Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
14 / total: 22

Babi Na 12 - Tsari Da Kicibis

A babukan da suka gabata, mun ga yadda rashin yiwuwar samar da rayuwa kwatsam yake. Bari mu suke yarda da wadannan rashin dan kadan. Mu dauka cewa shekaru miliyoyi barkatai da suka shude ne kwayar halitta ta samu dukkanin sunadaran rayuwa kuma sai “rayuwa ta samu”. Daga nan ne kuma juyin halitta ya rushe. Idan da ace kwayar halittar ta cigaba da rayuwa, da kuwa lokacin mutuwarta yayi kuma bayan mutuwar, babu abinda zai yi saura sannan komai zai kome inda ya fara. Domin kwayar halittar farko, ta rasa bayanai na halitta saboda haka ba zata kasance tana samar da sababbin halittu ba. Da rayuwa ta kare saboda mutuwarta.

Tsarin halitta ba wai kawai yana dauke ne da jigidar halittar DNA ba. Sai an samu wadansu daga wadannan masu zuwa: sunadaran da zasu tsakace jigidar DNA, bayan karantar wadannan mukullai jigidar RNA zata samu, wata tattarace wadda akanta jigidar RNA zata rika rafiya tana aika sako, ta nanne za’a samu mukullan da samar da sunadarai, canza RNA don ta canza zuwa sunadarin amino acids zuwa wannan tattara do yin amfani wajen samar da sunadarai, da dogwayen cakuduwar sunadaran da zasu samar da tsaka – tsakin tsari. Wannan muhalli fa ba zai samu a ko’ina ba sai dai kawai a taskataccen wuri kuma muhallin da yake samun kulawa kamar kwayar halitta, inda duk sunadaran da ake bukata da kuzari suke.

A sakamakon haka ne, sunadaran da suke tattare da halitta zasu iya cigaba da samuwa idan sun samu cikakken tsarin da muhalli da ya dace dashi, yayi musayar kayan aiki, da samun kuzari daga kewayanta. Wannan yana nufin cewa tantanin halittar da ya fara samuwa a duniya ya samu ne “kwatsam” tare de cikakkiyar siffarsa.

Saboda haka, idan cikakkiyar sifa zata samu kwatsam, me ake nufi da haka?

Bari muyi wannan tambaya tare da misali. Bari mu kamanta tantanin halittar zuwa ga mota mai girman fasahar kira saboda cikarta. (A hakika, tantanin halitta ya kunshi tarin abubuwa masu yawa da ingataccen tsari fiye da mota da irin kayan jikinta.) Yanzu bari muyi tambayar: yaya zaka ji idan kana tafiya da kafa a kungurmin daji can sai ka hango mota ajiye jikin bishiyoyi? Shin zake yi tunanin cewa bangarori da dame dage cikin wannan dajin ne sama da shekaru miliyoyi ne suka hadu suka samar da wannan mota? Dukkan abubuwan da aka head wajen samar da motar sun fito ne daga karfe, danko, roba, kasa ko abinda aka sane’anta daga gareta, amma wannan hujja zata saka ke tunanin cewa wadannan sun hadu “kwatsam” wuri guda sai suka zama mota?

Babu shakka, duk wanda yake da lafiyayyar zuciya ya san cewa mota dai wani mekeri ne ya kera to, ma’ana a masana’anta, kuma zai yi mamekin abinda motar take yi a tsakiyar dokar daji. Bayyanar abu kwatsam a cikakkiyar sifa na nune cewa lallai akwai maheliccin wannan abu. Cikakken tsarin halitta kamar kwayar halitta babu shakka halittaciye ce daga iko madaukaki mai cikar hikima. A wasu kalmomin, ta wanzu daga halittar Ubangiji.

Yarda da cewa halitta ne iya semuwa kwatsam, lallai juyin halitta ya ketare shingen hankali da kimiyya. Daya daga cikin masu fada aji a wannan fage shine shehararren masanin dabbobi dan kasar France Pierre Grasse’, tsohon shugaban cikbiyar kimiyya ta France. Grasse dai dan jari hujja ne, amma ya fito ya tabbatar da cewa Darwiniyanci ya kasa bayanin asalin rayuwa kuma ya fadi ra’ayinsa akan hikimar kalmar “kwatsam”, wadda itace kashin bayan Darwiniyanci:

Sa’ar bayyanar maye gurbi dake kyale dabbobi da tsirrai su samu bukatunsu me ganin abu ne mai wuyar gasgatawa. Duk da haka ka’idar Darwin aba ce mai yawan bukatu: kadaitaccen tsiri, dabba daya zata bukaci dubban sa’a, a lokaci daban-daban. Saboda haka, mu’jiza ce zata zama ka’ida: duk abinda yake tattare da karfin iko ba zai gushe ba sai ya faru … Babu wata ka’ida dake hana mafarkin rana, amma kada kimiyya ta shiga ciki. 147

Grasse ya takaice abinda kalmar “kwatsam” take nufi ga masana juyin halitta: “… kwatsam ta zama wata hanya ce, wadda, a karkeshin kariyar magazanci, bata da suna amma ita ake bautawa a boye”. 148

Faduwar tunanin masanan wani sakamako ne na bautar ilmin kwatsam. a alkur’ani, an rubuta cewar wadanda suke bautawa wanin Allah sune marasa fahimta;

Suna da zukata, basu fahimta dasu, kuma suna da idanu, basu gani dasu, kuma suna da kunnuwa, basu ji dasu: wadancan kamar bisashe suke. A’a, sune mafi bacewa: wadancan sune gafalallu. (Suratul A’araf: 179)

Fomular Darwin!

Bayan dukkanin shaidun da muka gabatar tun a farko, bari sau daya yanzu muyi nazarin irin camfin da masanan suke fada ma wanda yaro karami na iya fahimtar misalinsa:

Ka’idar juyin halitta ta riki cewa rayuwa ta samu ne kwatsam. Kamar yadda wannan da’awa tace, matattun tarwatsatstsun kwayoyin halitta ne suka hadu wuri daya don samar da tantanin halitta kuma daga nanne sai suka samar da wasu rayayyun halittun, kamarsu mutum. Bari muyi tunani akan wannan. Idan muka hada sunadaran da suke gina rayuwa kamar carbon, phosphorous, nitrogen da potassium, ya zama kenan curi daya ya samu. Duk irin abinda za’a mayar dasu, wadannan sunadarai ba zasu taba samar da komai kankantar halitta rayayya ba. Idan kaso, bari mu shirya maka “gwaji” akansa kuma ka bari mu jarraba shi a maimakon masanan da abinda suke da’awa ba tare da sun fito da babbar murya sun fadi cewa “Fomular Darwin” bace:

Bari ma ace masanan sun zuba adadi mai yawa na sunadaran da suke cikin halittu masu rai kamarsu phosphorus, nitrogen, carbon, oxygen, iron, da magnesium a cikin babbar garwa. Haka kuma, ace su kara a cikin wadannan garewani dukkan wani abu da baya samuwa a yanayi mai kyau, amma suyi tunanin yiwuwarsa. Ace su kara a cikinsu sunadarun amino acid mai yawa – wanda babu yiwuwar samuwarsa ta hanyar yanayi mai kyan – kuma kamar sauran sunadaran gina jiki – da yiwuwar samuwar guda daya daga kashi 10-950 – kamar yadda suke so. Ace su sanya musu wuta don su hade yadda suke so. Ace su sanya a kusa dasu masana kimiyya. Ace wadannan kwararru su tsaya gabansu, shekaru biliyoyi da dubban biliyoyi. Ace su samu damar amfani da duk wani irin yanayin da suka yarda zai iya samar da mutum. Duk irin abinda zasu yi, ba zasu taba iya samar da mutum daga cikin garewanin ba, ace ma farfesa yayi nazarin sifar tantanin halitta ta na’urar hange. Ba zasu iya samar de Barewa, zakuna, kudan zuma, kanari, dawakai, kifaye manya, fure, bishiya mai furanni, ayaba, lemo, tufa, dabino tumatur, kankana, zaitun, inabi, mallam buda littafi, ko miliyoyin halittu rayayyu kamar wadannan. Hakika, ba zasu iya samar da mafi kankantar tantanin halitta a cikinsu ba.

A takaice, tarin kwayoyin halitta ba zasu iya samar da tantanin halitta ba ta hanyar haduwa da juna. Ba zasu iya daukar sabuwar shawara kuma su kasa ta biyu, sannan ya dauki waccan shawarar kuma a halicci farfesan da ya fara kawo su a karkashin zanen halitta a na’urar hange. Kwayoyin halitta, tulin matattun curi ne, kuma ta rayu ne da buwayar ikon halittar Ubangiji ne.

Kai’idar juyin halitta, wadda tayi da’awar sabanin haka, shirme kawai da sabawa hankali. Tunanin kadai akan wadannan da’awowin masana juyin halitta ta fito da hakikanin gaskiya, kamar yadda yazo a misalin daya gabata.

varil, canlılığın kökeni varil, canlılığın kökeni

Even if evolutionists placed all the substances necessary for life in a barrel and applied to them whatever processes they chose, involving all the scientists in the world in this experiment and waiting for billions of years, they would never be able to form a single living thing inside that barrel—nor even a single cell of a living thing.

Fasaha dake cikin Ido da kunne

Wata matsala data rage ba’a amsa ta a ka’idar juyin halitta ba itace kyakkyawan tsinkaye a cikin ido da kunne.

Kafin mu shiga magane akan gaba ta ido, bari mu amsa tambaya a takaice akan “yadda muke gani”. Hasken da yake tahowa daga abin gani kume ya fada cikin kwayar ido. Anan, wannan haske ana aikasu a sifar na’urar sakonni su isa zuwa wani kankanin wuri a bayan kwakwalwa mai suna cibiyar maganai. Wadannen na’urar sakonni ana tsinkayarsu a kwakwalwa a matsayin hoto bayan wani zangon tafiya. Tare de wannan share fage, bari muyi wasu tunani.

Kwakwalwa na karbar sako ne daga haske. Ma’ana cewa cikin kwakwalwa duhu gareshi, kuma hasken baya zuwa inda kwakwalwar take. Cibiyar maganan wuri ne mai duhu inda haske bai taba zuwa wurin ba; duhunsa zai iya yiwuwa duhu ne wanda baka taba tsammani ba. Duk da haka, kana ganin ado, hasken duniya daga wannan bigire mai duhu.

Hoton da zai baka tarwai yake wanda ko fasahar karni na 20 bata iya kaiwa nan ba. Misali, kalli littafin da kake karantawa, kalli hannunka da kake rike dashi, sannan daga kanka ka kalli ko’ina. Ka taba ganin wata irin na’urar bada hoto a ko’ina data taba baka irin haka? Koda mafi keruwar talabijin wanda mafi fasahar iya samar da ita a duniya ba zai iya samar maka da irinsa ba. Wannan shine tafarkai uku, launi cikakke, hoto tarwai. Sama da shekara dari (100), dubban injiniyoyi sun yi kokarin samar da haka. Anyi manyan gine-ginen masana’antun hotuna da zane-zane da dakunan bincike akan wannan. Haka kuma, kalli fuskar talabijin kuma kalli littafin dake hannunka. Zaka ga akwai bambanci mai yawa wajen fitar da hoto. Bayan haka, fuskar talabiyin zata baka hoto ne ta fuska biyu, bayan idanke kuwa ta fuska uku zai baka. Idan ka duba sosai, zaka lura akwai a cikin talabijin din, shin akwai wannan a ganinka?Tabbas babu.

Shekaru masu yawa, dubban injiniyoyi sunyi kokari su kara talabijin mai fuska ukun amma taki yiwuwar kallo ba tare da gilashi ba; haka kuma, kirar mutum ce. Fuskar tana rawa, zaka ga kamar takarda a shinfide. Ba’a taba samun saukin sarrafa hakan ba, sabanin ido ne. A camera da talabijin, akwai rashin igancin hoto.

Masanan sunyi da’awar cewa maganadisun dake samar da hoton shima ya samu ne kwatsam. Yanzu, idan wani ya fada maka cewa talabijin din dake dakinka ta samu kwatsam, yace maka dukkanin sassan jikinta sun hada jikinsu sai kawai ta zama mai bada hoto, yaya zaka ji? Shin yaya kwayoyin halitta za suyi abinda dubban mutane ba zasu iya ba.

Kusan karni guda, dubban injiniyoyi sun yi iya kokarinsu don ganin sun samar da wani mafi cikar fasaha a dakin na’urorinsu akan su kera, amma ba suyi sama da wannan ba.

göz, 3 boyutlu göz modeli  kamera, görüntü
kulak, biyoloji  ses, muzik çalar

Idan muka kwatanta kunne da ido da camera da kuma radiyo, zamu ga cewa ido da kunne suna da hadadiyar sifa, aikinsu, yafi na wadancan kayan

Idan akwai wani abinda zai iya fitar da hoto sama da ido to kuwa bai zama ya samu kwatsam ba, to kuwa shaida akan cewa ido da hoton da idon yake gani ba zai yiwu ace ya samu kwatsam ba. Yana bukatar tsari da nazari sosai fiye da na talabijin. Tsari da nazari mai karfi irin wannan mallakar Ubangiji ne; shi ne kadai yake da iko akan dukkan komai.

Haka al’amarin yake afkuwa akan kunne. Wajen kunne na daukar sauti ya shigar dashi kai tsaye can cikin kunne; tsakiyar kunne ya tafiyar da sauti, can cikin kunne su tura wannan raurawar sauti cikin kwakwalwa yayin da ake canza shi zuwa na’urar sakonni. Kamar dai ido, ji yana karewa ne yayin da ya shiga cibiyar majiya a kwakwalwa.

3 boyutlu görüntü, 3 boyutlu gözlük

For decades, thousands of engineers have been trying to create a high-quality three-dimensional imaging system, using special systems and glasses. Despite the extraordinary progress made in the technological arena, they have never been able to form a three-dimensional image as clear as what the eye can perceive.

Yanayin dake tattare da ido haka yake a kunne. Wato, kwakwalwa na karbar sako ne daga sauti kamar dai haske: bata barin wani sauti ya shiga. Saboda haka, komai yawan hayaniyar dake waje, cikin kwakwalwa kuwa babu komai sai shiru. Duk da haka, sauti mafi kara na tsinkayuwa ne daga cikin kwakwalwa. A kwakwalwarka, inda sauti yake tafiya, kana jinsa kamar taron makada ne suke kade-kade, kuma kaji duk wani sautin dake fita a cikin taro. Haka kuma idan da za’a auna karfin jin sautinka da wani abin gwaji na musamman da sai aji babu komai a kwakwalwarka sai shiru.

Bari mu sake kwatanta karfi da ingancin fasahar dake cikin kunne da kwakwalwa da fasahar da dan Adam ya kera. Idan muka dawo kan hoto, anyi iya kokari shekaru da dama don samar da sautin da zai yi daidai dana asali. Sakamakon haka aka samar da rediyo mai sauti, na’urori masu amfani da sauti, da wasu na’urorin. Duk da wannan fasahohi da kuma dubban injiniyoyin da kwararru suke ta aiki a wannan fanni, babu wata na’ura da aka yi wadda take tsinkayar sauti daidai da yadda kunne yake tsinkaya. Kayi tunanin duk wani irin kere-keren da manyan kamfanonin hada sauti suke samarwa. Ko a cikin wadannan na’urai, idan aka nadi sauti sai an rasa wasu abubuwa daga ciki; ko kuma idan ka kunna sai kaji sautin iska (hiss) kafin ka fara jin abinda ka nada. Bayan haka, sautin da ya samu daga fasahar jikin dan Adam yafi sahihanta da fitowa fili. Kunnen mutum kuwa ba zai taba tsinkayar sauti da shigar ko kaji sautin wani abu kamar yadda na’ura take yi ba, tana tsinkayar sauti ne kamar yadda yake. Haka al’amarin yake tun da aka halicci dan Adam.

A takaice, fasahar dake jikinmu ta shafe fasahar da mutum ya samar daga bayananta, kwarewa da samun dama. Babu wanda zai ce fasaha mai karfin fitar da sauti ko camera ta wanzu kwatsam. To ta kaka za’ayi da’awar cewa kimiyyar dake jikin dan Adam, wadda tafi wadannan, ta samu haka nan a sakamakon sarkar haduwa da juna wai shi juyin halitta ?

Shaida ta tabbata akan cewa, ido da kunne, da sauran sassan jikin mutum halitta ce daga kasaitaccen mahalicci. Wadannan ayoyi ne da suke tabbatar da kadaitakar Ubangiji wanda ya kagi halitta, daga ilminsa da buwayarsa.

Dalilin da yasa muka ambaci gabar ji da gani anan saboda kasawar masana juyin halitta wajen fahimtar shaidun halitta a fili kamar haka. Idan wata rana, ka tambayi dayansu ya bayyana maka yadda wannan kasaitaccen zubi da fasahar dake cikin ido ko kunne a dalilin samuwarsu kwatsam, za kaga cewa ba zai iya baka wata amsa ta hankali ko tunani ba. Har Darwin , a wasikarsa zuwa ga Asa Gray a watan Afrilu 3 ga wata 1860, ya rubuta cewa tunanin yadda halittar ido take yana sashi zazzabi kuma da kansa yayi kasaitar sifofin halittu masu rai.149

büyücü, evrim yalanı

In the same way that the beliefs of people who worshipped crocodiles now seem odd and unbelievable, so the beliefs of Darwinists are just as incredible. Darwinists regard chance and lifeless, consciousless atoms as a creative force, and are as devoted to that belief as if to a religion.

 

Footnotes

147Pierre-P Grassé, Evolutionof Living Organisms, New York: Academic Press, 1977, sh. 103.

148 Ibid, sh. 107.

149 Norman Macbeth, Darwin Retried: An Appeal to Reason. Boston: Gambit, 1971, sh. 101.

14 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top