Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
17 / total: 22

Babi Na 15 - Media: An Oxygen Tent for the Theory of Evolution

Kamar yadda muka rigaya muka sani tun acan baya, ka'idar juyin halitta bata doru akan hujjojin kimiyya ba.Duk da haka da yawa daga mutanen a fadin duniya basu san haka ba, har yanzu suna zaton juyin halitta wata hujja ce ta kimiyya. Babban dalilin wannan yaudara shine amfani da dabarun hanyoyi don yada farfaganda ta kafofin watsa labarai akan juyin halitta. Saboda haka ne yasa sai mun sanar da hanyoyin da suke amfani dasu wajen cusa wannan muguwar akida da farfaganda.

Farfagandar Masana Juyin Halitta
 focus, bilim teknik

Shararrun Mujallun Kimiyya sun dauki ragamar yada farfaganda akan juyin halitta, sun taka rawa wajen cusawa mutane yarda da ka'idar juyin halitta.

 national geographic, dergi discovery, dergi archaeology, dergi

idan muka dubi kafofin watsa labarai na kasashen turai da kyau, mukan ji wasu labarai da suka kunshi ka'idar juyin halitta. Manyan kafofin watsa labarai, da sanannun mujallu wadanda ake "girmammawa" sukan rubuta abinda yafi haka. Idan aka yi nazarin kamun ludayinsu, mutum zai dauka cewar an tabbatar da hujjojin ka'idar juyin halitta kuma ba'a bar wata kafa ta tattaunawa ba.

Gama garin mutanen da suke karanta irin wadannan labarai sukan fara tunanin cewa an tabbatar da ka'idar juyin halitta kamar yadda aka tabbatar da ka'idar lissafi.Irin wadannan labarai da suke fitowa a fittatun kafofin watsa labarai sune kananan kafofin watsa labarai suke tsintsinta. Suna buga kanun labaran da manyan rubutu : "kamar yadda mujallar Time ta buga, sabon daftarin da ya cike gurbi a sarkar daftarin halittu ya bayyana", ko "Nature" wato "Yanayi" yati nuni cewa masana kimiyya sun yi karin haske akan ka'idar juyin halitta". Ganowar da aka yi ta bataccen daftarin dake sarkar juyin halitta" ba komai bane domin babu wani abu da aka tabbatar akan juyin halitta. Kamar yadda muka tabbatar a babukan da suka gabata, duk abinda suka nuna a matsayin shaida karya ne. bayan kafofin watsa labarai, yarda da hakan ta afka akan tafarkan kimiyya, kundin tarihi, da littattafan koyon ilmin rayuwar halittu da tsirrai.

A takaice, kafofin watsa labarai da tsarar masana kimiyya, wanda sune suke tafiyar da irin wannan akida ta kin addini, kuma su suke riko da manufofin juyin halitta kuma suke tursasawa al'umma yarda da hakan.

Ta hakan ne saboda tafiyar lokaci juyin halitta ya zama wata akidar da ba za'a iya karyatawa ba. Kin yarda da juyin halitta ana ganin kamar karyata kimiyya ne da muhimmman al'amura tabatattu. Saboda haka, duk da cewa kusakurai da dama da skua fito fili (musamman tun 1950) kuma duk da cewar su da kansu masanan suka yi ikirari, a yau abu ne mawuayci kaga wata sukar juyin halitta a tsarar masana kimiyya ko a kafofin watsa labarai.

Ganin irin karbuwa da "girmamawa" da mujallu kamar su scientific American, Nature focus, da National Geographic suka samu akan ilmin halitta da yanayi a fadin turai, suka riki ka'idar juyin halitta a matsayin akidarsu da kokarin bayyanar da ka'idar wata aba da tabbatar da ingancinta.

Rufaffun Karairayi

Masana juyin halitta sun yi amfani da wata babbar dama da suka samu daga kafofin watsa labarai ta hanyar "juyar da kan mutane". Mutane da yawa sun yarda da juyin halitta kuma ba su damu su tambayi "ta kaka" da "menene yasa" ba. Ma'ana dai masanan kan fure wasu karairayi don suyi saukin jan hankali.Misali, har acikin manyan littattafansu na "kimyya" "rikidar halittar ruwa zuwa halittar ban kasa", wadda tana daya daga manya-manyan al'amura marasa hujja a juyin halitta, to anyi "bayani" akanta mai saukin fahimta.

A fadar ka'idar juyin halitta, rayuwa ta fara ne a ruwa kuma dabbobin farko wadanda suka bunkasa sune kifaye. Kuma wai wadannan kifaye ne wata rana suka fara tsallakowa zuwa kan kasa saboda wasu dalilai, (yawancin lokuta, sun fi kawo dalilin rashin saukar ruwan sama), kuma kifin da ya zabi ya rayu aban kasa, sai aka ga ya samo tafukan kafafu maimakon kayoyi, da kasusuwan kirji.

Yawancin littatafan masanan basu fadi yadda hakan ta faru ba. Koda a cikin asalin llittattafansu, zaka ji rufa-rufar da suke yi ta cikin wasu kalamai kamar “sai fitowa daga ruwa zuwa kasa tayi nasara”.

Gajerun Tatsuniyoyi Daga Masana Juyin Halitta

Juyin Halitta, kamar yadda wani masanin Kimiyya ya fada, tatsuniya ce ta manya. Kwata-kwata shirme ce kuma babu wata alaka ta Kimiyya, wadda tace matattun Kwayoyin Halittu suna dauke da karfi na sihiri da hankalin da zasu iya tsara yanayin halitta. Wannan dogon labari na dauke da gajerun karairayi masu ban sha’awa dangane da wasu kebantattun batutuwa. Daya daga cikin irin wadannan zurfafan labaran Juyin halitta shine akan “juyin halittar kifi Whale” wanda aka buga a mujallar National Geographic, mujallar da ake ganin tana daya daga cikin masu kiyaye Kimiyya kuma wadanda suka himmatu kwarai wajen buge-buge a Duniya:

Tasowar Whale zuwa girman jikinsa ya faro ne shekaru miliyan sittin da suka shude, yayin da tarin gashi, ta samu kafafu hudu, saboda neman abinci ko neman mafaka, sai ya fada ruwa. Shekaru na tafiya, ya fara canzawa a hanali. Kafafuwan baya suka fara bacewa, na gaba kuwa sai suka zama masu kadawa a ruwa, gashi ya koma ya zama fatar jiki mai santsi, hanci ya koma goshi, sannan jela ta fadada ta zama faffadan kayoyin dake kasan jelar kifi, da yake a cikin ruwa ne sai jikin ya dace da mazaunin.1

Duk da hujjar cewa babu wata hujja ta kimiyya ko ta kwabo a ciki, faruwa hakan ya sabawa ka’idar yanayin rayuwa. Domin wannan Tatsuniyar da aka buga a National Geographic ya tabbatar da irin nisan da suke yi wajen yada karairayin masana Juyin halitta.

Wata Tatsuniyar da masanan suka rubuta itace asalin Dabbobi masu shayarwa. Masanan sun kada baki sunce wai Dabbobi masu shayarwa sun samo asali ne daga magabatan halittu masu rarrafe. Amma idan aka zo bayanin haka sai kaji suna ta kawo irin wadannan tatsuniyoyi. Ga daya daga cikinsu:

Wasu daga cikin Dabbobi masu rarrafe a nahiyoyi masu hunturu sai suka fara samar da hanyar da zasu rika dumama jikinsu. Zafin dake fita daga jikinsu ya karu yayin da zafin dake fita daga jikinsu ya karu a lokacin da ake sanyi saboda haka jin duminsu ba ya raguwa lokacin da kwayoyinsa suke kankancewa, sannan su canza zuwa gashi. Guminsu yana taimakawa wajen rage sanyin. Amma Kwatsam sai aka ga kananan wadannan Halittu masu rarrafe suna lasar gumin iyayensu mata don samun kuzari. Sai gumin ya fara inganta, can sai ya zama nono. Saboda haka sai kananan Dabbobi masu shayarwa na farko suka samu kyakkyawan farko.2

Dabarar cewa tsararren abinci kamar nono zai samu Kwatsam daga sunadarin gumi da dai sauran bayanan da syka yi tati don Kirkiro hasashen juyin halitta, tare da rashin madafa a kimiyance.

1. Victor B. Scheffer, “Exploring the Lives of Whales”, National Geographic, vol. 50, December 1976, sh. 752

2. George Gamow, Martynas, Mr. Tompkins Inside Himself, London: Allen & Unwin, 1968, sh. 149

Kaka akai wannan “fitowa” tayi nasara? Mun sani dai kifi ba zai iya rayuwa sama da wasu ‘yan mintina ba a ruwa ba.

Idan muka dauka cewar fari ne ya faru sannan kifi ya fito zuwa ban kasa, to menene ya samu kifin? Amsar a bayyane take. Dukkanin kifayen da zasu fito daga ruwa mutuwa zasu yi daya bayan daya a cikin kankanin lokaci. Koda wannan tsari zai kai har shekaru miliyan goma, amsar dai zata zauna a haka: kifi zai mutu daya bayan daya. Dalili kuwa saboda cikakkiyar gabar hakarkari ba zata wanzu “kwatsam” ba, wato, ta hanayar maye gurbi, amma kuma rabin hakarkari, ta daya bangaren, bashi da wani amfani.

Amma shine hakikanin abinda masanan suka bayyana. “Canji daga ruwa zuwa ban kasa”, “canji daga ban kasa zuwa iska” da kuma wasu zace-zace wadanda “bayanansu” suka zama marasa ma’ana. Idan muka koma akan samuwar hadaddun gabobi kamarsu ido da kunne, masanan sun zabi suyi shiru akansu.

Abu ne mai sauki ka ja hankalin mutum a kwararo idan ka nuna masa kunshin “kimiyya”. Ka zana kirkirarrun hotuna da suke nuna canjin ruwa zuwa kasa, ka kirkiri sunaye ga dabbobin ruwa, “magabatansu” a ban kasa, da kuma “tsaka-tsakin tsari” (wanda kuma kirkiran dabba ne), sannan ka shirya kirkirarriyar karya: “Eusthenopteron ya rikida zuwa Rhipitistian crossoptergian, sannan Icthyostega ta wani dogon tsarin juyin halitta”. Idan ka snaya wadannan kalmomi a cikin bakin masanin kimiyya tare da kakkauran gilashi dauke da farin yanki, zaka yi nasara wurin gamsar da mutane da yawa, saboda kafofin watsa labarai, wadanda suka sadaukar da kansu wajen yada juyin halitta, zasu fade shi a matsayin wani kyakyawan labari mai kayatarwa ga duniya.

 

17 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top