Evolution Hoax

Rudun Juyin Halitta

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
21 / total: 22

Babi Na 19 - Alakar Lokaci da Faruwar Kaddara

Kowane abin dake alakantuwa da abubuwan dake sama suna bayyana cewa babu wanzuwar "tafarkai uku" a hakikani, wannan yana nuna cewa abu ne dake tattare da sabani wanda tsinkaye yake riskar dashi kuma zai jagoranci rayuwar mutum a cikin rashin kufai. Sanya wata magana sabanin haka kamar yarda ne da camfe-camfen da tunani da gaskiyar kimiyya ta rushe; domin babu wata cikakkiyar shaida akan wanzuwar tafarkai uku a zahirin rayuwar duniya.

Wannan hujja ta soki zaton falsafar jari-hujja wadda ta goyi bayan ka 'idar juyin halitta. Wannan zaton shine wanda suke cewa kwayoyin halitta gaskiya ne babu makawa kuma wanzazzu ne. Zatonsu na biyu wanda akansa ne aka dora falsafar jari-hijja shine na ikirarin cewa lokaci shima gaskiya ne babu makawa kuma wanzajje ne. Wannan ma yafi zama camfi fiye da na farkon.

Tsinkayar Lokaci

materyalist profesör, rennan pekünlü
 

Tsinkayen da muke kira lokaci, a hakika, wani tsari ne da ake kwatanta yanayi guda zuwa wani. Zamu iya bayanin haka tare da misali. Misali, idan mutum ya nadi wani abu a cikin rediyo, zai ji wani sauti. Yayin da ya sake dauka bayan minti biyar, zai sake jin wani sautin. Mutum zai tsinkayi cewa akwai wata rata tsakaninsu kuma wannan rata yana kiranta "lokaci". Duk da cewa a lokacin da yaji sauti na biyu, sautin farko ba wani abu bane illa hasashe a cikin zuciyarsa. Wani guntun sako ne dake cikin kwakwalarsa. Daga nan ne mutum yake samar da tsinkayar "lokaci" ta hanyar kwatanta wani yanayin da yake rayuwa da abinda yake a cikin kwakwalwarsa. Idan ba'a yi wannan kwatance ba, ba za 'a samu tsinkaye akan lokaci ba.

Haka ma, mutum na iya yin kwatance idan yaga wani na shiga wani daki ta kofarsa kuma ya zauna a kujera a tsakiyar dakin. A lokacin da mutumin ya zauna akan kujera, hotunan dake da alaka da lokacin da ya bude kofa, ya shiga dakin, da nufo kujera da yayi duk zasu taru waje guda a matsayin wani sako a cikin kwakwalwa. Tsinkayen lokaci zai samu yayin da aka kwatanta zaman mutumin akan kujera da wadancan bayanan da yake dauke dasu.

A takaice, lokaci na wanzuwa ne sakamakon kwatancen da ake yi tsakanin wasu hotunan dake tattare a kwakwalwa. Idan mutum ba ya iya tuna abu, to kwakwalwarsa ba zata iya yin wadannan fassarori ba kuma tsinkayen lokaci ba zai iya samuwa a wurinsa ba. Dalilin da yasa mutum yake tabbatarwa da kansa cewa ya shekara talatin saboda ya tara bayanai ne dake dauke da wadannan shekaru a zuciyarsa. Idan ba ya iya rike abu, to ba zai iya tunanin wanzuwar gabatar wadannan lokuta ba kuma zai kawai rika tsinkayar "yanayin" da kawai yake ciki a wannan lokacin ne.

Bayanin Rashin Lokaci a Kimiyance

Bari muyi kokarin fayyace wannan gabar karatu da kawo bayanan da mafi yawan masana kimiyya da malamai suka yi akai. Dangane da batun da muke yi akan kwaranyar lokaci zuwa abinda yake baya, shahararren masani kuma marubuci Farfesa a fannin ilmin jinsin halitta, Francois Jacob, ya rubuta a cikin littafinsa Le Jeu des possibles (Yiwuwa da Hakikani):

Hotunan fina-finai dake komawa baya, sun sa mana yarda da hasashen yiwuwar duniya da lokaci ke kwaranya baya. Duniyar da madara ke rabewa daga (coffee) yayi tsalle ya fito daga kofi ya koma cikin akushi, duniyar da dutse yake gangarowa daga hannun mutum ya fada cikin ruwa tsulum kuma dutsen yana yin tsalle ya fito daga ruwan ya koma hannun. Duk da haka, a wannan duniyar da lokaci yake da sabanin sifofi, yadda kwakwalwarmu take aiki da yadda muke tattara bayanai a ciki, shima zai iya aiwatarwa ta komawa baya. Haka gaskiyar al'amarin yake akan abinda ya wuce da wanda zai zo kuma duniyar zata zo mana kamar yadda muke ganinta. 214

Tunda kwakwalwarmu tana kunshe ne da faruwar al 'amura, duniya na aiwatuwa ba kamar yadda aka ambata a sama ba, kuma zatonmu shine lokaci kullum yana kwaranya ne gaba. Bayan haka, wanna wani hukunci ne da aka yanke shi a kwakwalkwa saboda haka yana da cikakkiyar alaka. A zahiri, ba zamu taba iya sanin yadda lokaci yake tafiya ba ko yana tafiya ko a 'a. Wannan wata alama ce dake tattare da hujjar cewa lokaci bashi da hakikanin tabbas amma kawai wani tsarin hasashe ne.

Alaka ta lokaci wata hujja ce da mafi muhimmancin masana kimiyyar lissafi na karni na 20 ya tabbatar da ita, Albert Einstein. Lincoln Barnett, ya rubuta a littafinsa The Universe and Dr. Einstein.

Dangane da samuwar sarari, Einstein ya karyata samuwar tabbacin lokaci daga tafiyarsa. tare de bambancin lokacin dake tafiya a duniya, wanda yake kwarara daga abinda ya wuce zuwa wanda zai zo gaba. Mafi yawancin abinda yake boyuwa wanda ta kewaye ka'idar kwatanci daga sakankancewar mutum izuwa fahimtar gabar lokaci, kamar gabar launi, itama tsarin tsinkaye ce. Kamar dai yadda sarari yake wani tsari ne na halittar da ake iya gani, haka ma lokaci wani tsari ne gabar lokaci ta samu cikakkken bayani daga kalaman Einsten. "Rayuwar muturn ta yau da kullum" yace, "itace take bayyana garemu a jere daga faruwar abu zuwa wani; a wannan jeri ne idan muka tuna faruwar wani abu dake zuwa a irin wannan tsari muke ganinsa a matsayin 'abinda ya wuce' da 'wanda zai zo'. Saboda haka ga kowane mutum akwai wanzuwar lokaci-guda, ko kayadadden lokaci. Wannan a karan kansa bashi da ma'auni. Ina iya, danganta kaina da faruwar abubuwa da dama, ta inda adadi mai yawa wadanda suke da alka da faruwar abubuwan da zasu zo akan wadanda suka wuce. 215

Einsten da kansa ya fito da abin fili, kamar yadda aka hakaito daga littafin Barnett: "Sarari da lokaci wasu sifofi ne da ake fahimta kai tsaye, wadanda ba za'a iya raba su da hankali ba fiye da fassararmu akan launi, sifa, ko girman abu". Kamar yadda yazo a kaidar dangantaka: "Lokaci bashi da wanzuwa a karan kansa idan ba mun tsara shi bisa auna shi da faruwar al'amura ba" 216

Tunda lokaci yana kunshe ne da tsinkaye, ya dogara ne akan mara tsinkaye saboda haka akwai dangantaka.

Bigiren da lokaci yake tafiya akai ya bambanta da irin kwatancen da muka auna shi saboda babu agogon asali a jikin mutum wanda zai iya nuna hakikanin lokutan da suka shude. Kamar yadda Lincoln Barnett ya rubuta: "Kamar dai yadda babu wani abu wai shi launi ba tare da idon da zai kallato shi ba, haka ma yanzu ko nan da sa 'a guda ko kwana guda ba komai bane ba tare da faruwar wani abin da za 'a iya tunawa saboda shi ba." 217

Dangantakar lokaci wani abu ne da ake riskarsa a mafarki. Koda yake abubuwan da muke gani a mafarki sukan dade zuwa sa'o'i, hakika, sun dade ne izuwa wasu mintoci, koma ince wasu sakunkuna.

Bari muyi tunani akan misalin da zai fayyace mana abin sosai. Mu dauka cewa an samu a cikin wani daki mai taga daya wadda musamman aka gina ta kuma aka ajiye mu zuwa wasu lokuta. Kuma ace akwai agogo a dakin yadda zamu iya ganin adadin lokacin da ya wuce. A daidai lokacin, muna gani ta taga daga dakin yayin da rana take fitowa da dagawarta a wani lokaci. Bayan 'yan kwanaki, amsar da zamu bayar akan yawan lokacin da muke zaune a ciki zai dogara ne akan bayanan da muka tattara wajen lura da agogo lokaci beyan lokaci da kuma lissafin de muha yi akan adadin yawan fitowar rana da tsayarwarta. Misali, mu dauka mun kwana uku ne a dakin. Saboda haka, idan mutumin da yasa mu cikin dakin yazo yace mana kwana biyu muka yi a dakin kuma yace ranar da muke ta gani daga tagar ta karya ce aka tsara da na 'ura kuma agogon da aka sanya a cikin dakin an shirya shi musamman don ya rika gudu sosai, saboda haka lissafinmu zai zamanto bashi da ma 'ana.

Wannan misalin ya tabbatar mana cewa bayanan da muka tara akan tafiyar lokaci yana da alaka izuwa abubuwan da zamu iya dangantawa dasu. Dangantakar lokaci hujjar kimiyya ce wadda aka tabbatar da shaidun tsaunukan kimiyya. Ka'idar Dangantakar ta Einsten ta tabbatar da cewa tafiyar lokaci na canzawa amma ya danganta da saurin tafiyar abu da kuma nisansa daga tsakiyar fizgawarsa. Yayin da saurin tafiyar ke karuwa, lokaci yana raguwa, yana tsukewa; yana tafiya kadan-kadan kai kace yazo magaryar "tukewa". Bari muyi bayani tare da misalin da Einsten ya bayar da kansa. Mu dauka ga wasu 'yan biyu, daya yana zaune a wannan duniya da muke ciki yayin da dayan yayi tafiya izuwa duniyar wata a gudun tafiyar kusa dana haske. Idan ya dawo, zai ga cewar dan' uwansa ya fi shi tsufa. Dalili shine lokaci na tafiya kadan - kadan ga wanda zai yi tafiya a gudun da ya kusa dana haske. Idan za 'a iya sanya wannan misali akan uban da ya shirya tafiya duniyar wata da dansa a duniya, idan shekarunsa 27 lokacin da ya shirya tafiyar kuma dansa yana dan shekera 3; idan uban ya dawo duniya bayan shekaru 30 (a lokacin duniya), dansa zai zama dan shekaru 33 amma mahaifinsa zai zama 30 kacal. 218

Zai fito fili cewa wannan dangantakar lokaci ba tana gamuwa bane saboda tafiya a hankali ko gudun tafiyar agogo lo karancin gudun wata na' ura ba. Sai dai a sakamakon bambancin gudanarwar tsarin rayawa wanda yake tafiya mafi nisa kamar isin kwayoyin komayya. A wasu kalmomin, gajartar lokaci ba daya yake da tafiyar - hotunan fina-finai a hankali ba wanda yake ganinsu ba. Ta wannan tsarin lokaci yake gajarcewa ne, zuciya take bugawa, kwayar halitta take yaduwa, kuma kwakwalwa take aiki, da dai sauran abubuwan da suke aiki a hankali kamar mutumin da yake tafiya a hankali aban kasa. Mutum na cigaba da gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum kuma baya fahimtar gajarcewar lokaci. Hakika gajarcewar lokacinma ba zai ganu ba sai idan an tashi gwaji.

Time is a concept entirely contingent on the perceiver. While a certain time period seems long for one person, it may seem short for another. In order to understand which one is right, we need sources such as clocks and calendars. It is impossible to make correct judgments about time without them.

Dangantaka A Cikin Kur 'Ani

Tukewar da ta kaimu ga samo amsoshi a kimiyyar zamani shine cewar lokaci ba tabbataciyyar hujja bace kamar yadda 'yan jari-hujja suke zato, sai dai kawai dangantakar hasashe. Abu mai ban sha'awa shine wannan hujja, wadda ba'a gano ta ba sai a karni na 20 a kimiyance, an ilmantar da dan Adam a cikin Alkur'ari karnuka 14 da suka wuce Akwai misalai a cikin Alkur'ani dake nuna dangantakar lokaci.

Abu ne mai sauki gano irin shaidun hujjoji a kimiyance cewa lokaci wani al'amari ne da yake tasirantuwa da tsinkaye kuma ya dogara ne akan abu mai faruwa, tsara wani abu da yanayi a ayoyi da yawa daga Alkur;ani. Misali, gaba dayan rayuwar dan Adam tana da karancin lokaci inji Alkur'ani:

A ranar da yake kiranku, sannan ku rika karbawa game da gode masa kuma kuna zaton baku zauna ba face kadan. (Suratul Isra, 52)

Kuma ranar da yake tara su, kamar ba su zauna ba face sa'a guda daga yini. Suna gane juna a tsakaninsu. (Suratu Yunus, 45)

A wasu ayoyin, an nuna cewa mutane suna tsinkayar lokaci daban - daban kuma ance wasu lokuta mutane sukan tsinkayi dogon lokaci a matsayin gajere. Tattaunawa da zata afku tsakanin mutane ranar alkiyama kyakkyawan misali ne akan wannan.

Hakika Ni, Ina saka musu a yau, saboda abinda suka yiwa hakuri. Domin lalle ne su, sune masu samun babban rabo. Yace, "Nawa kuka zauna a cikin kasa na kidayar shekaru? Sukace, "Mun zauna a yini daya ko rabin yini, sai ka tambayi masu kidayawa." Yace, "Ba ku zauna ba face kadan, da dai kun kasance kuna sani! "(Suratul Muminun, 112-114)

A wasu ayoyin an tabbatar da cewa lokaci yana iya tafiya ta fuskoki dadan – daban :

Kuma suna neman ka yi gaggawa da azaba, alhali kuma Allah ba zai saba wa 'adinsa ba, kuma lalle ne, yini daya a wurin ubangijinka kamar shekara dubu yake daga abinda kuke kidayawa. (Suratul Hajj, 47)

Mala'iku da Ruhi (Jibrila) suna takawa zuwa gare shi, a cikin yini wanda gwargwardonsa, shekara dubu hamsin ne. (Suratul Ma'arij, 4)

Wandannan ayoyi dukkansu na nuni akan dangantakar lokaci hujjar cewa wai sakamako ya samu a kusa saboda fahimtar kimiyyar karni na 20 da Alkur'ani ya bayyanawa dan Adam shekaru 1,400 da suka shude wata alama ce dake tabbatar da saukar da Alkur'ani daga Allah, wanda yake dauke da lokaci da kuma sarari (kufai).

Ambaton da ake yi a ayoyi masu yawa a alkur'ani ya nuna cewa lokaci tsinkaye ne. Misali, Ubangiji ya ajiye Ashabul kahfi, wasu kungiyar muminai a cikin Alkur'ani, cikin dogon barci sama da karnuka uku. Yayin da aka farkar dasu, sai suka yi zaton sun zauna a wannan wuri lokaci kankani, kuma suka kasa fahimtar adadin kwanakin da suka zauna.

Sai muka yi duka akan kunnuwansu, a cikin kogon, shekaru masu yawa. sannan muka tayar dasu, domin mu san wane dayan kungiyoyin biyu suka fi lissafi ga abinda suka zauna na lokacin.(Suratul Kahfi, 11-12)

Kuma kamar wannan ne, muka rayar dasu, domin su tambayi juna a tsakaninsu. Wani mai magana daga cikinsu yace, "Menene lokacin da kuka zauna?" Suka ce, "Mun zauna yini daya ko sashin yini". Suka ce, "Ubangijinku ne mafi sani ga abinda kuka zauna ... (Suratul Kahfi, 19)

Wannan yanayin da aka fada a aya mai zuwa a sama shima shaida ce da take nuna cewar gaskiya fa lokaci tsinkaye ne a kwakwalwa.

Ko kuwa wanda ya shude akan wata alkarya, alhali kuwa tana wofintacciya akan gadajen resunanta. Yace "Yaya Allah zai rayar da wannan a bayan mutuwarta." Sai Allah ya matar da shi, shekara dari; sannan kuma ya tayar dashi. Yace: "Nawa ka zauna?" Yace: "Na zauna yini daya ko kuwa rabin yini. "Yace: "A'a, ka zauna shekara dari. "to, ka duba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kowannensu) bai sake ba, kuma ka duba zuwa ga jakinka, kuma domin mu sanya ka wata aya ga mutane. kuma ka duba ga kasusuwa yadda muke motsar dasu, sannan kuma mu tufatar a gare shi, yace: "Ina sanin cewa lalle Allah akan dukkan komai mai ikon yi ne."(Suratul, Bakara, 259)

Aya ta sama ta karfafa a fili cewa ubangiji da ya halicci lokaci ba ya bukatuwa izuwa gare shi. A daya bangaren kuwa, mutum na bukatuwa izuwa lokaci kamar yadda Allah ya kaddara. A cikin ayar da ta gabata, mutum ba ya sanin adadin lokacin da yayi a barcinsa. A wannan yanayi, idan ance lokaci wanzajje ne (kamar dai yadda 'yan jari-hujjia suka fada a rashin hankalinsu), zai zamanto rashin hankali.

Kaddara

Wannan dagantaka ta lokaci ta fito da wani muhimmin abu fili. Wannan dangantaka tana daukar yanayin lokaci wanda yake iya zuwa mana daga shekaru biliyoyi, yazo mana ya tafi cikin sakan daya ta wata hanyar.

Haka kuma, wani dogon lokaci wanda zai faro tun daga farkon duniya izuwa karshenta na iya zuwa ya tafi a tsarin lokacin da bai kai sakan daya ba amma a wani dan tsinkaye kwatsam ya tafi.

Wannan wata muhimmiyar alama ce dake nuni akan kaddara - wani ilmi ne wanda mafi yawancin mutane basu fahimce shi sosai ba, musamman ma 'yan jari hujja, wadanda suka karyata hakan baki daya. Kaddara wani ilmi ne na Ubangiji akan faruwar abubuwan da suka faru da wadanda zasu faru nan gaba. Mafi yawa daga mutane sukan tambayi yadda Ubangiji ya riga ya san abubuwan da basu riga sun faru ba" basu riga sun faru bane kawai a wurin mu. Ubangiji baya bukatuwa izuwa lokaci ko sarari domin shine da kaga ya halicce su. Saboda haka, abinda ya riga ya faru, wanda zai zo, da wanda ake ciki yanzu duk daya ne a wurin Allah; domin a wurinsa, komai ya riga ya faru ya kare.

Lincoln Barnett yayi bayani akan yada ka'idar Dangantaka (theory of General Relativity) take shiryarwa izuwa wannan hujja a cikin. The Universe and Dr. Einstein: Kamar yadda Barnett ya fada, sararin samaniya zata "iya dauka a karan kanta nauyin fitar da haske nagartacce".219 Ikon da Barnett ya ambata "haske nagartacce" shine hikima da ilmin Ubangiji, wanda yake saman sararin duniya. Kamar yarda muke ganin farkon shugaba, tsakiyarsa, da karshensa, da duk sassan dake hade dashi, Ubangiji ya san lokacin da muke karkata izuwa faruwar wani abu guda tun daga farkonsa har zuwa karshe. Mutane suna riskar faruwar wani abu idan lokacinsa yazo kuma suna ganin abinda Ubangiji ya kaddara halitta garesu.

Yana da muhimmanci jawo hankali izuwa kankantar rashin fahimtar da ake fama akan kaddara da ya yadu cikin al'umma. Wannan fahimta ta riki cewa Allah ya riga ya halicci "kaddara" ga kowa amma wani lokaci mutane na iya canza wannan kaddara din. Misali, ga majinyacin da ya farfado daga kofar mutuwa yana fadar wani zance kamar yace "ya tsallake kaddara" Duk da cewa, babu wanda zai iya kokarin canza kaddararsa. Mutumin da ya juyawa kofar mutuwa baya ba zai mutu ba saboda an kaddara masa cewa ba zai mutu wannan lokacin ba. Haka kuma kaddarar mutanen da suke yaudarar kansu ne da cewa "Na tsallake kaddara ta" kuma suke yarda da hakan a zuciyarsu.

Kaddara ilmi ne na Ubangiji wanda ya barwa kansa, ya san lokaci kamar wani zamani guda kuma ilminsa yake kewaye da gaba dayan lokaci da kufai komai yana faruwa kuma ya kare cikin kaddarawa. Mun kuma fahimta daga abinda ake fada a cikin Alkur'ani cewa lokaci daya ne wurin Ubangiji: Wadansu abubuwa da suke faruwa akanmu a nan gaba da aka fade su a cikin Alkur'ani a matsayin sun rigaya sun faru tuntuni. Misali, ayoyin da suke bayani akan cewa mutane za su amsa tambaya gaban Ubangiji a alkiyama ana kawo su a matsayin labarin abinda ya rigaya ya faru tuni:

Kuma aka busa a cikin kaho, sai wadanda ke a cikin sammai da kasa suka suma, sai wanda Allah ya so (rashin sumarsa), sannan aka hura a cikinsa, wata hurawa, sai gasu tsaitsaye, suna kallo! Kuma kasa tayi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littafi; kuma aka zo da Annabawa da masu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakaninsu, da gaskiya , alhali kuma, su, ba za ' a zalunce su ba… kuma aka kora wadanda suka kafirta zuwa Jahannama, Jama'a - jama'a… kuma aka kora wadanda suka bi Ubangijinsu da takawa zuwa Aljanna, jama'a - jama'a… "(Suratuz-zumar, 68-73)

Wasu ayoyin da suke maganar wannan batu sune: kuma kowane sai yazo, tare da shi akwai mai kora da mai shaida. (Suratu Qaf, 21)

Kuma Sama zata tsage, domin ita a wannan, mai yauni ce. (Suratul Hakka,16)

Kuma ya saka musu, saboda hakurin da suka yi, da Aljanna da tufafin alharini. Suna masu zaman ginciri (kishingida) a cikinta, akan karagu, basu ganin rana a cikinta, kuma basu ganin jaura. (suratul Insan, 12-13)

Kuma a bayyana Jahim ga mai gani. (Suratun Nazi'at, 36)

To, yan fa (a lahira) wadanda suka yi imaiu, su ke yiwa kafirai dariya. (Suratul mudaffifin, 34)

Kuma masu laifi suka ga wuta, shka tabbata lalle ne su masu auka mata ne, kuma ba su sami majuya ba daga gare ta. (Suratul kahf, 53)

Kamar yadda ake iya gani, abubuwan da zasu faru bayan mutuwarmu (a irin fahimtarmu) ana labarta mana su a matsayin abinda ya rigaya ya faru ya wuce tuni a cikin Alkur'ani. Allah ba ya dabaibaye da dangantakar lokaci kamar yadda muke. Ubangiji ya shirya ikonsa akan wadannan abubuwa a rashin lokaci: mutane tuni sun aikata abinda zasu yi kuma dukkan wadannan shafukan an yi su a raye kuma sun kare. An ilmantar a ayar dake zuwa cewa dukkan wani abu, karami ne ko babba, yana kewaye da ilmin Ubangiji kuma a rubuce a littafi:

Kuma baka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma baku aikata wani aiki ba, face mun kasance Halarce a lokacin da kuke zubawa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra ba zai yi nisa ba daga Ubangijinka a cikin kasa, haka kuma a cikin Sama, kuma babu wanda yake mafi karanci daga haka, kuma babu mafi girma, face yana a cikin littafi bayyananne. (Suratu Yunus, 61)

Damuwar 'yan Jari-Hujja

Batutuwan da aka tattatuna a wannan babi, kamarsu gaskiyar dake karkashin kwayoyin halitta, rashin lokaci, da rashin kufai, sun fito fili. Kamar yadda ya bayyana a baya, wadannan ba wani tsarin falsafanci bane ko wata hanyar tunani, amma tsantsar gaskiya wadda ba za 'a iya karyata taba. Kari akan tabbatar gaskiyarta, shaidun hankali da tunani ya tabbatar babu wata makawa akan batun sararin duniya, hakika kawayeniya ce gaba dayanta tare da abinda yake cikinta da mutanen da suke zaune akanta. Tarin tsinkaye ne.

'Yan jari - hujja suna sha fama wajen fahimtar wannan batu. Misali, idan zamu dawo kan misalin motar Politzer: koda yake politzer ya san cewa ba zai iya fita daga hasashen ba sai dai zai iya karbar abinda yazo masa saboda wasu yanayi. Ma'ana, ga Politzer, faruwar wani abu a kwakwalwa kafin hadarin mota, amma yayin da motar tayi hadari, abubuwa na fita daga kwakwalwa kuma su samu ganuwa a zahiri. Hikimar dake tattare anan ta fito fili: Politzer ya maimaita kuskure irin wanda bafalsafen jari-hujja Johnson wanda yace "Na bugi dutse, kafa ta taji rauni, saboda haka ya wanzu "kuma ya kasa fahimtar cewa zafin da yaji bayan faruwar hadarin motar shima hasashe ne kawai.
Dalilin da yasa 'yan jari-hujja ba zasu iya fahimtar wannan batu ba shine tsoron da suke yi na karbar hujjar da zasu iya fuskanta yayin da suka yarda da batun. Lincoln Barnett ya sanar da cewa wannan batu fa wasu masana kimiyya ne suka "ki yarda dashi":

Tare da takaicewar bayani na zahiri daga falsafawa akan inuwar-duniyar tsinkaye, masana kimiyya suna sane da irin yiwuwar takaice hankalin mutum. 220

Duk wata alaka da zata iya nuna cewa kwayoyin halitta da lokaci tsinkaye ne suna kawo babbar fargaba ga 'yan jari-hujja, saboda akan wadannan suke dogara a matsayin allolinsu. Shi, a ganinsa, ya dauke su kamar gumaka abin bauta; saboda yana tunanin kwayoyin halitta da lokaci sune suka halicce shi (ta hanyar juyin halitta).

Yayin da yaji cewa duniyar da yake raye a cikinta, duniya, gangar jikinsa, sauran mutane, falsafar jari-hujja wadanda ya gamsu da dabarunsu, a takaice dai, kowane abu, tsinkaye ne, sai ya kidime daga irin abinda yake tsorata shi. Dukkan abubuwan da ya dogara akansu, yayi imani dasu, kuma ya dauki tafarkin karewa sannu - sannu. Yana jin damuwa a ransa, wadda zai fuskance ta a ranar alkiyama kamar dai yadda aka bayyana ta a cikin aya "A ranar nan zasu shiga neman sulhu zuwa ga Allah, kuma abinda suka kasance suna kirkirawa ya bace daga garesu. "(Suratun Nahli, 87)

Daga nan ne kuma, wannan dan jari - hujjar yake kokarin gamsar da kansa a hakikanin lamarin kwayoyin halitta, kuma ya yarda akan wannan "shaidar"; ya buga kansa a garu, so suke su ga kowa yayi wurgi dashi. Suna cike da sanin cewa idan mutane suka gane gaskiyar kwayoyin halitta, to kuwa dadewar falsafancinsu da jahilcin dake tattare da ra'ayinsu zasu fito fili kowa ya gani, kuma ba za'a sake samun abinda zasu fake akansa ba don tabbatar da ra'ayinsu. Wadannan tsoro shine dalilin da yasa suka damu da hujjar da aka yi bayaninta anan.

Ubangiji ya ambaci tsoron da kafirai suke yi zai karu a ranar Alkiyama. A wannan rana ta Alkiyama, za'a tambayesu kamar haka:

Kuma ranar da muka tara su gaba daya, sannan mu cewa wandanda suka yi shirka: "Ina abokan tarayyarku wadanda kuka kasance kuna riyawa?" (Suratul An'am, 22)

Bayan haka, kafirai zasu yi shaida akan abinda suka mallaka, 'ya 'yaye da makusanta wadanda suke zaton wanzuwarsu kuma suke riya cewa abokan tarayya ne da Allah su rabu dasu kuma su lalace. Ubangiji ya sanar da wannan hujja a ayar "ka duba yadda suka karyata kansu! Kuma abinda suka kasance suna kirkira karyarsa, ya bace daga garesu." (Suratul An 'am, 24)

Ribar Muminai

Yayin da hujjar cewa kwyoyin halitta da lokaci tsinkaye ne dake nuni izuwa 'yan jari-hujja, sabanin haka mummunai na gaskiya suka rika de gaskiya. Ahalin imani suna farin ciki yayin da suka tsinkayi sirrin dake karkashin kwayoyin halitta saboda wannan gaskiya itace mukullin tambaya gaskiya itace mukullin dukkanin tambaya. Tare da wannan kukulli ne, ake kulle dukkanin suruka. Mutum zai gare a saukahe batutuwa masu yawa wadanda a baya yahe da karancin fahimtarsu.

Kamar yadda aka fada a baya, tambaya akan mutuwa, aljanna, wuta, alkiyama, canjin alkibla, da sauran muhimman tambayoyi kamarsu "Ina Allah yake?" "Menene kafin Allah?" "Waye ya halicci Allah?" Har tsawon wane lokaci rayuwar kabari zata kasance?" "Ina Aljanna de wuta?" kuma "Ina ne Aljanna da wuta suke yanzu?" zasu yi saukin amsawa. Za 'a fahimci irin tsarin da Ubangiji ya halicci duniya daga babu. Ta kai cewa, tare da wannan sirri ne, tambayar "yaushe" da "Ina" zasu zamo marasa amfani saboda babu lokaci da wani bigire da zai yi saura. Idan aka fahimci rashin sarari, za'a fahimci cewa duk abubuwan dake faruwa suna faruwa ne a lokaci guda: baby abinda ake jira kuma lokaci baya tafiya a haka, domin komai ya riga ya faru kuma ya kare.

Da wannan sirri ne, duniya take zama kamar Aljanna ga mumini. Dukkan wani kuncin rayuwa, zakuwa, da fargaba sun buce. Mutumin dake fahimtar cewa gaba dayan duniya tana da Ubangiji daya, kuma yana canza zahirin duniya yadda yaso saboda haka babu abinda yakamace shi illa ya mika wuya izuwa gareshi. Ya mika kansa gaba daya izuwa ga Allah "nayi bakancen abinda ke cikin cikina gareka". (Suratu Al 'Imrana, 35)

Fahimtar wannan sirri itace babbar riba a duniya. Ta wannam siri ne, wani mulimmin al 'amari ya fito fili a cikin alkur 'ani: hujjar cewa "Ubangiji shine mafi kusanta zuwa mutum daga lakar jannayensa". (Suratu Qaf, 16). Kamar yadda kowa ya sani, lakar jannaye a cikin jiki take. Wane abu ne kuwa zai fi kusanci de mutum fiye de abinde yake jikinsa? Za 'a iya bayanin wannan a saukake ta hanyar fahimtar rashin sarari: Wannan aya ma zata fi fahimtuwa idan an gane wannan sirrin.

Wannan shine tsantsar gaskiya. Kuma za'a iya tabbatar da cewa babu wani mataimaki kuma majibincin mutum idan ba Allah ba. Babu komai sai Allah; shine kadai zati wanzajje wanda mutum zai iya neman agajinsa, neman taimako, kuma ya kidaye lada.

Duk inda ka juyar da kanka, akwai wanzuwar Ubangiji.

 

Footnotes

214 François Jacob, Le Jeu des Possibles, University of Washington Press, 1982, p.111

215 Lincoln Barnett, The Universe and Dr.Einstein, William Sloane Associate, New York, 1948, sh. 52-53

216 Lincoln Barnett, The Universe and Dr.Einstein, William Sloane Associate, New York, 1948, sh.17

217 Lincoln Barnett, The Universe and Dr.Einstein, William Sloane Associate, New York, 1948, sh.58.

218 Paul Strathern, The Big Idea: Einstein and Relativity, Arrow Books, 1997, sh. 57

219 Lincoln Barnett, The Universe and Dr.Einstein, William Sloane Associate, New York, 1948, sh.84

220 Lincoln Barnett, The Universe and Dr.Einstein, William Sloane Associate, New York, 1948, sh.17-18

21 / total 22
You can read Harun Yahya's book Rudun Juyin Halitta online, share it on social networks such as Facebook and Twitter, download it to your computer, use it in your homework and theses, and publish, copy or reproduce it on your own web sites or blogs without paying any copyright fee, so long as you acknowledge this site as the reference.
Bayani akan shafin | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to author “Mr. Adnan Oktar”.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top