Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
3 / total: 22

Babi Na 1 - Kubuta Daga Son Zuciya

Mutane da yawa sukan yarda da duk abinda suka ji daga wurin ma`abota kimiyya a matsayin tsantsar gaskiya. Basa dauka cewar suma suna da wata fahimta ta falsafa ko akida ta son zuciya.Magana ta gaskiya itace masana kimiyyar juyin halitta sune suka cusa son zuciyarsu da ra`ayoyinsu na falsafa akan mutane, suna fakewa da sunan kimyya. Misali, koda yake sun sani cewar kwayoyin halitta wadanda suke juyawa ta ko`ina ba sa jawo komai sai karkacewar tsari da rudani, kuma duk da haka suke da`awar cewa kyakkyawan tsari, shiri da adon da ka iya gani a fadin duniya da kuma halittu sun samu haka nan.

Misali, ka ga masani akan halittu zai iya fahimtar akwai babban gibi a haduwar abubuwan gina jiki kuma babu tabbacin cewar sun samu ne haka nan. Koda yake, yayi zargin wai abubuwan gina jiki sun wanzu ne ta yanayin duniya dadadde kuma haka nan,shhekaru biliyoyi da suka wuce. Bai tsaya anan ba,ya cigaba da cewa,ba tare da damuwa ba, kuma ba daya ba,amma miliyoyin kwayoyin gina jiki ne suka hadu suka zama abu guda, har suka wuce. Bai tsaya anan ba,amma miliyoyin kwayoyin gina jiki ne suka hadu suka zama abu guda,har suka zama farkon abin halitta. Dada, ya kare ra`ayinsa da wani shurbataccen dalili. Wannan mutumin fa “ma`abocin kimiyyar juyin halitta ne.”

Idan da ace zai ga wasu tubalai uku wani yana kan wani, a yanayin da yake tafiya akan hanya,ba zai taba zaton cewa wadannan sun wanzu ne haka nan har daya ya hau kan daya ba,duk dai haka nan. Hakika, duk wanda yayi zaton haka lallai zai zama mara hankali.

Ta yaya zai zamanto mutanen da suke iya lura da abubuwan da suke faruwa gaba garesu su yarda da wani tunani akan hakikanin samuwarsu?

Babu tababa ayi da`awar wannan halayya ta samu ne da sunan kimiyya; ita kuwa fuskantar kimiyya tana daukar hanyoyi biyu ne, wato idan har akwai tafarkai guda biyu,masu nauyin hujjoji daya akan wani abu. Amma idan har a cikin dayan biyun hujjojin akwai mai raunin hujja, misali koda ya yakasance dayan ya dara da digo guda ne,to a kimiyance, wancan shine daidai.

Bari mu cigaba, tare da barin wannan hadafi a ranmu.Akwai ra`ayoyi biyu wadanda za`a iya sawa a gaba akan yadda halittu suka samu a duniya.Na farko dai, Ubangiji shine ya halicci dukkan halittu a yanayin da suke. Na biyu kuwa, halittu sun samu ne ta hanyar haduwar wasu kwayoytin halitta mabanbanta a cakude. Wannan itace da`awar ka`dar juyin halitta.

Idan muka dubi dalilai na kimiyya, babu yadda za`ayi ace wai kwayar halitta ko dayan miliyoyin kwayoyin gina jiki wadanda suke cikin kwayar halitta-zasu wanzu ne haka nan ba tare da an halicce su ba, kamar yadda suke da`awa.Kuma kamar yadda zamu nuna a babika masu zuwa, kididdiga mai yiwuwa ma ta tabbatar da hakan, sau da yawa. Saboda haka, ra`ayin ma`abota juyin halitta babu gaskiya ko ta kwabo a cikinsa.

Wannan shi yake nuna mana cewa ra`ayin farko yana da tabbacin gaskiya “dari bisa dari”.Wato,halittar rayuwa akai.Dukkanin halittu sun wanzu ne daga kirkirar kasaitaccen Mahalicci,mai wadataccen iko,hikima da sani.Wannan gaskiya ba wata aba ce mai wuya ba,illa kawai shine abinda hikima,tunani da kimiyya zata kai mutum.

A cikin wannan hali, masananmu na kimiyyar evolution sun ka sa wurgi da da`awarsu su kama gaskiyar da aka tabbatar.Kin yin haka shi yake nuna cewar da ya zama masanin kimiyya na gaskiya gara ya sadaukar da kimiyyarsa da fakewa da falsafar, akida da ra`ayoyin da babu koyarwar addini a ciki.

Fushi, gagara da son zuciyar masana kimiyyarmu na karuwa a duk lokacin da aka fuskanceshi da gaskiya.Za`a iya bayyana halayyarsa a kalma guda: “Imani”.Koda yake gurbataccen imani ne, tunda babu wani gamsashshen bayanin da zai nuna halim ko-in kula akan hujjoji ko kuma dadadden has ashen tunani wanda ya shirya.

Makauniyar Jari-hujja

bilim adamı, michale behe

Michael Behe:"An embarrased silence surrounds the stark complexity of the cell"

Imanin da muke magana akai shine falsafar jari-hujja, wadda suka yi kalubale cewa wai kwayoyin halitta sune a farkon komai.Ka`idar evolution itace ai “tushen kimiyya” ta falsafar jari-hujja kuma suke kokarin kare ta a makance don suyi riko da wannan falsafar.Yayin da kimiyya ta rushe da`awar evolution-wannan itace gabar da aka cimma anan,a karshen karni na ashirin-sannan sai aka yi kokarin hargitsa abin don akai wani matsayi da za`a marawa evolution baya saboda jari-hujja ya rayu.

Sudurori kadan din da wani shararran masanin kimiyyar evolution a kasar Turkey misali ne mai kyau da zai iya nuna mana irin karkataccen hukunci da son zuciyar da wannan makauniyar hanya take kaiwa. Masana kimiyya sun bayyana yiyuwar samar da Cytochrome-C, wanda daya ne daga cikin kwayoyin halittar dake ciyar da rayuwa gaba, kamar haka;

Yiwuwar samar da cytochrome-c wato abu ne mai kamar wuya.Wato yana bukatar matakai,za`a iya cewa akwai yiyuwar samar da kwaya daya a duk fadin duniya.Idan ba haka ba, wadansu sashe na karfi sama da abinda muka fassara ya rigaya ya aiwatar da samuwarsa.Yarda da wannan zance na biyu ba abu ne karbabbe ba daga manufofin kimiyya.Saboda haka dole ne mu koma bayaninmu na farko.2

Masanin kimiyyar ya sameta "mafi kimiyya" da yarda da yiyuwar "abu mai kamar wuya" a maimakon halitta.Bayan haka a tsarin ka`idojin kimiyya.Idan akwai bayanai na zabi guda biyu dangane da faruwar wani abu kuma idan daya daga cikinsu babu kanshin gaskiya,to dayan shine yafi karbuwa.Haka kuma mummunar akidar jari-hujja ta haramta yarda da mafificin halitta,wannan haramtawa ta kai wadannan masana kimiyyar da wadansunsu da yawa wadanda sukai imani akan dai wannan akida ta jari-hujja da su amince da wannan da`awa wadda ta sabawa hankali da tunani.

Mutanen da suka yi imani da yarda da wadannan masana sun samu kansu cikin dimuwa da rashin ganewa daga wadannan zantuttukan jari-hujja kuma suka dabbaka wannan rashin tunani a yayin da suke karanta littattafansu da kasidunsu.

Wannan akida da ra`ayin `yan jari-hujja shine dalilin da yasa sanannun masana a cikin al`ummar masana kimiyya duk suka zama mushrikai.Wadanda kuma suka kubuta daga wadannan zantuttuka suka yi tunani da budaddiyar zuciya basu gushe ba suna yarda da samuwar mahalicci.Wani Ba Amirke masanin hada magunguna Dr. Micheal J. Behe, daya daga cikin masana wadanda suka marawa

ka`idar “kyakkyawan tsari” baya, kuma ta samu karbuwa sosai daga baya, ya bayyana irin rikon da masana kimiyya suka yi akan yarda da “tsari” ko “halitta” na rassan gabban halitta kamar haka:

Shekaru arba`in da suka shude, ilmin hada magunguna na zamani ya bude sirrikan kwayar halitta (cell).Tana bukatar dubban mutanen da zasu sadaukar da rayuwarsu akan wannan muhimmin aiki a dakin gwaje-gwaje…Sakamakon wadannan kokari na bincike game da kwayar halitta-da bincike akan rayuwa a matakin kwayoyin halitta-abu ne sananne,a bayyane mawahalcin “tsari!”.Sakamakon ba mai wuya bane kuma gashi Micheal Behe: da muhimmancin da dole ne a saka shi ya zama daya daga cikin “Abin kunyar da ya manyan tarihin kimiyya…Sai dai ya zama mai wahala, kuma kewaye hadaddun abin kunyar da ya kewaye hadaddun kwayoyin halitta.Menene kwayoyin halitta.” ya sa dandazon ma`abota kimiyya basu rungumi bayyanar gano tafarkin ba? Me yasa wajen lura da tsari aka yi amfani da tafiyar dashi? Takaddamar da ake itace wato kwibi daya na Giwa zai zama ana danganta shi da kyakyawan tsari,daya kwibin kuma dole a danganta halittarsa izuwa Allah.3

Wannan shine yanayi mara dadi ga mushrikai ma`abota kimyyar evolution da kuka gani a mujallu da talabijin da littattafansu ma wadanda watakila kuke karantawa. Dukkanin bincikensu a kimiyance ya tabbatar musu da cewa akwai mahalicci. Duk da haka sun kurumce da makancewa da yaudarar jari-hujja wadda sukai ilmi akanta,ta hana su har yanzu sun ka sa fahimta.

bilim adamı, richard dawkins

Richard Dawkins, ya shagala da yada juyin halitta

Mutanen da kiri-kiri suka yi watsi da alamomi bayyanannu da hujjojin dake tabbatar da samuwar mahalicci lallai basu da hankali.Sun samu kansu cikin jahilci da rashin hankalin da suka jawowa kansu,zasu iya karewa a marawa karya baya kamar gaske.Ga kyakkyawan misali daga kalmomin wani kusa a fagen evolution Richard Dawkins wanda yayi ga kiristoci akan kada su dauka sun ga mu`jiza koda sun ga gunkin Nana Maryamu na dago musu hannu.Dawkins yace, “Watakila dukkanin sunadaran hannun gunkin kawai sun motsa ne ta fuska daya a lokaci guda-abu ne mai karancin yiyuwa,amma zai iya yiyuwa.”4

Tunanin makiya addini ya dade yana wanzuwa a cikin tarihi. A Alkur`ani an bayyana hakan da cewa:

“Kuma da ace,lallai Mu,mun saukar da mala`iku zuwa garesu, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tara dukan kome akansu,gungu-gungu, ba su kasance suna iya yin imani ba,sai fa idan Allah Ya so, kuma amma mafi yawansu suna jahiltar haka.” (Suratul An`am: 111)

Kamar yadda wannan aya ta bayyana, mugun tunanin `yan juyin halittai ba hanyar tunani ce mai kyau ba, bare ma ace su kadai ke da ita ba. Alal hakika abinda masana kimiyyar juyin halitta suka rike ba ma sahihiyar kimiyyar juyin halitta bace, amma wani jahilci ne tun na maguzawan mutanen Da. Wannan dai tunani, kur`ani ya fassara shi a wata ayar da cewa:

“Kuma da Mun bude wata kofa daga sama akansu har suka wuni a ciki suna takawa.Lalle ne da sunce,’Abin sani kawai,an rufe idanuwanmu ne.” (suratul hijr : aya ta 14-15)

Cusawa Mutane yarda da akidar Evolution

icons of evolution, jonathan wells

Icons of Evolution, by Jonathan Wells

Kamar yadda aka bayyana a aya ta sama,daya daga cikin dalilan da yasa mutane ba zasu iya ganin zahirin halittarsu ba wato wani irin dabaibayi ne kalamai da ya kanannade tunaninsu.Wannan ne dai ya jaza wajen karbuwar ka`idar juyin zamani a duniya baki daya.Abinda muke nufi da dabaibayi shine sharadin karbuwar akidar.An yadawa mutane wannan akidar da gasgata ka`idar juyin zamani wanda basu san irin kwamacalar dake ciki ba.

Wannan dabaibayi ya haifar da illar da ta shafi kwakwalwa da raunana tunani .Har ila yau,kwakwalwa wadda take cigaba da karbar sako mai dabaibayi,ta fara karbar sakwanni na hakika ba yadda suke ba amma ta hanyar da akai musu dabaibayi,za`a iya kwatanta wannan da wasu misalai,.Misali,idan aka yiwa mutum rufa ido da dabaibayi don ya yarda da cewar gadon da yake kwance akan mota yake,sai ya zaci gadon a matsayin mota.Yana tunanin cewa wannan zai iya yiyuwa saboda yana kallon abin ta haka,kuma baya kokwanton cewar ba daidai yake ba.Wadannan misalai kamar wannan na sama,wanda ke nuna kokari da ikon kanannadewar dabaibayi, a kimyance an tabbatar dasu da gwaje-gwaje masu yawan gaske wadanda aka rawaito a littattafann koyon kimiyya da ake karantawa kullum a fannin sanin halin mutum da kuma na hankalin mutum.

Wadanda suka dogara da ka`idar juyin halitta da ra`ayoyin jari-hujja sun tursasa su akan talakawa ta hanyar salon dabaibayi.Mutanen da suke ta cin karo da akidar juyin halitta a kafofin watsa labarai, tafarkin karatu mai zurfi, da manufofin kimiyya, sun kasa fahimtar cewa yarda da wannan ka`ida ya sabawa manufofin tunani.Ta wannan hanya ce aka zarge masana kimiyya.Matasa masu tashen suna a fannin nazarin kimiyya sun riki ra`ayoyin jari-hujja, kuma suna yawaita lokaci bayan lokaci.

A dalilin wannan dabaibayi ne,yawancin masana kimiyyar juyin zamani suka tafi neman yarda da hujjojin kimiyyar karni na sha 19 da da`awoyinsu wadanda aka daina amfani dasu kuma hujjojin kimiyya ma sun rushe su.

Akwai wasu Karin tafarkai da suke tursasawa masana kimiyya akan su zama `yan juyin halitta da jari-hujja. A kasashen turawan yamma, masanin kimiyya ba zai taba samun girma ba sai ya taka wasu matakai tukuna, wato ya samu karbuwa a fannin ilmi ko kuma a buga wata kasidarsa a mujallar kimiyya.Yarda ta kai tsaye da zai yiwa juyin halitta shine mataki na farko.Wannan tsari ne yake tafiyar da masanan wajen karar da rayuwarsu akan tabbatar da wannan muguwar akida.Ba Amurken nan masanin kwayoyin halitta Jonathan Wells yai magana akan matsin lambar a littafinsa Icons of Evolution wanda aka buga a shekara ta 2000:

…Masu akidan Darwin sun fara ne da tursasa gajeriyar fahimtarsu akan hujjoji da tabbatar da cewa ita kadaice hanyar zuwa kimiyya. Kalubale akanta na iya zama babu kimyya ciki, kasidunsu basa karbuwa a mujallu, kuma duk wani kalubale ba zai samu tallafi daga wasu rukunonin gwamnati ba, wanda suke turawa don cigaba da raya akidar don yin bita; kuma kalubalenma ana fitar dashi daga tsarar masana kimiyya. Akan haka, dukkan wata hujja ta ra`ayin Darwiniyanci ta fara bata, kamar shaidu akan Mob.Ko hujjojin su zama an killace su a wasu littattafai na musammam, wanda kawai wani mai bincike ne na sadaukar da kai ne zai iya samo su.Ko kaka aka dan sassauta kalubalantar abin da kuma lullube hujjojin da zasu yi karo da ita,sai kaga an shelanta cewa akwai mahawarar kimiyya akan ka`idar,kuma babu wata hujja akan yakar ta.5

Wannan shine hakikanin cigaban al`amarin dake boye da cewar “juyin halitta na karbuwa har yanzu a duniyar kimiyya.”An kyale juyin halitta ya numfasa ne ba don yana da cancantar kimiyya ba amma saboda yana da manufa ce ta akida da ake son a cimma. Kadan ne daga cikin masana kimiyya wadanda suka san haka ke iya nusar da cewar sarkin fa baya sanye da tufafi.

A sauran shafukan wannan littafi, zamu yi bitar binciken kimiyyar zamani akan juyin halitta wadda masana juyin halitta suka ki amincewa dasu ko “killace su a wasu littattafai na musamman,” da suke baje-kolin hujjoji mabayyana akan samuwar Ubangiji. Mai karatu zai shaida cewar ‘evolution theory’ ko ka`idar juyin zamani lallai rudu ne-rudun kimiyya ta karyata a kowane mataki amma aka raya ta don a boye hakikanin halitta.Abinda muke fata ga mai karatu shine farkawa daga dabaibayin da makafin mutanen dake da makafin zukata wadanda suka karar da lokacinsu, kuma yayi izina daga irin abinda za`a rawaita masa a wannan littafi.

Idan ya kubutar da kansa kuma yayi tunani mai kyau, `yantacce, ba tare da son zuciya ba, zai gano gaskiya. Gaskiyar da babu mkimiyyar zamani ta tabbatar ta kowace fuska, cewar kwayoyin halitta sun wanzu ne ba haka nan ba, sai dai a dalilin halittarsu da aka yi.Mutum zai iya saukin ganin haka idan ya dubi halittarsa,yadda yazo duniya dagaruwa,ko kyakkyawar kuma cikakkiyar halittar kowane irin abu mai rai.

 

Footnotes

2 Ali Demirsoy, Kalitim ve Evrim (Inheritance and Evolution), Ankara: Meteksan Publishing Co., 1984, sh. 61.

3 Michael J. Behe, Darwin's Black Box, New York: Free Press, 1996, pp. 232-233.

4 Richard Dawkins, The Blind Watchmaker, London: W. W. Norton, 1986, sh. 159.

5 Jonathan Wells, Icons of Evolution: Science or Myth? Why Much of What We Teach About Evolution is Wrong, Regnery Publishing, 2000, sh. 235-236

3 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top