Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
18 / total: 22

Babi Na 16 - Kammalawa: Juyin Halitta Rudi ne

Akwai wasu shaidu, bayan kaidojin kimiyya wadanda suka soki juyin halitta, amma a wannan littafin mun fadi kadan ne kawai daga ciki.Wadanda ma muka fada din sun isa su gamsar wajen fadar gaskiya. Koda yake an cure ta a inuwar kimiyya. Ka’idar juyin halitta ba kome bane illa rudin da ake kare shi kawai saboda amfanin fassara jari hujja. Rudin da ba’a kafa shi akan kimiyya ba sai akan yaudara, farfaganda da juyar da kwakwalwa.

Zamu iya takaice abubuwan da muka fadi a baya kamar haka.

Ka’idar Juyin Halitta Ta Rushe

Ka’idar juyin halitta ka’ida ce data fadi tun daga matakin farko. Dalili kuwa shine masana juyin halitta sun kasa bayani gamsashshe kai koda akan kwayar sunadarin gina jiki. Ballantana ka'idojin tabbatarwa ko ka,idojin kimiyyar lissafi dana hade-hade wajen samun wata damar da zata samar da rayuwa.

Shin akwai hankali ko natsuwa a yayin da kwayar sunadarin da zai samu kwatsam,dakuma cewar milliyoyin wadannan sunadarai wadanda aka jerasu atsare su samar da kwayar halitta mai rai;kuma ance akwai billiyoyin kwayoyi sun kokarta wajen haduwa kwatsam dominsu samarda halitta mai rai; kuma daga nan aka samu kifi; kuma wadanda suke fitowa ban kasa suka zama halittu masu rarrafe, tsuntsaye, kuma har da cewa wannan shine yadda miliyoyin jinsuna mabanbanta aban kasa suka samu?

koda bai zama wata hikima a wurinka ba, masanan su sun yarda da wannan labari. Saboda haka, wani sabon imani ne ko ince addini- saboda basu da hujja ko ta kwabo wadda zata tabbatar da gaskiyar labarinsu. basu taba samo wani tsaka-tsakin sifa kamar dai rabi kifi/rabi dabba mai rarrafe ko rabi dabba / rabi tsuntsu ba. ballantana su tabbatar da cewa sunadarin gina jiki, ko kuma tilon sunadarin amino acid wanda yake cikin sunadari, zai samu tilon sunadarin amino acid wanda yake cikin sunadari, zai samu a karkashin abinda yanayin duniyar yake; koda ma dakin gwaje-gwajensu wanda yake cike da kayan aikin kuma sunyi nasara akan haka. Sabanin haka, duk da kwazonsu, su da kansu masanan sun nuna cewa tsarin juyin halitta akwai alamu dake tabbatar da rashin samuwar tsarin juyin halitta a wani lokaci a fadin duniya.

Ba Za'a Iya Tabbatar da Juyin Halitta A Wani Lokaci anan Gaba ba.

Ganin haka, masanan suka koma tuntubar junansu da shirya mafarkin cewa wata rana kimiyya zata warware wannan takaddama a wani lokaci mai zuwa. bayan kuwa, kimiyya komai yawan shekarun da zasu zo. maimakon haka ma, lokaci na tafiya kuma kimiyya na bankada shiriritar da'awar masanan da fito dasu fili.

Wannan shine abinda yake faruwa. yayin da ake samun cikakkun bayanai akan ayyukan rayayyan tantanin halitta, sai ya bayyana a fili cewa tantanin halitta ba wai sassauka, zagayayye ne kamar yadda yazo a fahimtar zamaninsu Darwin ba

Duk da cewar yanayin na bawa kansa-dalili, kin yarda da hujjojin halitta da dora asalin rayuwa akakn zunzurutun rashin tabbas, da kokarin kare wadannan da'awoyi, wanda daga baya yana iya zama abin jin kunya. domin yayin da zahirin fuskar ka'idar juyin halitta zata kai su ga boye fuskokinsu.

Babban Abinda Ke ciwa Juyin Halitta Tuwo a Kwarya: Rai

Akwai jinsuna da yawa a duniya da suka yi kama da wasu. Misali, tana iya yiwuwa akwai halittun da suka yi kama da doki ko mage da wasu kwarukan da suka yi kama da wasu. Wadannan kamace basa bawa kowa mamaki.kamancen dake tsakanin mutum da gwaggwon biri kuwa abu ne da yaja hankali sosai. Wani lokacin ma yakan kai matsayin da wasu mutane su yarda da karairayin zantuttukan juyin halitta. A gaskiyance, wannan kamance tsakanin mutum da gwaggwon biri bashi da wata ma'ana. Dabba rhinoceros beetle da rhinoceros sun debo kamanni amma zai zama hauka ace za'ayi kokarin tabbatar da alakar juyin halitta tsakaninsu, daya kwaro ne kuma daya dabba ce mai shayarwa, ta waccan hanyar kamanni.

Har lia yau, gwaggwon birrai, ba za'a iya cewa wai sun fi sauran dabbobi kusanci da mutane ba. Hakika, idan za'a duba bisa tsari na hankali, to kuwa kudan zuma wanda yake samar da sakar zumar dake tattarae da mu'jiza ko gizo-gizon dake gina kasaitacciyar mu'jizar sakar igiyar giza-gizai sune yakamata ace sun fi kusanci da mutum. kuma sun fi dan adam kwarewa a fannonisu.

Akwai bambanci mai girma tsakanin mutum da biri duk da dan kamannin da suka debo. Biri dabba ce da bata da bambanci da doki ko kare idan za'a kwatanta yanayin hankalinsu. Amma mutum wata nitsatstsiya, kakkarfar halitta ce wadda take iya tunani, magana, fahimta, zabi da hukunci. Duk wadannan sifofi aiki ne na ruhin da mutum yake dauke dashi. Rai shine muhimmin da ya samar da bambanci mai fadi tsakanin mutum da sauran halittu. Kuma babu wata kama ta zahiri tsakanin mutum tsakanin mutum da sauran halittu da zasu iya rufe wannan ratar. A hakikanin halitta, rayayyiyar halittar dake da ruhi shine mutum.

Ubangiji Yana Halitta Ne Bisa Ikonsa

Idan da ace labaran da masana juyin halitta suka tsara sun faru a gaske shin zasu dauki hankali? Ko kadan. Dalili kuwa shine kowane matakin da juyin halitta ya gabatar kuma aka sanya shi a tafarkin wanzuwa kwatsam to ya samu ne ta hanyar mu'jiza. Koda rayuwa ta fara ne a hankali-mataki-mataki, kowane mataki zai taso ne daga wani kasaitaccen iko. Ba zai yiwu ace wadannan tafarkai zasu taso kwatsam ba kawai, ba zai yiwu ba.

Idan ance sunadarain gina rayuwa ya samu kansa karkashin taskar yanayi, to kuwa lallai ne a tuna cewa ka'idar daidaito, halitta, gwajin kimiyya sun nuna tuni cewar wannan yanayin ba zai faru kwatsam ba kawai, ba zai yiwu ba.

Idan ance sunadarin gina rayuwa ya samu kansa karkashin taskar yanayin, to kuwa lallai ne a tuna cewa ka'idar daidaito, halitta, gwajin kimiyya sun nuna tuni cewar wannan yanayin ba zai faru kwatsam ba. Amma idan da za'a dauka ma sun wanzu hakan, to babu wani zabi illa a yarda cewa wanzuwarta na fitowa ne daga ikon mahalicci. Wannan magana ita za'a dora akakn dukkanin zantuttukan da masana suka gabatar.

Misali, babu wata shaidar burbushi ballantana ta zahiri, sunadarai, tarin halitta ko wani tunani yake tabbatar da cewa kifi ya fito daga ruwa ban kasa, kuma ya rikida ya zama dabbar dake tafiya aban kasa.

Idan mutum zai yarda cewa kifi lallai ya koma ban kasa kuma ya rikida zuwa halitta mai rarrafe, mai yin irin waccan da'awa lallai ya yarda da wanzuwar mahaliccin da yake da ikon duk abinda yaso ya halitta tare da kalmar "kasance". Duk wani bayani da zai sabawa wannan mu"jiza karyata kai ne da sabawa ka'idojin hankali.

Gaskiya a bayyane take. Rayuwa gaba dayanta aiki ne na kasaitaccen mai iya tsarawa da kera halitta. Wannan shi yake samar da shaida akan wanzuwar mahalicci, mamallakin dawwamamman iko, sani da hikima.

Kuma Allah shine mahalicci, Ubangijin sammai da kasa da duk abinda yake tsakaninsu.

 

18 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top