Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
9 / total: 22

Babi Na 7 - Bayanin Kasusuwan Yaudara

Kafin mu fara mu bayani akan labarin juyin halittar mutum, babu bukatar mu sake komawa kan farfagandar tsarin da ya gamsar da jama'a akan wai rabi mutum - rabi biri sun taba rayuwa a baya. Wannan farfaganda tayi amfani da kalmar "sake gini" wato "reconstructions" dangane da burbushin halitta. Ma’anar kalmar sake gini shine zane-zanen hoto ko gina surar rayayyar halitta akan faletin kashi-wani lokaci ma akan irin tsince-tsincen da aka yi daga cikin kasa. Gwaggwon birin da muke gani mai kama da mutum a jaridu, mujallu ko fina-finai duk zane ne ko surantawa.

java adamı, sahte çizim

Two drawings of Java Man, which are totally different from each other, provide a good example of how fantastically fossils are interpreted by evolutionists.

Tunda yake burbushinsu yawanci ba cikakke bane domin ba'a samun wasu sassan jikinsa, saboda zane dake nuna cikarsa kawai jita-jita ce. Magana ta gaskiya, zane ko surantawar da masanan suke yi akan burbushin ragowarsu sunyi sune domin su goyi da bayanan da suke gabatarwa akan juyin halitta. Wani masanin tarihin mutum daga Harvard, David R. Pilbean ya karfafa wannan hujja da yace "A kalla a fannin ilmin halittar mutum, bayanai masu karfi suna nan wanda babu wata ka'ida da zata iya kokarin canza bayanan. A baya, ka'idoji sun bi tafarkin akidojinmu maimakon hakikanin bayanan."61 Tunda bayanai na gani da ido sunyi tasiri a tunanin mutane, to kuwa zanen ko surantawa sun biya bukatun masana juyin halitta, dama don su gamsar da mutane ne akan lallai halittun sun taba wanzuwa a baya.

A wannan gaba, dole mu tsokaci da cewa: sake sake surantawa akan ragowar kasusuwa zasu iya bayyana abinda kawai ke jikin kashi ne, tunda ana yinsu ne a jikin tattausan kashin da wani lokaci zai bace nan da nan. Saboda haka, jita-jitar da suke fada dangane da tattausan kashin, zanen ko surantawa da suka yi zai dogara ne akan hasashen wanda ya kirikiro su. Earnest A. Hooten shima daga jami'ar Harvard, yayi bayani akan wannan lamari:

Yunkuirn cike gurbin tausasan gabobi wani gagarumin aiki ne. Labba, idanu, kunnuwa, da karan hanci basu nuna fitar kasusuwan jikinsu ba. Kana iya ganin samfurinsu a kwarangwal din Neanderthaloid, siffofin gwaggwon biri ko zanen hoton fuskar da wani masanin falsafa yayi. Wadannan zane-zanen karyar da suke suranta dadaddun nau'ukan mutum suna da kankanuwar kima a kimiyance idan ma akwai kuma ana yin sune don a yaudari jama'a...saboda haka kada ku yarda da zane-zanensu.62

Zane-Zane Daban - Daban Guda Uku Akan Kwarangwal Daya
kafatası, sahte çizimler

Ya bayyana a Jaridar Sunday Zanen Maurice Wilson Zanen

N. Parker N. Geographic

Times 5 ga Afrilu, 1964 Satumba 1960

A hakikanin gaskiya, masanan sun kirkiro "shiryayyun tatsunoyoyi" ne kuma suka samar da fuskoki iri-iri akan kwarangwal daya. Misali, wadannan zane guda uku da suka yi akan burbushin halitta mai suna Australopithecus robustus (Zinjanthropus), wani shahararren misali ne akan zane-zanensu na jabu.

Bayanan da suke yi akan zane-zanensu na son zuciya ko kirkirar surar halittu zai iya zama wata alama ce dake nuna yadda masanan suka yi nisa wajen kirkirar dabaru. Duk da haka zai zamanto kankani idan an kwantanta da zane-zanen jabun da aka yi a tarihin ka'idar juyin halitta.

 

Kirkirar Zanen Karya
lucy ailesi, sahte çizimler
evrim, hayali çizim
evrim, hayali çizim

Geheimnisse Der Urzeit, Tiereund Menschen, s. 200

National Geographic, March 1996

A hotuna da zane-zane, masana suna sane suka gabatar da wasu sifofin da babu wata alamar samuwar burbushinsu, kamar yadda siffar hanci da labba, sifar gashin, shatar ido, da yadda gashi ya baibaye jikinsu don dai su tabbatar da juyin alitta. Suka shirya wasu hotuna da suke nuna irin wannan halittau suna tafiya tare da iyalinsu, gashi suna farauta, ko wasu shafuka da suke gabatar da rayuwarsu ta yau da kullum. Bayan haka, wadannan zane-zane ba komai bane illa kirkirensu wanda bashi da nasaba a daftarin burbushin halitta.

 

Footnotes

61. David Pilbeam, "Rearranging Our Family Tree", Nature, Haziran 1978, s. 40

62. Earnest A. Hooton, Up From The Ape, New York: McMillan, 1931, s. 332

9 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top