya, sun sami tasiri da gamsuwa a ayyukan Harun Yahya. Wani littafi na kimiyya "Creationism Takes Root Where Europe Meet",wanda aka buga shi ranar 18 ga watan Mayu 2001, an lura a kasar turkey, " Ingattattuun littattafai kamar su 'The evolution deceit' da kuma 'The Dark Face of Darwinism. Sun samu karbuwa fiye da duk wasu littattafai a wasu bangarori na kasar." Mai rahoton yaci gaba da bayani akan ayyukan Harun Yahya cewar, "yana daya daga cikin abokan adawar da yafi kowanne karfi a duniya akan evolution, wanda ba a Amurka ta Arewa yake ba."

Koda yake sun riski kalubale na "The Evolution Deceit," amma basu bada wata amsa a kimiyance da zata yi karo da mahawarorin da marubucin ya kawo ba.Dalili kuwa shine,ba abu ne mai sauki ba. Magana ta gaskiya itace, evolution yazo karshe,kuma dalili ne da zaka gani a yayin da kake karanta babukan wannan littafi.Littafin zai taimaka maka ka fahimci cewa Darwiniyanci ba ka`ida ce ta kimiyya ba,amma wani hasashe ne na kimiyya dauke da yaudarar addini,duk kokarin kawo dalilai da hujjoji,da karin girma ne don kare falsafar jari-hujja.

Fatanmu ne ace "Rudun Juyin Halitta" ya dade yana bada gudunmawarsa ta wayar da kai akan rudun da Charles Darwin ya kawo wanda ya dade yana batar da mutane tun daga karni na sha tara (19th century).Kuma ya tunasar da mutane akan gaskiyar al`amarin rayuwarsu, kamar yadda su kazo duniya (ma`ana halittarsu) da kuma nauyin da kansu a wajen bautar Ubangijinmu.

 

Footnotes

1. Cliff, Conner, "Evolution vs. Creationism: In Defense of Scientific Thinking", International Socialist Review (Monthly Magazine Supplement to the Militant), November 1980.

2 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top