EVOLUTIONDECEIT.COMhttp://evolutiondeceit.comevolutiondeceit.com - Makalai - Recently AddedhaCopyright (C) 1994 evolutiondeceit.com 1EVOLUTIONDECEIT.COMhttp://evolutiondeceit.comhttp://harunyahya.com/assets/images/hy_muhur.png11666TUNANI MAI ZURFI 1.   A wani lokaci guda ka kasance a matsayin ‘yar mitsitsiyar kwayar halitta da ido ba ya iya ganinta. Wannan kwayar halitta ita ce ta rabu biyu kuma ta ribanya kanta sannan ta zama tsokar nama. Daga bisani ta zama mutum mai ji da gani. Sannan ka girma…

2.   Kowacce shekaru kamanninka su kan canja…

3.   Shin ko ka taba gane cewa babbar mu’ujiza ce wannan?

4.   Shin ko ka taba yin tunani kan cewa:

5.   Kowane abu a sararin duniya an halicce shi ne a bias wata ka’ida sannan kuma akwai tsarin daidaito marar nakasa a cikin kowane abin halitta?

6.   Ko kuma cewa kasar nan da ka ke tafiya a kanta cewa tana juyawa a bisa gudun kilomita 1,670 a cikin awa guda?

7.   Shin ka taba tsammanin sanin…

8.   Yadda a ka halicci tsirrai da bishiyoyin da ka ke gani suna kawata duniya?

9.   Yadda ýa’yan itace ke fitowa daga kasa ssannan yanayin dandano, kamshi da kuma launukansu ke burge ‘yan Adam?

10.  Yadda fatar ‘ya’yan itace ta kasance riga mai ban al’ajabin gaske…

11.  Shin ko ka taba tunanin…

12.  Cewa annobar da ke zuwa nan gaba tana iya afkawa birnin ku kuma ta tarwatsa gidanku cikin kiftawar ido, ka yi hasarar duk abin da ka mallaka a cikin kasa da minti guda?

13. Shin ka taba yin tunanin cewa…

14. Rayuwarka tana shudewa da sauri, kuma cewa wata rana tsufa zai zo maka ka rasa karfi da lafiya da kuma kyawun kamanninka?

15. Sannan ga mutuwa… ba ka san lokacin da za ta zo maka ba, sai dai kamar kowane mai rai, tabbas kai ma za ta zo maka!

16. Allah ya halicci mutum ya sanya masa ikon yin tunani.

17. Duk wadannan abubuwa kadan ne daga cikin al’amuran da ya kamata dan Adam ya rika yin tunani a kan su.

 

IKON YIN TUNANI GA DAN ADAM

18. Kowane mutum an sanya masa ikon  yin tunani, duk da yake yana iya jahiltar hakan. Yayin da mutum ya fara amfani da wannan iko na yin tunani sannan zai fara ganin abubuwa wadanda a da bai lura da su ba.

19. Allah ya halicci duk abubuwan da mu ke gani a bisa wata manufa inda kuma ya nemi mutane da su yi tunani a kansu. A wata aya yana cewa:

20. Hakika a cikin halittar sammai da kasa, da sabawar dare da yini, da jiragen ruwa wadanda ke gudana a cikin teku (dauke) da abin da yake amfanin mutane, da abin da Allah ya saukar daga sama daga ruwa, sai ya rayar da kasa da shi bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikinta daga dukkan dabba, kuma da juyewar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da kasa; akwai ayoyi ga mutane masu hankalta. (Sura ta 2, aya 164)

21. Mutumin da yake lura da kuma yin tunani kan halittar duniya da sararin subhana mai yalwa shine zai fi gane kyawu da cikar daidaito a tsarin halittar duniya.

22. Dan Adam na rayuwa ne cikin wata ‘yar karamar duniya da ke sagale cikin wani faffadan sarari marar iyaka, sannan kuma ita wannan duniya tana cikin barazar hatsarin da ka iya fada mata daga sararin sama. Kuma babu abin da bil’adama za su iya yi don kare faruwar wannan hatsari.

23. Alal misali, akwai wasu guma guman duwatsu da nauyinsu ya kai miliyoyi a ma’aunin ton da ke ninkaya a cikin iska a sararin subhana.

24. Kowanne daga cikinsu yana iya cin karo da wannan duniya da mu ke ciki wanda hakan baraza ne ga rayuwar mutane da dabbobi a duniyar.

25.  Wata barazar kuma da ka iya sanya rayuwar duniya cikin hatsari ita ce tartsatsi da fesowar zafin rana.

26. Taartsatsin yana iya karuwa inda hakan zai iya jawo karuwar yawan tsananin hasken rana da ke zuwa cikin duniya.

27. Akwai barazana mai yawa ga rayuwar mutum, ba kawai daga cikin sammai ba, har ma daga kasa.

28. Daga kasan murfin kasa ko duniya, akwai wani zirin wuta mai zafin gaske da a turance muke kira “magma.” Kuma shi murfin kasar ba shi da kauri. Ko don haka, amon wuta yana iya faruwa a kowane lokaci inda madin narkakkun duwatsu za su furzo zuwa doron kasa.

29. Ko kuma wata tsaga ko baraka a murfin kasa kan iya haddasa gagarumar girgizar kasa....

30. Dan Adam dole ne ya kasance yana sane da irin barazanar wadannan hatsarurruka da yake rayuwa cikin su.

31. Duniyarmu tana samun kariya daga barazar wadannan hadarurruka ne daga turakun daidaito na duniyar.

32. Mutumin da ya kasance yana tunani a kan wadannan abubuwa shi zai gane cewa dukkan halittu suna rayuwa ne a doron kasa bisa ikon Allah sakamakon tsarinsa na halitta marar nakasa a cikin sa.

 

MATSAYIN DUNIYARMU A SARARIN SUBHANA

33. Yalwar fadin sararin subhana ya bambamta da irin rayuwar da muka saba da ita. A yanzu haka, nisan kilomita miliyan 560 sama daga inda ka ke zaune, akwai buraguzan tartsatsin rana da ke zagayawa a sararin sama a kan tafiyar kilomita 100,000 a cikin awa guda.

34.Yanayin sanyin da ke sama ya kai digiri 273 debewa a ma’auni.

35. Yanayin sanyin da ke cikin taurari kuwa ya kai miliyoyin digiri a ma’auni.

36. Manyan manyan duwatsu ke harbawa da karfin gaske suna tarwatsa cikin holokon sararin samaniya.

37. Ka yi tunanin naka muhallin a cikin wannan holokon sararin duniya marar iyaka...

38. Don gano haka, bari mu fara kwatanta yanayin nisan wurare a wannan duniya tamu da nisan wurare a sararin sama.

39. A cikin sararin sama, nisan da ke tsakanin taurari mafiya kusanci da juna shi ne kilomita tiriliyan 30. A gaba dayan taurarin da ke haskawa a sama, wadda ta fi kusa da kai ita ce mai nisan kilomita tiriliyan dubu biyar.

40. To yanzu bari mu dubi yadda matsayin duniyarmu ya ke a cikin gungun taurari da ke sararin sama.

41. Akwai kimanin taurari bilyan 250 da ke yawo a cikin gungun taurarin.

42. Daga cikin su akwai rana.

43. Akwai wasu duniyoyi guda tara da suke kewaya rana bisa kyakkyawan tsari. Wadannan gaba daya su a ke kira da kwambar duniyoyi majibinta rana. A cikin wannan kwambar, wadda fadinta ya kai murabba’in kilomita bilyan 12, za ka sami duniyarmu ‘yar mitsitsiyar gaske.

44. In za ka dauki duniyarmu a matsayin dan ludo, to rana za ta kasance kwatankwacin girman kwallon kafa da ke nisan mita 280 daga dan ludon...

45. Duk da yawan fadadan duniyoyin da ke cikin gungun taurarin, gaba dayan gungun karami ne a cikin sararin subhana mai gungun duniyoyi bilyan dari uku (300).

46. Ba ma abin mamaki da kayatarwa kamar yanayin motsi da tafiyar duniyoyi da taurari a sararin sama.

47. Wannan duniya da mu ke ciki tana mirginawa a cikin sasanninta a gudun kilomita 1,670 a kowace sa’a guda.

48. A lokaci guda kuma tana zagaya rana, wadda ta linka duniyar sau 103 a girma.

49. Duniyar tana wannan zagaye (na rana) ne a gudun kilomita dubu dari da takwas a sa’a guda. Wato gudunta yafi  tafiyar harsashi da linki sittin.

50. A daidai haka kuma, duniyarmu da rana suna fuskantar tauraro “vega” a gudun kilomita 200 cikin dakika guda. Wannan yana nufin suna tafiyar kilomita dubu dari bakwai da ashirin a cikin sa’a guda.

51. Sannan kuma shi kan sa gungun duniyoyin yana tafiya.

52. Sannan kuma ko a jikinmu ba ma sanin irin wannan gagarumar tafiya da a ke yi da mu a kowane lokaci.

53. Ba ma sanin ana tafiyar ne, saboda lamarin yana tafiya ne bisa tabbataccen tsarin Allah mahalicci.

54. Shin ko ka taba tunani kan dalilin da ya sa ba ma taba sanin a na wannan tafiya?

55. A yanzu, daidai wannan lokaci da ka ke kallon wannan shiri, ba ka jin wata girgizza ko tangal tangal. Yayin da ka ke zaune a lambun shakatawa ko kuma kana tafiya ne a kan titi, ba ka da masaniyar cewa duniya tana juyawa... Amma duniyar nan wata katuwar shigifa ce da take fesa gudu a sararin subhana a kan gudun kilomita 200 a kowace dakika. Motsi guda kawai, mun ci gudun kilomita 200, a wani motsin mun ci 400, sai 600...

 

DARASI DAGA GANGAR JIKIN MUTUM

56. Yayin da rana ta fito, to gari ya waye kenan, an shiga wata ranar.

57. Hakika  ba karamar mu’ujiza ba ce yadda mutum ya ke tashi lafiyayye a kowace safiyar Allah.

58. Duk da ya ke cewa yayin barci mutum yana fita daga hayyacinsa, amma ya kan tashi washe gari cikin hayyaci da sururi kamar yadda ya ke kafin ya kwanta barcin.

59. Sa’annan kuma ya kan iya tunani, da magana, da gani.

60. Sai dai yayin da ya ke barci da dare, ba shi da tabbas cewa zai sake samun irin waccan rahama washe gari.

61. Wajibi ne ga mutane su yi nazari kan wannan, su gane irin falala da kariyar da Allah ya yi musu don su kara gode masa.

62. Wajibi ne ga mutane su yi tunani kan raunin halittarsu: Kamar yadda Allah ya fada a cikin Alkur’ani sura ta 4 aya ta 28 cewa: “An halicci mutum yana mai rauni.”

63. Idan mutane ba sa lura da abinda suke ci, da abinda suke sha ko tufafin da suke sanyawa a jikinsu, suna iya kamuwa da rashin lafiya...

64. Kwayar cuta daya tak wadda ido ba ya iya gani ita kadai ta isa ta kwantar da mutum mai nauyin kilo 60 zuwa 70. Marar lafiya kuwa ba abin da ya ke iya yi ban da kwanciya a gado.

65. A yayin wannan hali kuwa marar lafiyar ba shi da ikon komai, jidali ne ke afkuwa a cikin jikin.

66. Duk irin tsananin kiyayewarsa da ka’idojin da likita ya sanya masa, Allah mahalicci shi ne kadai zai iya dawo masa da lafiya da kuma karfin jikinsa. Don haka, zai yi kyau mu tuna abin da Ibrahim (AS) ya fada a cikin Alkur’ani cewa: “(Allah) Shi ne wanda ya ke ciyarwa ya shayar da ni, kuma yayin da na kamu da rashin lafiya, shi ne ke warkar da ni.” (Sura ta 16, aya ta 79 – 80).

67. An gina gangar jikin mutum bisa tsarin ilimin Allah mabuwayi. Hatta gashin kansa. Hatta gashin gira da na idanun mutum a kayyade suke. Rashin tofon su fiye da kima amfani ne gare mu. Amma kuwa gashin kan mutum, wanda ke taimakawa wajen fitar kyawun sigar mutum, ya kan ci gaba da tofo a tsawon rayuwarmu, kuma mu kan iya yin ado da shi ta sigar da muke so. Yanzu ka yi tunani kan wannan: idan gashin idanunka zai yi tofo ya girma kamar  gashin kanka, me ka ke tsammanin zai faru? Wa ye ya hana gashin girar idonka ci gaba ta tofo, ya dakatar da shi a wani ma’auni? Mutumin da ya ke lura da irin wadannan al’amuran baiwa to shi zai fi saurin gane cewa kowane sashe na jikin mutum, kowace gaba da tsoka ta jikin an halicce ta ne bisa kwarewa da kyakyawan tsari.

68. Akwai matukar tsari da gayar hikima a yadda kasusuwan mutum ke tofo suna  kara girma.

69. Kwakwalwar dan Adam tana fara habaka ne tun daga kuruciyarsa. A lokaci guda kuma kokon kansa shi ma yana kara girma da fadada. Idan girman kokon kai da na kwakwalwa ba sa tafiya tare, in har kokon kan ya yi kankanta ya matse kwakwalwar to tana iya yin bindiga ta fashe. Amma hakan ba ya faruwa. Kokon kai da kwakwalwa girman su tare ya ke tafiya har zuwa wani mataki inda kokon kan  kan rufe kwakwalwar ruf kamar keji.

70. Ta  ya ya kasusuwa, wadanda ke girma suna habaka tare, su ke sanin sun kai matakin karshen girmansu? Me zai faru in har kasusuwan suka ci gaba da girma?

71. Misali, da kasusuwan kirjin mutum za su ci gaba da girma har su wuce ka’idarsu, da sai a ga sun tsaga nama sun fito waje.

72. Amma saboda cikar tsarin halittar kasusuwan, hakan ba ya taba faruwa.

73. Kwayoyin halittar kashi su ke suranta kowane kashi kamar yadda masassaki ke suranta itace. Su ke fitar da sigar kowane kashi da mulmula shi sannan su dakatar da girmansa a daidai inda ya dace.

74. Ya kamata mu yi tunanni a kan wannan.

75. Shin kwayar halittar kashi tana da sani ne da hankali da kuma tsari da lura na yin duk wadannan abubuwa da muka zana?

76. Ta ya ya ta ke sanin inda za ta tsaya da kuma daga inda za ta ci gaba?

77. Koda ya ke dukkan kasusuwan da ke jikinmu sun samu ne daga tushen kwayar halittar kashi daya, amma ta ya ya a ke samun wasu sandararru da kuma wadanda a ke iya lankwasawa?

78. Shin wa ya tsara wa kasusuwa aikinsu a gangar jiki?

79. Ta ya ya nau’in kananan kasusuwa da ke hannayenmu suka san yadda za su sarrafa hannayen?

80. Ta ya ya kasusuwan hannaye, da kafafuwa da kuma na yatsunmu suke isa matsayin da a ke bukata kafin tsarin jiki ya daidaita?

81. Wadannan tambayoyi ne da ya kamata mu tambayi kanmu don mu iya fahimtar yadda tsarin tafiyar da halittar jkin mutum ya ke.

82. Sai dai abu ne mai wuya a dauka cewa duk wadannan abubuwa sun samu  ne a bisa katari ko dace; ba shi yiwuwa a ce kwayoyin halitta wadanda su ne tushen samuwar mutum da kuma sassan da suka hadu suka gina kwayoyin halittar suna da ikon haifar da abu a radin kan su. Kowane daya daga cikin wadannan abubuwan halitta alama ne da ke nuna fasahar Allah wanda ya halicci mutum kuma ya tsara halittarsa. A wata ayar Alkur’ani Allah yana cewa:

83....Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa´an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma... (Sura ta 2 aya 159).

 

DARASIN DA ZA MU KOYA A CIKIN ABINCI

84. Allah, a rahamarsa, ya halicci abubuwa mabambantan dandano ga bayinsa don su ci su sha daga gare su. Wannan rahama tana nuna matsayin Allah mai kyautar baiwa ne ga bayinsa:

85. Allah  ne...  Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana. (Sura 40 aya 64).

86. Da Allah ya ga dama da sai ya kasance abinci kala daya kawai a duniya. Amma saboda ‘yan Adam su gode masa, sai ya halitta musu nau’in abubuwa don rahamarsa.

87. Wannan rahamar Allah ce da ludufinsa ga bayinsa.

88. A cikin kowane nau’in abinci da abin sha akwai abubuwan lura da ke tunatar da mu dimbin ni’imomin Allah gare mu.

89. Ga misali, mafi yawan ‘ya’yan itace an halicce su ne da bawonsu. Wadannan bawo ko fata su kan kare su daga lalacewa ko rubewa, sannan suna kare su daga datti inda hakan ke kara musu kyau da kamshi.

90. ‘Ya’yan itace irin su lemon zaki, da sauran nau’in ‘ya’yan itace masu kunshe da sinadarin vitamin C mai yawa a cikinsu, an tsara su ne don saukin ci. Irin wadannan ‘ya’yan  itace suna yin ýaýa ne a lokacin yanayin sanyi lokacin da mutane suka fi bukatar sinadarin vitamin C...

91. A lokacin zafi a na matukar bukatar ruwa. Don haka, a wannan yanayi a ke samun ‘ya’yan itace kamar su kankana da tufa da sauran ire irensu a wadace.

92. Duk wannan yana nuna cewa Allah ya halicci ‘ya’yan itace ne don amfanin bani-Adama...

93. Ganin yadda dan itace ke habaka a gan shi ya nuna yana lilo a jikin rassan bishiyoyinsa shi ma wata kyakkyawar baiwa ce ta Allah ga ‘yan Adam.

94. Dandazon ‘ya’yan itacen tufa masu launin kore ko ja da kuma sauran ‘ya’yan itace nau’inta...

95. Idan ka  bara dan itacen kiwi zuwa bari biyu, za ka ga kyakkyawan tsarin halittarsa mai burgewa. Wani kuma dan itacen da a ka sani wajen kyawun tsarin halittar sa shi ne garahuni, za ka gan shi jawur a tsakiyar koren ganyensa. Duk da yake cewa duk wadannan ‘ya’yan itace sun fito ne daga kasa wadda ta ke mai duhu, amma kowannensu ya sha bamban da irin dandano da kamshinsa, da kuma launin jikinsa mai kyau. Har ila yau, suna kara nuna mana gwanintar halittar Ubangiji, iliminsa mayalwaci da kuma hikimarsa a cikin ayyukansa.

96. A cikin wata ayar Alkur’ani, Allah yana umartar bani-Adama da su  yi tunani a kan wannan baiwa da ya yi musu:

97. Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa´an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren),kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũn da ruman, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku yi dũba zuwa ´ya´yan itãcensa idan ya yi ´ya´yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni. (Sura 6 aya 99)

 

ABUBUWAN IZNA A CIKIN YANAYI DUNIYA

98. Da za ka fita waje ka dan zagaya a cikin sarari, za ka ga wasu abubuwa masu kyau da ka iya daukar idonka: kamar kyawun furanni masu launi, ko koriyar ciyawa ko gona, ko kuma ‘yar karamar tururuwa...

99. Hatta ‘yar karamar tururuwa da ka ke gani, an halicce ta da siffofi masu ban al’ajabi. Wannan mitsitsiyar kwaruwa ta kan iya gutsuttsura ganye da bakinta, ko ta dauki abubuwan da suka fi girman jikinta kuma har ta kai su cikin gidanta a saukake.

100. Ta kan  iya doguwar tafiya mai nisa duk kuwa da kankantar ta. Kuma duk inda ta je ba ta  mance hanyar komawa gidanta. Tabbas, wannan ‘yar karamar halitta a radin kanta ba za ta iya kididdige wadannan abubuwa ba. Allah ne mahalicci ke kimsa mata yin hakan da ludufin sunansa mai jinkai.

101. Yadda garahuni ke yado a jikin rassan bishiyoyi ko kuma a jikin bango ko wani abu, al’amari ne da  ya kamata mu yi tunani da lura a kan sa. Da za a yi rikodin din wannan yado a faifan bidiyo sannan daga bisani a kalle shi a yanayin saurin hoton bidiyon, za ka ga yadda garahunin ke motsi kamar wanda ke da rai. Kai ka ce ya hango wani reshe ne a nan kusa inda ya kan cafko shi ya hade da shi. Wani sa’ilin ma ya kan kanannade jikin reshen ne. A haka ya ke bazuwa cikin sauri, sannan bayan ya gama yadon ta fuska guda, sai kuma ya koma kasan sannan ya sake daukar wani bangaren daban.

102. Wani kuma abu daga cikin kyawun halittar Allah shi ne kamshin da furanni ke fitarwa. Misali, akwai irin filawar da ke fitar da wani yanayin kamshi mai karfin gaske da ke dume guri. Hatta irin turaren kamfani da a ke yi ya  gaza kai kamshinta. Lokacin da masu gwaje gwajen kimiyya suka yi kokarin kirkiro kwatankwacin kamshinta, karshe abin ya faskara. Yawancin irin turaren kamshin da suka samar su kan kasance masu karfi da duma kai. Ko kuma kamshin kan gushe cikin dan lokaci kadan.

103. Amma shi kamshin fure ba  ya dimautar da mutum. Koda ka tsinke furen daga jikin filawa to zai ci gaba da fitar da kamshinsa har sai lokacin da ya bushe.

104. Wata mu’ujizar ta Allah kuma ita ce ta bishiyoyi da ke daukar ruwa su kai shi sama har na nisan mitoci. Shin ka taba tsayawa ka yi tunani kan yadda ruwa kan isa can saman rassa da ganyen dogayen bishiyoyin da ka ke gani?

105. Bishiyoyi suna tsotso ruwa daga cikin zurfin kasa zuwa saman rassan su. Su kan yi hakan ne ba tare da wani famfo ko inji ba.

106. Domin fahimtar wannan kyakkyawar hikimar halitta, bari mu duba wani misali: A kan yi amfani da famfo don turo ruwa zuwa saman bene. Ba don wannan famfo ko wani abu makamancinsa ba, ba yadda za iya tura ruwa koda zuwa hawa daya na bene.

107. Sai dai kuma bishiyoyi su kan yi wannan aikin ba tare da famfo ko wani inji ba. Amma su kan iya jawo ruwa su shayar da rassa da ganyensu na can sama.

108. Saiwoyi masu kamar bututu da ke cikin jijiya da gangar jikin bishiya an yi su ne ta yadda ruwa zai iya wucewa ta cikinsu. Yayin da ruwa ya taso sama, jijiyoyin su kan tsuke don ruwan ya sami damar wucewa. ‘Ya’yan halittar da ke cikin ruwa suna yin gogoriyo da juna yayin da a ke tunkuda ruwan zuwa kololuwar saman ganye.

109. Allah Ubangiji shi ne ya halicci tsarin saiwoyi (ko hanyoyin ruwa) a jikin kowane ganye tare da tsarin ruwa don lamarin ya tafi daidai. Kamar yadda ya zo a wannan aya ta Alkur’ani, Allah wanda tausayi da rahamarsa ba su da iyaka, ya halicci bishiyoyi da sauran tsirrai don amfanin mutane da sauran abubuwa masu rai:

110. Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Ya fitar game da shi, daga ´ya´yan itãce arziki dõminku... (Sura ta 14 aya 32)

 

ABABEN LURA A RAYUWAR YAU DA KULLUM

111. Kullum a akwatunan talbijin din mu mu kan ga labaran ta’addanci da sauran nau’in mugayen ayyuka. Babban abin da ke haddasa wadannan abubuwa shine saboda cewa wadansu mutane suna gudanar da rayuwarsu ba a kan kyakkyawan tsarin rayuwa wanda Allah mahalicci ya dora mu a kai ba. Mafi yawan mutanen da ke gudanar da rayuwarsu sabanin yadda addini ya tsara su ne kan iya aikata ta’addanci a kan sauran mutane ba tare da jin komai a ran su ba, tun da ba su da imani.

112. Rashin jin tsoron Allah  yadda ya kamata a tsorace shi shine babban dalilin da ke sa mutane su fada cikin ayyukan ta’addanci da barna; alhali suna sane ne ko kuma saboda jahlci sun kasa sanin cewa Allah zai tambaye su a kan rayuwarsu a duniya.

113 .Amma kuma kyakkyawar niyya, da amana, da tausayi, gaskiya sadaukar da kai da sauran kyawawan dabi’u wadanda addini ya koyar su ne ke bude hanyar zaman lafiya, da tsaro da kuma adalci a cikin al’umma.

114. Sau da yawa mu kan ji labaran annoba iri iri a kafafen watsa labarai. Mutum kan iya gamuwa annoba ko hatsari a wannan duniya. Wani lokacin, ba zato ba tsammani, mu kan ga wata gagarumar girgizar kasa ta afku, ko kuwa gobara ko ambaliyar ruwa su faru.

115. Annobar yanayi, cikin kankanin lokaci ta kan iya shafe duk wani gini ko kayan kere kere da ke baiwa mutane kariya. Cikin dakika daya kawai, abubuwan da mutane suka mallaka kamar gidaje da motoci, har ma da su kan su mutanen suna iya salwanta.

116. Mutumin da ke sauraron irin wadannan labarai na annoba zai san cewa ba shi da wata mafita face ya koma ga Allah mai ikon komai. Ga abin da Allah ya ke fada mana a cikin Alkur’ani:

117. Yã kũ mutãne! Kũ ne mãsu bukãta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadãci, Abin godewa (Sura ta 35 aya 15)

 

ABIN DA ALKUR’ANI YA KE FADA

118. 118.Allah ya saukar da Alkur’ani don ya zama shiriya ga mutane. Don haka, abin da ya kamaci mutum shine ya tsaya ya yi tunani da nazari a kan kowace aya ta Alkur’ani. A cikin Alkur’anin, Allah yana kira gare mu da mu yi nazari a kan abubuwa masu yawa. Misali, yana kiran mu da yin tunani kan halittar jikinmu...

119. To, mutum ya yi dũba, daga me aka halicce shi? An halicce shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna. (Sura ta 86 aya 5 – 6)

120. Allah yana so mu yi tunani a kan halittar sammai da kasa...

121. Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma´abota hankali.Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da kuma a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a banza ba. Tsarki ya tabbata gareKa! Ka tsare mu daga azãbar wuta. (Sura ta 3 aya 190 – 191)

122. Allah yana kiranmu da mu yi tunani kan rayuwar duniya wadda ba  ta dauwama...

123. Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani. (Sura 29 aya 64)

124. Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mene ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci,kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma suke dõgara ga Ubangijinsu kawai. (Sura ta 42 aya 36)

125. Allah yana sanar da mu don mu hankalta mu lura cewa duniya baki dayanta ya halicce ta ne don bil-Adama...

126. Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni. (Sura 45 aya ta 13)

127. Allah yana kiranmu da mu yi tunani kan sauran abubuwa masu rai da ya halitta...

128. Lalle kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni´ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini, nõno tsantsa mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã. (Sura ta 16 aya 66)

129. Haka nan kuma Allah yana kiranmu don mu yi tunanin ranar lahira, ranar tashi kuma ranar sakamako...

130. A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata na  alheri da kuma na sharri, a halarce, alhãli yana gũrin dã ace akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa. (Sura ta 3 aya 30)

 

KAMMALAWA

131.Mutumin da ke yin tunani da tafakkuri shi ke fahimtar sirrin halittar Allah da kuma yadda hakikanin rayuwar wannan duniya ta ke. Zai gane alamomin Allah a cikin kowane abu. Sabanin mafi yawan mutane, zai kasance a tsawon rayuwar sa yana tunanin yadda ya zo duniya da yadda ya ke rayuwa. Ta hanyar ilimin da Ubangiji ya sanar da shi ya ke yin tunani daidai yadda Ubangiji ya umarta.

132. Saboda haka shine zai fi kowa ni’imta da rahamar Allah da tagomashinsa, haka kuma ba abin da zai dame shi na daga al’amuran duniya masu sanya damuwa a zukatan mutane.

133. Wadannan kadan ne daga cikin manyan abubuwan daukaka da irin wannan mutum mai tunani zai samu a rayuwar duniya. Ta hanyar tunani da kuma gane gaskiya a rayuwarsa, a ranar lahira, wannan mutum zai sami soyayyar Allah, da  yardarsa, da rahamarsa da kuma aljannarsa.

134. Allah madaukakin sarki yana kira ga mu bayinsa zuwa ga hanya mafita don mu rabauta:

135. Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici tun kafin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgewa (su rabu biyu).Wanda ya kãfirta,to,kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa. Dõmin Ya sãkã wawaɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai. (Sura ta 30 aya 43 – 45)

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/37594/tunani-mai-zurfihttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/37594/tunani-mai-zurfiWed, 26 Jan 2011 10:19:30 +0200
An Dauki Larabawa da Yan Kwaminis Aiki Wajen kai Hari ga Tagwayen gida a Ran 9/11. OKTAR BABUNA: Manzon mu Muhammad (saw) ya jawo hankalin mu akan yadda fitina zata kasance kamar kura da hayaki, kuma alamu ne zuwan Mahdi (as) fitinah zai bayyana kamar kura da hayaki,sai kuma wasu fitina su biyo baya.( Al-Muttaqi al-Hindi, Al-Burhan fi Alamat al-Mahdi Akhir az-Zaman). Kamar abinda ya faru a lokacin da kura da hayaki suka bayyana a New York ran 11 ga September 2001. Ance fitinah da hayaki ya bayyana,kuma ko ina cike yake da kura da hayaki.

ADNAN OKTAR:  Ku lura a cikin maganar manzo (saw)akwai hikima a ciki kuma cike yake da hikimomi masu yawa,fitnah zai bayyana tare da kura da hayaki ,kura da hayaki ana samun su a ko ina, abin nufi sai wani abu ya faru kafin ka ga kura da hayaki ya tashi ,kamar rusherar gida ko gobara,babban abin nufi anan shine rushewar gida.Amma kura shi yafi jan hankali tunda shi aka fara gani. kuma shine ya turnuke sama kafin a fara ganin hayaki,mutane suna mamaki suna cewa mun zo mun ga irin tasirin kura, amma ita fitnah babban kalma ce ,wannan fitnah shine ta wannan kura da hayaki.anfara da kura sai hayaki sune fitnah. An kai hari kan iraki da afganistan da kuma ana tsokanar kasashen musulmi ,shekarun da suka gabata cike yake da fittintinu.kuma kiristoti suna nemam fitnah don su jawo yaki a duniya. maida martanin  musulmi zai sa ya zama yaki kamar ka ce za’a  tada duniyar saboda rigingimu.

Wannan fitnah CIA ne ta shirya shi tare da manyan kiristoti da niyyar su tada hankalin duniya kuma sunyi amfani da rubabbun larabawa da yan komunis  a wani bangare anyi amfani da karya da larabawa masu son abin duniya .kuma duk sunyi karatun su a kasashen turawan ingila da amerika kuma anyi amfani dasu wajen aikata wannan mummunan aiki.

Kuma sunce jirgi yakai hari a Pentagon,”mun ga jirgin amma babu alamun sa a Pentagon, ko da kusa daya ba’a gani ba ko wani bangaren jirgin a inda ji kara,sun sa duniya cikin rudani da rashin kwanciyar hankali sunyi haka don su jawo hankalin mutane su yarda  abinda ya faru alhali babu abinda ya shafi Pentagon kuma babu wani bangaren jirgin da aka samu a pentagon.

.ina tambaya ina kurakuzan jirgi ? sunce ya narke to a nuna mana narkeken sunce ya riga ya narke ya waste yaya za’ayi ace jirgi ya fadi ace babu sauransa koda kadan, wanda kowa ya sani duk lokacin da jirgi ya fadi akan samu bangaren sa,amma wannan babu abinda aka samu,to yaya wannan ya zama daban?

 Mafi yawan hatsarin jirgi yakan bar sauran sassan jikinsa amma wannan jirgin babu wanda ya ga sassan jikin sa,kuma sun sa kowa ya yarda da cewa hakan mai faruwa ne kuma ya faru,game da rushewar gini kuwa shi ma akwai abin mamaki a ciki,jirgi ya doki gini sai gini ya kama da wuta.

 Hatsarin jirgi yana faruwa a kasshe mai yawa amma yaya za’a ce wai jirgi ya doki ginin kuma ace wuta ta kama a hawa ta daya da biyu da uku daga karshe gini ya fadi, musamman irin wannan gini da aka gina da karafuna, babu dalilin da zai sa ace ya fadi a dalilin wannan dukan da jirgin yayi ,wannan gina ta musamman ne . Shin abin tambaya anan shine wutar daga kasa ta faro? yaya jirgi zai doki gini ta sama kuma wuta ta tashi ta kasa?

OKTAR BABUNA: Rushewa gaba daya yana faruwa.

ADNAN OKTAR: Kuma dama hikima ta inginiyoyi ya nuna cewa ginin  zata fadi saboda ginin ya riga ya tsufa ,yana bukatar a rushe shi a sake sabo.  A wurare da dama a duniya akwai irin wannan hikimar da dabarun rushe tsohon gini, sukan yi amfani da  na’ura mai rushe gini,kamar yadda wannan gini ya rushe. kuma  za’a kama mutane da laifi sa’anan kuma a sake su rana daya,wanda a ke son a rike su sai a rike su tunda  dama sune ake bukatar kamawa.yanzu zan kara maka bayani don ka kara gamsuwa da abin mamaki kuma duk duniya zata gamsu.

 “Ance ka aikata wannan Laifi  ,ance musulmi sunyi aikata kaza da kaza ‘’,kamar yadda suke fadi’’ saboda haka zamu mamaye kasar ku dalilin abinda kuka aikata ‘’ sun kai hari kan Afghanistan da Iraq kuma sun rushe masu gidaje da kampanoni masu yawa kuma kullum sai rashin mutunci yake  karuwa akan kasashe musulmi .mutane da yawa suna ganin yin haka ya kamata ,kuma suna cewa basu ga  laifi a cikin kai hari kan musulmi ba.”ka ga haka  dajjal yake gudanar da aikin sa ta hanyoyi masu yawa, kuma wannan yana  daya daga cikin hanyar  dajjal da aikin su. 

Nov 14, 2010

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/36968/an-dauki-larabawa-da-yanhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/36968/an-dauki-larabawa-da-yanSun, 09 Jan 2011 09:27:45 +0200
AKWAI DA YAWA DAGA KIRISTOCI DA YAHUDAWA MUSULMAI, AMMA SUNA BOYE MUSULUNCIN SU ADNAN OKTAR: Haka yake, Yakamata abi Hanya da ta dace wajen kiran kiristoci da yahudawa zuwa ga yarda da karban Addinin musulunci, Ina tsammanin wadanda da suke nuna Kyama da Wulakanta Kiristoci da Yahudawa,basu son Addinin Musulunci ya yadu ya cigaba, ko kuma basu da Ilmin ta Da’awah. Akwai Kiristoci da Yahudawa Musulmai masu yawa a Wannan Kasa tamu ta Turkey, amma suna boye Musuluncin su.Kuma akwai wasu jama’a masu yawa wanda ba kirista ba ba kuma yahudu ba musulmai, wanda suma suna boye musuluncin su a wannan kasa. Haka idan da zan kirga maka wanda  na hadu dasu da wanda Na sani Musulmai, zakayi mamaki saboda yawan su. Amma suna boye Musuluncin su saboda suna fama da matsi da fitintinu daga cikin gida. Ya Kamata su bayyana kansu, kuma kada su ja da baya.Yana daga Cikin halin dan Adam na Rashin Dauriya da Hakuri akan Jarrabawa Musamman jarrabawa marar kyau.Kuma suna  tsammanin zasu iya kare kansu tare da  boye musuluncin ba tare da ansani ba.Musuluntar Kiristoci da Yahudawa yana nuna  Tabbatacin  Yaduwar Addinin Musulunci da Cigaban sa , Kuma Alama ce mai nuna Cewa  Lokaci yayi da Addinin Musulunci zai mamaye Duniya baki daya.

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/28573/akwai-da-yawa-daga-kiristocihttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/28573/akwai-da-yawa-daga-kiristociTue, 20 Jul 2010 02:32:57 +0300
WURAREN TARON MATSAFA TA MASONIC ZASU ZAMA MASALLATAI ,KUMA SU MATSAFAN ZASU MUSULUNTA KUMA SU NEMI ILMIN ADDININ MUSULUNCI ADNAN OKTAR: A Halin Gaskiya Kungiyar  Matsafa ta Freemasonry zasu ga Canje Canje a cikin Shekaru Kadan Masu zuwa,Kungiyar su zata yi Rauni sosai,Ina  Nufin zasu Musulunta ,bugu da kari Zamu Mayar da Gidajen Tsafin su Zuwa Masallatai in Allah ya Yarda. Kuma za’a samu Kyakyawar Zamantake wa.Kuma wannan Manyan Kyawawan Gidaje da suka gina na Tsafi zamu  mayar dasu Wurin Ibada  wato zasu zamo masallaci da yardan Allah.Kuma zasu zama Yan’uwan mu, za’a zauna lafiya dasu da  kwanciyar hankali, saboda  gane gaskiya da sukayi da kubuta daga hannun shaidan mai  hallakarwa,Kuma zasu Tabbata cikin Natsuwa da Fahimta. Misalin a Wannan lokacin Manyan Matsafan,Masu Girma da Mabiyan su zasu zo su Ziyarace ni, In Allah ya yarda. Kuma zasuyi Farin Ciki Ma’ana Zasuyi Murna da Wannan Ziyarar ‘’kuma Za suce’’Zamu yi taka tsantsan da duk abinda ya sabawa koyarwar Addinin musulunci, Kuma zamu Tabbatar da cewa sun Fahimci Addini, zasu nemi taimakon mu wajen neman Ilmin Addini Musulunci, kuma zasu koyi Karatun Alkur’ani lalle zamu Taimaka masu akan haka ,Saboda guje masu bazai amfane mu ba. Misali Annabi Musa (AS) bai gudu ba, zuwa yayi Fadan Fir’auna ya Fada mashi Kalmomin Ubangiji. ya kuma  Bayyana mashi Hukuncin Addini. Shima Annabi Ibrahim (AS) yaje wajen Nimrud yayi mashi wa’azi akan Musulunci. I dan muka dawo kan Maganar Kungiyar Matsafa ta Masonic,Duk  yaram mu ne ,kuma yan kasar mu, kuma suma halittar Allah ne a bayan kasa,kuma suna daga cikin zuriyar Annabi Adam (AS).Muna masu fatan Alheri tare da samun Shiriya ta Gari. Duk Lokacin da Yan Kungiyar Matsafa ta Masonic suka Shiga Musulunci to Daga Ran nan Addinin Musulunci ya cimma burin sa  na mamaye  duniya baki daya in Alllah ya Yarda.
 


 

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/27583/wuraren-taron-matsafa-ta-http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/27583/wuraren-taron-matsafa-ta-Fri, 02 Jul 2010 07:31:36 +0300
MANZANNIN ALLAH ZA'A TASHE SU CIKIN KYAKKYAWAN SURAR SU DA AKA SANSU A DUNIYA RANAR KIYAMA,AMMA KAFIRAI ZA’A TASHE SU CIKIN MUMMUNAN HALITTA. OKTAR BABUNA: "Allah gafarta Mallam  Adnan, Shin lokacin da za’a tara Mutane wajen Hisabi ,za’a  tashe su ne cikin kamannin su da fuskokin  da aka sansu dashi anan duniya idan kiyama ta tsaya?. Misali  zamu iya gane fuskokin mutane da muka sani  anan duniya da Manzannin da aka bamu labarinsu a can Lahira? Hikmet Samil."

ADNAN OKTAR: Kwarai kuwa ,Manzanni zasu tashi cikin Kyakkyawar surar da aka san su dashi a nan duniya ,Amma su kafirai za’a tashe su Cikin Mummunar Sura.Halittar su bazata cika ba,Kodai ba Hannu ko Babu Kafafuwa.Saboda sun ki cika Umurnin Ubangijin su anan  Duniya, Saboda Wannan Dalili  Halittar su Bazata Cika ba acan lahira, Insha'Allah.

 

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/27582/manzannin-allah-zaa-tashe-suhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/27582/manzannin-allah-zaa-tashe-suFri, 02 Jul 2010 07:22:43 +0300
HIKIMA A CIKIN SIRRIN WAHALHALUN DA ANNABAWA SUKA SHA Hakika Allah (SWT)  ya sani cewa dukkan Annabawa mutane ne masu tsananin imani da tsarkin zuciya da kuma madaukakan kyawawan halaye da dabi’a, don kuwa shine ya halicce su ya sanya su masu kakkarfan imani da iklasi. Sai dai kuma, duk da ya ke cewa Annabawa zababbun bayi ne wadanda Allah ya daukaka su birbishin sauran bayinsa, su suka fi kowa haduwa da mafi girman jarrabawa da fitintinu a rayuwarsu ta duniya. Kuma wadannan wahalhalu da suke sha sun kasance alamu da ke nuna tsananin gaskiya da karfiin imaninsu ta yadda mutane za su yi koyi da kyawawan halaye da dabi’u irin nasu, sannan kuma don ya kara kusanci da soyayyar su Annabawan ga Allah ubangiji, haka nan don ladansu ya ribanya a ranar lahira gwargwadon wahalarsu a duniya. Allah ya bayyana mana nau’in yanayin jarrabawar Annabawa ta hanyar hikayoyi a cikin Alkur’ani.

Yayin da Annabi Musa (as) da mutanensa suka sami kansu cikin tsaka-mai-wuya; wato gabansu kogi bayansu kuma rundunar fir’auna ce ke dab da cim masu, da yawa sun fid da rai da samun kubuta. Wadanda ba su da imanin sanin karfin Allah suka ce “An rutsa da mu,” to amma kamar yadda ya zo a ayoyin sai Musa (as) ya ce “A’a, Ubangijina yana tare da ni kuma zai ba ni mafita.” (Suratul Shu’ara, aya ta 62).

Annabi Yunuusa (as) kuwa a tsawon lokacin wahalhalun da ya sha yayin da ya ke cikin kifi, ya mika lamarinsa ne ga Ubangiji inda, kamar yadda ayar Kur’ani ta fada mana, “Ya yi kira (ga Ubangiji)  a cikin halin tsanani." (Suratul Kalam, aya ta 47). A saboda kaskantar da kai da mika lamarinsa ga Allah da Yunus ya yi cikin mawuyacin halin da ya sami kansa, sai Ubangiji cikin rahamarsa da jinkansa ya kubutar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi, sannan ya aika shi ga wata al’umma a matsayin Annabi. Alkur’ani mai girma ya yi mana bayanin wannan jarrabawa da ta sami Annabi Yunus kamar haka:

“Yunus yana daga cikin ma’aikanmu. Yayin da ya gudu zuwa cikin babban jirgin ruwa. Suka yi kuri’a sai ta fada a kansa. Sai kifi ya hadiye shi alhalin ya kasance abin zargi. Ba don ya kasance yana daga cikin masu tasbihi ba, da ya zauna cikin sa har zuwa ranar da za a tashe su. Sai muka fito shi bisa doron kasa yana marar lafiya; kuma muka fitar da bishiyar duma a kansa. Sannan muka aika shi zuwa ga (al’umma mai yawan) dubu dari ko fiye da haka. Sai suka yi imani kuma muka jiyar da su dadi na wani lokaci.” (Suratua – Saffat, aya ta 139 – 148)

Yayin da Manzan mu (saas) mushrikai suka yi masa zobe shi da al’ummarsa babu mai zaton tsira a garesu. Wannan ita ce ranar kunci, ranar jarraba imani. Sannan kuma wannan jarrabawa ce ta musamman wadda za ta sa cikakkun muminai masu karfin imani, wadanda suka hakikance a zukatansu cewa taimakon Allah zai zo kuma suka mika dukkanin lamarinsu  gare shi, za su kasance tabbatattu bisa dugadugansu. Kuma kamar yadda Allah ya hukunta, wadanda suke da nakasa a cikin imaninsu da Allah da kuma munafukai sun fid da kaunar samun rahamar Allah a wannan hali inda suka kama dabarun kansu don neman mafita. Allah mabuwayi yana bayyana mana wannan mawuyacin hali a wata ayar kamar haka:

  “Yayin da suka zo muku daga birbishi da kuma ta kasanku, yayin da idanunku suka juye kuma zukatanku suka zo makogoro, kuma kuka yi wa Allah mummunan zato, a wannan hali an jarrabi muminai aka girgiza su matukar girgizawa. Yayin da munafikai da wadanda suke da ciwo a zukatansu suka ce ‘ba abin da Allah da Manzansa suka alkawarta mana sai rudi.’ Kuma wata kungiya daga cikinsu ta ce ‘Ya ku mutanen Yathrib, babu matsayi gare ku don haka ku dawo!’ Wasu daga cikinsu suna neman izini daga Annabi suna cewa ‘Babu tsaro a gidajenmu,’ alhalin ba batun rashin tsaro ba ne; kawai dai suna nufin gudu ne.” (Suratul Ahzab, aya ta 10 – 13)

A cikin wannan matsanancin yanayi, Ma’aikinmu (saas) tare da sauran muminai da ke tare da shi sun kasance suna masu tsammanin taimako daga Allah mabuwayi yayin da suka mika lamuransu gare Shi tun da sun san dama ya yi alkawarin zai taimaki masu imani da dogaro gare Shi. A wannan ayar Allah yana fada:

“Yayin da muminai suka ga rundunar taron dangi sai suka ce: ‘Wannan shine abin da Allah da Manzonsa suka alkawarta mana. Allah da Manzonsa sun yi gaskiya. Wannan bai kara musu komai ba sai imani da sallamawa.” (Suratul Ahzab, aya ta 22).

Haka kuma kamar yadda a wata ayar Allah ya ke bayyana mana, “Allah ya dauke wa muminai yaki. Allah mai karfi ne, mabuwayi.” (Ahzab, aya ta 25)

Annabi Yusuf (as) shi ma   ya hadu da manyan nau’o’i na jarraba a zamaninsa. Yadda a ka kulla masa kazafi sannan a ka wurga shi cikin kurkuku a ka mance da shi na tsawon shekaru, tabbas ba karamar jarraba ba ce wannan. Haka kuma tabbas daya daga cikin jarrabawar da ya tsallake cikin nasara da taimakon Allah ita ce yadda tun farko ‘yan uwansa suka jefa shi cikin rijiya inda ya zauna cikin duhun rijiyar yana mai tawakkali da tsammanin taimakon Allah. In da tawagar matafiyan nan ba ta biyo ta wajen rijiyar nan, kuma da mutanen cikin tawagar ba su nemi jawo ruwa a rijiyar ba, to da watakila nan zai shafe kwanaki ciki  har shahada ta zo masa. Sai dai kuma ba makawa komai yana gudana ne da ikon Allah. Allah ya halicci Annabi Yusuf (as) ya sanya shi cikin madaukakan Annabawa masu girma sannan ya hukunta samun tsira da daukakarsa a bisa kyakkyawan tsari.

Annabi Ludu (as) ya sha fama da mutane batattu a zamaninsa, Annabi Ayyub (as) ya nuna juriya a yayin tsananin rashin lafiyar da a ka jarrabe shi da ita, Annabi Haruna (as) ya sha wahala yayin wa’azi kan mushirikan mutane masu kin gaskiya, Annabi Yahya (as) kuma ya yi shahada a hannun masu adawa da kiran Allah ne a zamaninsa, yayin da kuma Annabi Isa (as) ya sha wahalar gwagwarmaya da kaidin munafukai. Gaba daya wadannan Annabawa an jarrabe su da bala’o’i makamantan juna. Haka nan kuma musulmi da suka bi hanyar Annabawan su ma sun hadu da irin wadannan nau’i na bala’i daban daban. Mutanen da suka yi imani bayan sun ga hujjojin da Allah ya baiwa Annabi Musa (as)  sun yi hakan ne bisa yakini duk kuwa da sun san cewa fir’auna zai yanke hannaye da kafafunsu sannan ya kashe su. Sahabban Manzanmu (saas) sun sha gwagwarmaya da kafirai wadanda suka fitar da su daga gidaje da garuruwansu, suka azabtar da su har kuma suka kashe wasu daga cikinsu. Hakika muminai sun gamu da babbar jarrabawar imani yayin da suka shiga cikin ukubar kafirai. Allah madaukaki ya na yi mana bayanin  halin da muminai suka sami kansu yayin da a ka wurga su cikin wutar da kafirai suka hura a cikin wadannan ayoyi kamar haka:

“An la’anci ma’abota rami. Wuta ce wadda a ke hura wa. Yayin da suke zaune a gefenta, suna kallon abin suke aikatawa a kan masu imani. Ba komai ba ne ya sa suke azabtar da su sai don cewa sun yi imani da Allah, mabuwayi, abin godiya. Wanda mulkin sammai da kasa ke gare Shi. Allah mai gani ne a kan kowane abu. Wadanda suke azabtar da muminai maza da mata, sannan ba su tuba ba, suna da azabar wuta kuma suna da azabar gabara.” (Suratul Buruj, aya ta, 4 – 10)

Tabbas Allah mabuwayi shi ne mai yin halitta, da halitta ta musamman, ya halicci Annabawa da muminai da masu wa’azi, wadanda ke mika wuya gare Shi, kuma suke daukaka son Sa fiye da komai, rayuwarsu da mutuwarsu don shi suke yi. Ya haliccesu don aljannarsa, amma a na jarrabarsu a rayuwar duniya. Akwai hikima a cikin wannan; jarraba da wahalhalun da suke fuskanta alamu ne na daukaka, da sadaukarwa da kuma iklasi da tsananin soyayyar Allah mai girma. Annanbawa da tsananin juriya da gaskiyarsu, da sadaukar da kansu, da mika wuya da kuma tsananin iklasi da kyawawan dabi’unsu, suka kara girman matsayinsu. Wadannan kyawawan dabi’u na su wadanda saboda su suka zama mafi daraja da daukaka a cikin ‘yan aljanna, su ne juriya da dogewarsu a bisa bin tafarkin Allah. Kuma Allah mahalicci ya shirya wannan yanayi na wahalar jarrabawa ne don mu da su mu gane muhimmancin sallamawa da mika wuya gare Shi. Babu kokwanto cewa Allah yana bada kariya da tallafawa muminai yayin da kuma yake tare da su a kowane hali. Don haka yana da muhimmanci muminai su san haka don su rika nuna juriya da hakuri a halayen wahalhalu da suka sami kansu a cikin a kan tafarkin Allah. Annabawa da wadanda suka yi imani tare da su kuma suka bi su za su tarar da kyakkyawan sakamako da kyakkyawar rayuwa a  ranar alkiyama saboda hakuri da suka nuna. A wasu ayoyi Allah yana cewa:

“Wadannan za a saka musu da madaukakiyar aljanna saboda hakurin da suka yi, kuma za a tarbe su a cikinta da gaisuwa da aminci. Za su dauwama a cikinta har abada. Makoma da mazauni sun kyautata.” (Suratul Furqan, aya ta 75 – 760

Jarrabawar duniya babbar rahama ce ga musulmi masu imani

Samuwar Allah abu ne da babu tantama a cikinsa. Duk mai inkarin samuwar Allah makaryaci ne, kuma mayaudarin kai, domin hujjoji da alamomin samuwar Allah bayyane suke a ko’ina. Kuma abu ne mai wuya mutum, bayan sanin wadannan alamomi bayyanannu, a ce ya kasa gane samuwar Allah mabuwayi.

Halittar mutum da kwayar halittar rai, da haske, da kwayar zarra, da halittar wannan duniya da sauran duniyoyi daban da ta mu, duk hujjoji ne da suke nuna girman daukaka da gwanintar Allah a halitta. Babu mai musun wannan. Dalilin da ke sa wasu mutane fada wa a cikin rudu na samuwar Allah ba wai don suna musun samuwarsa ba ne. A’a, sai dai abin kawai da yake nauyaya zukatan wadannan mutane wajen mika wuya ga Allah shine kasawarsu wajen fahimtar jarrabawar da Allah ya ke yiwa bayinsa da kuma hikimarsa ta y in hakan. Jarrabawar duniya  ta kan firgita su su dimauce, yayin da wahalhalun da  ke cikinta suke kara nisanta su daga Allah Ubangiji. Tun da yake dama ai kowa  yansan umarnin da a ka yi masa na bautar Allah mahalicci. A wata aya Allah mai girma yana cewa:

“Suka yi musun ayoyinmu bisa zalunci da dagawa, alhalin suna da yakini a kansu. Dubi yadda karshen masu barna yake.” (Suratul Namli, aya ta 14)

Dukkan mutane a cikin zukatansu sun san da samuwar Allah da kuma wajibcin rayuwa a bisa umarninsa, amma duk da haka wasunsu sun kasance suna kidimewa da sanya  kokwanto a duk lokacin da a ka jarrabe su. Abin da ya sa mutanen Annabi Musa (as) suka ce da shi “Ka je kai da ubangijinka ku yi yakin, mu muna nan zaune” (Suratul Ma’ida, aya ta 24), a yayin da suka fuskanci jarrabawa, shine saboda zukatansu sun fifita son duniya a kan yaki don daukaka addinin Allah.

Hakikanin lamarin shine kyakkyawar dabi’a da musulmi suka nuna a yayin hadin guiwar kafirai suna caccakar Alkur’ani, shine kamar haka:

“Wadannan da mutane suka ce da su ‘hakika mutane (kafirai) sun yi taron dangi a kanki, ku tsorace su.’ Amma sai wannan ya kara musu imani inda suka ce ‘Allah ya isar mana, madalla da (Allah) majibincin lamari.” (Suratu Al’Imrana, aya ta 173)

Musulmi wadanda suka mika wuya suka dogara ga Allah a halin kunci, an bayyana su da cewa:

“Wadanda in musiba ta same su sai su ce ‘Daga Allah mu ke kuma zuwa gare shi za mu koma.’” (Suratul Bakara, aya ta 156)

Allah mai girma da buwaya yana fada mana a wata ayar cewa riskar kyakkyawan sakamako da samun babban matsayi ya kan samu ne ta hanyar cin jarrabawa da kyakkyawar dabi’a da mika wuya tare da hakuri da sadaukarwa:

“Kyautata aiki (bauta) ba shine juya fuska sashen gabas ko yamma ba. Sai dai kyakkyawan aiki shine wanda ya yi imani da Allah, da ranar lahira, da mala’iku, da littafi, da Annabawa, da wanda kuma ya bayar da dukiya, da matafiya, da mabarata, da wadanda ke cikin kangi (na bauta) , sannan ya tsaida sallah ya bada zakkah, da wadanda suke cika alkawari in sun dauka, da masu hakuri a halin tsananin talauci da ciwo da halin yaki. Wadannan sune wadanda suka mika wuya da gaskiya. Wadannan sune masu takawa (tsoron Allah).”  (Suratul Bakara, aya ta 177)

Allah kan sanya halin kunci ga al’ummun da suka bar  hanyarsa a bisa wata hikima da kuma manufa. Yawancin mutane suna da halayyar nan ta maida hankulansu kan al’amuransu na rayuwar duniya, su mance da Allah yayin da suke cikin ni’ima da jin dadi. Irin wadannan mutane zatonsu idan suna da hali da wadata shikenan ba su ba samun matsala, har ma suna ganin su ma masu iko ne. Sai dai Ubangiji ya jarrabi al’ummu wadanda suka fada cikin rudun shagala da rafkanuwa saboda wadata da arzikin da Allah ya ba su, duk kuwa da an gargade su cewa su guji girman kai da dagawa. Amma sai suka yi wa Allah tsaurin kai suka fandare, a maimakon jarrabawar da suka sami kansu ciki ta sa su gane su komo kan tafarki don Allah ya yafe kurakuransu. A wata aya Allah ya na cewa:

“Hakika mun aika da manzanni zuwa ga al’ummu kafin zuwanka, sai muka kama su da tsanani da wahalhalu domin cewa ko za su kaskantar da kan su.” (Suratul An’am, aya ta 42)

Tabbas jarraba ta hanyar kunci da tsanani ta kasance babban hanyar tunatarwa ga fandararrun al’ummu. Allah ya bamu labarin halin wata fandararriyar al’umma da mutanen ta suka kasance  cikin jirgin ruwa wadda kuma ke fuskatar igiyar ruwa ta kowane bangare a tsakiyar teku, kamar haka:

“Shine wanda ke tafiyar da ku a doron kasa da cikin kogi, har yayin da kuka kasance a cikin jirgin ruwa, kuna tafiya da iska mai dadi kuna farin ciki da ita, sai kakkarfar iska (mummuna) ta zo musu, inda igiyar ruwa ta taso musu ta kowane bangare, suka yi zaton za a halakar da su, sai suka roki Allah suna masu tsarkake bauta gare Shi suna cewa ‘in har ka tserar da mu daga wannan za mu kasance cikin masu godiya.”  (Sura Yunus aya ta 22)

Ga hikimar wannan jarrabawa. Wadannan mutane, bayan sun fahimci cewa rayuwar wannan duniya ba mai dauwama ba ce, kuma suka tuna cewa duk wani iko da karfi yana ga Allah shi kadai sannan sun san a wannan hali da suke fuskantar halaka daga igiyar ruwa ba su da wata mafita sai komawa ga Allah mai komai da ikon komai. Amma bayan sun kubuta daga wancan hatsari sai suka koma ga halinsu na rafkana.A aya ta gaba Allah yana bayyana mana kamar haka:

“Amma yayin da ya kubutar da su sai ga su suna dagawa a bayan kasa ba tare da hujja ba. Ya ku mutane! Hakika dagawarku kuna yi wa kanku ne. Dan dadi ne na rayuwar duniya, sannan gare mu za ku dawo kuma mu ba ku labarin abin da kuka aikata.” (Sura Yunus, aya ta 23)

Mutane a hankalin kansu sun san abin da ya kamata su yi na daidai. Domin kowane mutum ya san yakamata ya zama cikakken bawan Allah kuma ya dage wajen neman yardarsa. Abin da ke sa wa wasu mutane ba su damu su san girma da karfin Ubangiji ba shine saboda rudin zuciya da shaidan wanda ke fifita musu son rayuwar duniya marar dauwama har su mance da tunanin Allah da lahira. Sai dai kuma duk irin kokarin mutane na ganin sun yi watsi da hikimar Allah ta jarrabawa a duniya, hakan ba zai hana a  jarrabe su ba. Ruduwa da shagala da rayuwar duniya ba zai ba su nutsuwa da salama ba matukar sun yi watsi da al’amarin gaskiyar da zukatansu suka sani amma suka take. Farin ciki da jin dadin da suke hankoron samu a wannan rayuwa duk rudu ne da karya. Tun da sun kasa fahimtar cewa farin ciki da nutsuwa Allah ne ya ke saukar da su ga bayinsa, to yana da matukar wuya su iya samun kwanciyar rai da rayuwar farin ciki kamar yadda suke fata. Wanda ma bai yarda da cewa rayuwar duniya jarrabawa ce ba, to ya ya zai iya gane haka!

Me zai faru a duniya in babu jarrabawa?

Duk wasu abubuwa wadanda saboda su ne mutum ya cika mutum, in babu jarrabawa duk za su gushe. Darajoji da suke samuwa daga kyawawan dabi’u kamar sadaukar da kai, biyayya, hakuri da juriya, soyayya, tausayi, girmamawa, taimako da zumunta duk za su rasa ma’ana. Rigengeton aikata alheri da kuma son kyautatawa sauran mutane shi ma zai zama ya rasa muhimmanci ko daraja. Ka ga kuwa duk wanda rayuwarsa ta zama babu wani abu da ke da kima ko daraja a cikinta, to rayuwar nan ba  ta da amfani.

Soyayyar Allah ce dalilin mika wuyan muminai da juriyarsu a yayin da suka sami kansu cikin halin kunci. Domin in za a kyale mutum sakaka ba a jarrabarsa, to zai koma ne kamar dabba wadda manufar rayuwarta bai wuce ci da sha da yin barci ba. Hakan ne ya kan sa mutum ya rasa sinadarin jin dadin rayuwa. Irin wannan yanayin rayuwa na karya shine masu da’awar akidar Darwiniyanci suke ta kokarin tunkuda mutane cikinta a tsawon shekaru. A rayuwar da ba a jarrabar mutum, wadda kuma babu kyakkyawar dabi’a da sanin yakamata a cikinta, wadda rayuwa ce kawai marar manufa, a nan ba ka iya bambance rayuwar mutum da ta dabba tun da duk suna rayuwa ne, kamar yadda Darwiniyawa ke riya wa,  a bisa hanyar dabi’a guda marar bambanci. Duk lokacin da halitta ta yi watsi da tsarin Allah a doron kasa, daga nan rayuwa ta zama ta karfinka-ya-kwace-ka kenan.

Zai yi kyau a nan mu kawo wani al’amari: Hatta dabbobi an halicce su da ruhin so da kauna, biyayya, sadaukar da kai da kuma tallafawa juna. Saboda haka a yanayin da mutane suka kasance kara-zube ba a jarrabar su da komai, za su zama ba su da manufa ko kyakkyawar dabi’a wanda hakan zai sanya su  kasan dabbobi wajen kaskanci. Allah mai girma yana fada mana cewa kafirai wadanda suke bautar son zuciyarsu dabbobi ma sun fi su:

“Shin kana zaton mafi yawansu suna ji ko lura (su hankalta)? Su fa kamar dabbobi su ke. Kai sun fi (dabbobi) bacewa daga hanya!” (Suratul Furqan, aya ta 44)

Abin da wasu mutane suka kasa fahimta shine: jarrabawa ta na kara wa mutane daraja. Mu kan so wani bawan Allah da ya gabata saboda irin hakuri da juriyar da ya nuna don neman yardar Allah. Annabawa sun sami mafi girman daukaka ne saboda sun bi Allah da hakuri a kan duk abin da ya same su a tafarkinsa. Wanda kuwa ya yi hakuri kan bin Allah, Allah zai daukaka shi ya girmama shi. Su ne mutane masu kauna da son bayin Allah, wadanda kuma, duk da yake cewa an halicci mutum da dabi’ar son kai da hassada, amma ba su nuna haka ba saboda Allah, suka danne zuciyoyinsu a kan kyasi da hassada, suke daukaka sauran musulmi a kan kawukansu kuma suke rokon gafarar Allah a kan kurakuransu. To masu irin wannan siffa dole su kasance ababen ambato da girmamawa a gobe kiyama.

Ubangiji ya kan daukaka mutum mai juriya da hakuri a bisa jarrabar da Allah ya yi masa. A sakamakon dauriyar da mutum ya nuna saboda Allah duk kuwa da bakar wuya da tsananin ciwo da wasiwasin zuciya, amma ya jure ya mika lamari da fatansa ga Allah, to Allah yana kallonsa da girma da tausayawarsa.

Hakurinsa zai zama ado gareshi a cikin aljanna, saboda cewa ita aljanna a na samunta ne ta hanyar nuna hakuri da juriya yayin jarraba a tafarkin Allah, wanda a ka yi don neman yardar Allah kadai. A wannan aya ta Alkur’ani Allah yana cewa:

“Ko kuna zaton za ku shiga aljanna ba tare da Allah ya san wadanda suka yi kokari a cikinu da  kuma masu hakuri ba?” (Sura Al’Imrana, aya ta 142)

Bai kamata a mance da wannan batu na gaskiya ba: Allah mai ikon halitta wanda ya sanya kunci a matsayin jarrabawa musamman don ya jarrabi bayinsa, kuma shine ya nuna hanyoyin magance su. Daya daga wadannnan hikimomi wadanda Allah ya sanar da muminai su a cikin Alkur’ani shine cewa babu wanda za a dora wa abin da ya fi karfinsa:

“Allah ba ya dora wa rai face abin da za ta iya dauka. Abin da ta aikata yana gare ta; kuma abin da ya cancanceta yana kanta.’Ya Ubanfijinmu, kada ka kama mu da laifin abinda muka manta ko muka yi kuskure a kai! Ya Ubanhijinmu, kada ka dora mana nauyi kamar yadda ka dora a kan wadanda suka gabace mu! Ya Ubangijinmu, kada ka dora mana abin da ba za mu iya daukarsa ba! Ka yi mana rangwame, ka gafarta mana, kuma ka yi mana rahama. Kai ne majibincin lamarinmu, ka taimake mu a kan kafiran mutane.” (Suratul Bakara, aya ta 286)

Musulmin da ya fuskatar da lamarinsa ga Allah a cikin kowane irin hali shine cikakken bawan Allah mai biyayya gareshi. Kuma duk irin tsananin kuncin da mutum zai gamu da shi a halin jarrabawa, to ba za a jarrabe shi da abin da ba zai iya dauka ba. Halin kunci da wahala ya kan zama hanyar gyara halin bayi, a jawo su don su kusanci Ubangijinsu, kuma don a kare su daga shagala domin su dace da rahamar Allah madauwamiya ta aljanna.

Bugu da kari kuma, mutumin da ke gamuwa da kunci da wahala zai fi ganin darajar aljanna da tarin ni’imominta. Mutumin da a ka jarrabe shi da talauci da yunwa a wannan rayuwa ta duniya zai fi nuna godiya ga Allah da kara bauta da mika wuya gareshi yayin da ya sami kansa cikin aljanna inda yake samun abin da duk zuciyarsa ta ke bukata cikin sauki ba tare da wata wahala ba. Wanda ya yi hakuri da juriya a bisa tsananin rashin lafiya a duniya, ka san ba karamin farin ciki zai yi ba in ya ga cewa a aljanna babu sauran rashin lafiya ko wahala. Wanda a ka cuta bisa rashin adalci a wannan rayuwa to zai sami kyakkyawar sakayya a lahira inda zai shiga aljanna ya dauwama cikin halin farin ciki da jin dadi, da kuma uwa uba, samun kusancin Ubangijinsa, babu wata tawaya ko nakasa. Misali, musulmi wanda ya kasance gurgu a wannan duniya zai zama mai kafa a cikin aljanna kamar bai taba yin nakasa ba. Haka nan idan mutum makaho ne a duniya to a aljanna ganinsa zai kasance ya ma fi na masu idanun a wannan duniya, inda zai kalli halittu ya gane hikima da kudirar Allah a cikin sha’anin halittar. Idan kuma mutum a na ganinsa mummuna a duniya, to idan ya shiga aljanna za a maida shi kyakkyawa.  Haka kuma ba karamin abin daraja da godewa ba ne ga mumini wanda ya san yadda rayuwarsa ta kasance a duniya inda ya gudanar da ita cikin juriya da hakuri.

Musulmi zai gane rahamar Allah a kansa in ya kwatanta rayuwar wannan duniya da kuma madauwamiyar rayuwar lahira. Don kuwa  rayuwar duniya takaitacciya ce da a ke jarrabar mutum a cikinta, jin dadi ne na dan lokaci. Su kuwa wadanda suka yi hakuri a yayin kunci da wahala saboda Allah, wadanda kuma rayuwarsu gaba daya suka tafiyar da ita a hanyarsa yayin da tunaninsu da ayyukansu gaba daya Allah suka fuskanta, to su ne ke samun mafita a gobe kiyama.

“Wadanda kuma suka yi imani kuma suka yi ayyuka masu kyau, za su kasance masu jin dadi a cikin lambu (na aljanna).” (Suratur Rum, aya ta 15)

 

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/24798/hikima-a-cikin-sirrin-wahalhalunhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/24798/hikima-a-cikin-sirrin-wahalhalunThu, 20 May 2010 23:00:09 +0300
DADUWAN KARFIN IMANIN MUMINI Daya daga cikin manyan alamu ga musilmi da ya sami yardar Allah shine kwanciyar hankali. Hakika, Allah ya halicci dalilai da albarkoki da dama da suke sa musulmi walwala da farin ciki.

Jin cewa Allah wanzajje kuma Mai iko ne yakan sa mutum farin ciki mai dorewa. Duk mai la’akari da ikon Alllah maras iyaka, ilimi da ikon da ya buwayi sama da kasa, to hakika, ya mallaki tunani mai zurfi kamar yadda imanin kwanrai ya tanada. Ikon Allah maras iyaka shi ke raya ruhin dan Adam. Domin Allah Ubangiji tare da iko da kuma gwanintarsa wajen tsara halittatu iri-iri, shi yasa yake tsara halittar kome a mafiya kyawawan siffofi. Duk wqanda yake la’akari da hallitun Allah mabanbanta juna, hakan zai albarkaci tare da fadakarwa gameda nuna halaye na gari wadanda suka dace da Alkurani ta hanyar gabatar da kyawawan ayyuka wadanda Allah yake  so. Gushewar tsoro da bakin ciki ga musulmi shine tushen farin cikinsa.

A ayata 69 ta suratul Ma’ida, Allah ya kore tsoro da bakin ciki ga siffar muninai: “Lalle ne wadanda suka yi imani da wadanda suka tuba (Yahudu) da karkatattu da Nasara, wanda yayi imani da Allah da ranar Lahira, kuma ya aikata aiki na kwarai, to babu tsoro a kansu, kuma ba su zamo suna bakin ciki ba”.

Ga musulmi, duk abinda ya ya faru Alheri ne gareshi. Abu mafi mahimmanci kawai shine ya zamo mai mika wuya ga Allah. Babu abinda zai faru ya cutar da mumini a sarari ko a boye. Koda ya cutu a zahiri, to sakamakon karshe zai zama Alheri a gareshi. Alkurani yana nuni da cewa a koda yaushe masu karyatawa suna gwagwarmaya ne da musulmi kuma kullum suna dana tarko ga muninai. An sha kulle musulmai ba dalili, an sha raunatawa ko ma kashe su. To amma duk da matsannancin yanayin da suka sami kansu a ciki, muddin suna sane cewa haka Allah ya kaddara musu, daga Alheri zuwa sharri, hakan yana nuni da cewa muninai suna cikin hayyaci, walwala da kuma sadaukar da kai. Mika wuya ta hanyar biyayya ga Allah dalili ne na kwnaciyar hankalin  muninai.


Kamar yadda ya sauka a wannan ayar, “Kuma rayuwar duniya, bata zama ba, face wasa da shagala, kuma lalle ne lahira ce mafi Alheri ga wandanda suka yi takawa. Shin ba zakuyi hankali ba? (Suratul An’am, 32). Muminai suna fadake cewa rayuwar duniya ta wucin gadi ice kawai; kuma cewa a lahira ne rayuwar gaske take. Wannan tsagwaron gaskiya da Allah ya saukar a Alkur’ani shine tushen farin cikin musulmi. Wannan karfin imani shi ke karawa musulmi son lahira. Hakan kuma shi ke karfafa fafutukar nemen aljanna ta hanyar samun yardar Allah.

Yin tanadi ga rayuwar lahira, muhimmin al’amari ne wajen karawa mumini himma. Domin duk wanda a ko da yaushe yake cikin tanadi ga rayuwa ta har abada, zai zama fadakakke, kuma yadda yake nazartar al’amura zai dace da abinda ubangiji ya saukar a Alhur’ani.

A Alkurani Allah yana  bawa muminai dadadan labaru na duniya da lahira. Da yardar Allah, muminin mutum ne wanda kome yake gudana domin shi kuma wanda ko wane Alheri yake riskarsa. Akan jarrabe shi a takaitacciyar rayuwar duniyan nan, ta haka kuma yake kusantar lahira. Da’a ta gaskiya ga Allah, matsananciyar kauna, kwadayin lahira, tsoron wuta da kuma neman yardar Allah da son Aljanna duk suna gwada cewa musulmi mai fatar alheri  da zautuwa ne.

 

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/24431/daduwan-karfin-imanin-muminihttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/24431/daduwan-karfin-imanin-muminiThu, 13 May 2010 20:48:28 +0300
YADDA AKA BAYYANA RAHMAR TAUSAYIN ALLAH (SWT) A KUR’ANI
Sa’an nan kuma ya kasance daga wadanda suka yi imani ,kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi.Wadannan ne ma’abuta albarka. (Surat al-Balad: 17-18)

Kamar yadda aka bayyana a cikin ayah ta sama ,Allah (swt) ya umarci bayin sa (su tausaya wa juna )saboda su sami rahmar sa, tare da shiga aljannah da samun saukin wajen  hisabi. Bayin Allah (swt)da suka sadaukar da rayuwar su wajen neman yardar Allah(swt), su kanyi kokari wajen bin umarnin Allah(swt). Kyakkyawar Imanin su da Allah(swt) yasa suka fahimci muhimmancin Tausayi da Rahma,kuma suna da yakinin cewa ba abinda zai faru sai da sanin Allah. Kuma sun gane muhimmancin tausayi da Rahmar ubangiji da yayi masu.kamar yadda aka sani masu imani suna da tunani da  natsuwa,sanin haka yasa  suka zama wayayyu a cikin al’umma,kuma suka tabbata masu  tausayi a cikin jama’ar musulmi.

 Marar mutunci ba zai tausayawa kowa ba,saboda baya tunanin kowa sai kansa,  kuma yana bada muhimmanci ne kawai akan abinda zai amfane shi da son zuciyar sa,shiyasa baya damuwa da halin kunci da wasu jama’ar musulmi suke ciki,bugu da kari ba su tausaya yan uwansu a duk hallin da suke ciki na damuwa.

Dalilin da yasa Bayin Allah(swt) suke sadaukar da kansu wajen taimako da tausayin juna saboda bin umurni Allah (swt).Kamar yadda  aka bayyana a cikin   Ayoyi masu yawa.’’ Allah ne mafi tausayin masu tausayi".Saboda wannan dalili bayin Allah (swt)masu Imani suke daurewa akan duk halin da suka samu kansu a ciki na kunci ko jin dadi.

Kamar yadda Allah ya saukar a cikin Alkur’ani maigirma , "Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamar sa … Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne,Mai jinkai)." (Surat an-Nur: 20). Aya ta sama tana nuna yadda  Allah yake tausaya wa bayinsa ,kuma yadda yake umurtar su dasu tausaya wa junansu,ta haka  suma zasu samu yardar Allah(swt) da tausayin sa.Shiyasa masu Imani suka dauki matsayin tausayi da  muhimmanci,kuma suna fatan samun rahmar Allah(swt),kuma suna tausaya wa al’umma,suna kokarin wajen umurtar al’umma dasu tausaya wa juna domin ta haka ne za’a samu rahmar Allah (SWT).


Gaskiya  Alkur’ani maigirma  yayi bayani akan dukkan al’amari da ya shafi tausayi da yadda za’a tausaya wa juna .Matsayin bayin Allah nagari sune masu tausaya wa da tabbatar da adalci a lokacin daya dace cikin al’umma kamar yadda Allah (swt)yayi umurni.

Kamar yadda aka bayyana  tausayi a Alkur’ani maigirma,Tausayi yana da babban matsayi da girman gaske  fiye da dukkan sauran al’amura.Jama’ar da yawa  basu fahinci manufa da muhimmancin tausayi ba saboda rashin fahimta addini,shiyasa basu san yadda zasu tausaya wa al’umma ba tare da girmama su,kuma basu iya bambanta aiki maikyau da marar kyau, kuma basu tunani akan muhimmancin tausayi tare da duba menene Alkur’ani ya fada akan tausayi.,koda yaushe suna nuna halayen da zasu cutar da kansu da al’umma.;suna yin kuskure wajen magance wasu al’amura da suka taso ,saboda fahimtar su game da tausayi yan a cin karo da yadda Alkur’ani maigirma  ya bayyana tausayi da danganta  karsa da muhimmancin tausayi ga al’umma.Wani lokacin mutane sukan kai da komo wajen fahimtar tausayi, wanda daga karshe yakan zama kuskure tare da sabawa karantar war Alkur’ani maigirma.Irin wannan mummunar fahimta ga tausayi yakan zama cutarwa ga al’umma. Alummar da addini yasa ta rarraba zuwa kungiya  kungiya,za kaga shugabanni suna barin wasu mutane suna aikata wasu aiyuka batare da tunani da kuma  kallon riban  da zasu samu a ranar gobe (kiyama).Misali ,shugabanni  sukan kauda kai daga aikin  haramun da al’umma suke aikatawa,kuma ba tsawatar wa a lokacin ake aikata laifi da Allah (SWT) ya hana ko ya umurci al’umma dashi.      

A binda bayin Allah nagari suka zaba wa kansu a wannan al’amari, shine nuna wa juna tausayi da sauran jama’a, wanda zai jawo hadin kai da farinciki ga rayuwar al’umma duniya da lahira.Wasu lokuta kauna da tausayi da bayin Allah nagari ke nunawa al’umma yakan jawo masu matsala da zargi da wasu al’amura na  wahalar da kai. ,(an-nafs).Kuma suna shan wahala wajen fuskantar marasa gaskiya ta wajen nuna masu hanyar kwarai tare da jawo hankalinsu  su bar aikata haramun. Wannan shine gaskiyar tausaya wa juna, saboda kauce wa barna da illar sa,kuma  suna kokarin koyar da halin kwarai ta yadda za’a fahimci yadda Allah (SWT) ya koyar a cikin Alkur’ani maigirma,  wajen kare shi daga aikata aikin da zai kai shi ga shiga  wuta, kuma ba za’a bashi daman dawowa duniya ba ya gyara aikin sa.A bisa wannan dalili bayin Allah nagari suke karfafa mutane da su aikata aiki  nagari wanda zai sa su samu yardan Allah da tausayin sa, tare da samun Rahmar ubangiji shine shiga gidan Aljannah.Kamata mutum ya sani cewa aikata mugunta bazata kai mutum ga samun rahmar Allah (SWT) ba,kuma aika ta kuskure bisa  ganganci  yana jawo fushin  Allah (SWT) da azaba.

A bisa wannan dalili ,bayin Allah magari suke bin koyarwar Manzon tsira Muhammad (SAW) da halayen sa wanda Alkur’ani maigirma  ya bayyana mana.’’Kuma, lalle ,hakika kana a kan halayen kirki,manya". (Surat al-Qalam: 4)

A wata Ayar Allah (SWT)ya yabi manzon tsira (SAW) da halaye nagari: "Lalle ne,hakika ,Manzo daga cikinku yaje muku .Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa .Mai kwadayin ne saboda ku.Ga muminai Mai tausayi ne,Mai jin kai." (Surat at-Tawba: 128) A saboda wannan dalili bayin Allah (SWT) nagari da suka riki wannan umurni da  koyarwar Manzo (SAW)  suna masu nuna wa juna adalci da tausayi,tare da umartar al’umma su da aikata aiki  nagari saboda kwadaitar dasu samun tausayi da rahmar ubangijin su a gobe kiyama(lahira).

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/23666/yadda-aka-bayyana-rahmar-tausayinhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/23666/yadda-aka-bayyana-rahmar-tausayinSat, 01 May 2010 07:41:04 +0300
KUSKUREN DA WASU MUSULMI MASU RAUNIN IMANI WADANDA SUKA SHAGALA DA RAYUWAR DUNIYA SU KE YI A KALAMAN ADNAN OKTAR Wadansu bangaren musulmi su kan dauki wani tsarin rayuwa na daban marar dadi wanda ya sha bamban da irin rayuwar da Alkur’ani ya nuna. Daya daga cikin kurakuran da irin wadannan mutane masu raunin imani da alfahari, wadanda ba su damu da aikin yada sakon musulunci ta hanyar dabi’u masu kyau ba, shi ne yadda suka dauki rayuwar wannan duniya kawai ba ta wuce mutum ya yi aure, ya haifi ‘ya’ya ya rene su sannan ya tara abin duniya ba. Tabbas wadannan abubuwa ne da ba su sabawa koyarwar musulunci ba. Amma inda kuskuren yake shine musulmi ya mance da babban dalilin zuwansa wannan duniya, wanda shine bauta da bin dokokin Allah, ya ta’allaka kawai kan aure da haifar ‘ya’ya, da kin tafiyar da ni’imomin da Allah ya yi masa akan tafarkin addini inda ya kan tafiyar da daukacin rayuwarsa cikin hanyar gulma da cin naman sauran musulmi alhalin ya watsar da kyawawan dabi’u na addini.

Adnan Oktar ya yi cikakken bayani a kan irin halayya da dabi’ar mutanen da suka yi kuskuren fahimtar tsarin musulunci a hirarraki da dama da a ka yi da shi inda ya kan yi kira ga al’ummar musulmi don su guji fadawa cikin irin wannan halayya marar kyau.


Babban dalilin samun rarraba a tsakanin musulmi a tsawon shekaru da kuma irin tashin hankali da zaluncin da a ke wa musulmi a sassan duniya daban daban, shi ne cewa wasu musulmin sun dauka rike sallah kadai da azumi da zuwa hajji sun ishe su addini, don haka ba ruwansu da al’amuran da ke da bukatar mika wuya da sadaukarwa domin ba abin da ya dame su kamar holewa da jin dadin rayuwar ni’ima da suke ciki, ba sa ko tunani game da matsalolin da ‘yan uwansu musulmi suke fuskanta a sassan duniya.

Misalin irin musulmi masu raunin imani da son kai, wadanda suke ruduwa da rayuwar duniya, suka yi watsi da kyawawan dabi’u na addini

“Babban burinsu shine su yi Aure Kuma su shiga kasuwanci”


“Akwai wasu mutane, kamar wadanda a ka bayyana, masu ra’ayin mazan-jiya ne koda yake suna da ra’ayin addini. Sun kasance suna aiki ko wani nau’i na kasuwanci ko sana’a. Suna da ‘ya’ya mata guda uku da kuma namiji guda daya. Shi dan ya na karatunsa a kasar waje, yayin da ‘yan matan kuma suke zaune a gida. Shin ka san ko me ‘ya’ya matan suke yi a gidan? Kawai a na jiran su girma ne a yi musu aure su ma su shiga haifar ‘ya’ya, iya manufar kenan ba su da wani buri. In ka tambayi mijin me ya sa a gaba, shine ya sami makudan kudi ya zama fitaccen dan kasuwa. “Wannnan shine buri na,” haka zai fada. “Me kuma ya rage banda wannan,” in ji shi. “In muka gaji da zama wuri daya, mu kan tafi Umra.” Ya kan rataye dardumar siliki mai hoton Ka’aba a bangon dakinsa, shi ke nan sai ya ci gaba da shekewarsa.” (An dauko daga hirar da Adnan Oktar ya yi da tashar talbijin ta Kanal 35 da Kanal Avrupa a ranar 31 ga Janairu, 2010.)


Musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al’ada, ko matsayin mutum a cikin al’umma ko kuma  kowane irin ma’aunin bambanci na duniya. Allah ne kadai ya san matsayin kowane mutum ta fuskar takawa, imani da kuma kusancinsa ga Allah mahalicci. Don haka Allah ya haramta wa muminai masu imani yin maganganu sabanin haka. Don mutumin da ya ce “Na yi imani” to ya zama lalle mu kyautata zato a gareshi tare da taimako da karfafarsa a duk lokacin da yake bukatar hakan.


“Sukan bayyana kansu a matsayin waliyai”

“Na sha ganin mutane suna tattauna darussan addini inda sukan dauki wani salon karya na daban don su nuna wa jama’a wai lalle suna da ruhin addini. Su kan daga kai suna duban sama, su yi tamkar suna tafiya ne a kan gajimare, ga kida kuma na tashi daga bayansu, suna riya wai su sufaye ne. Su kan yi wasu abubuwa da suka sabawa hankali, tare da kalamai a cikin wata irin murya da ba a iya gane abin da suke fada. Na sha ganin irin wadannan mutane da yawa. Ka ga suna wasu abubuwa kamar a irin wasan kwaikwayon sinima. In za ka tsaya ka kare musu kallo za ka ga dabi’arsu ta fita daban. Ko mutanen da suke nuna su waliyai ne; in suna magana sai su dinga daga kai sama don a ga kamar suna nazari ne. Da irin wannan halayya suke ambaton Annabinmu (saas) a maimakon su yi bayaninsa cikin hankali da hikima yadda kowa zai fahimta. Me ye ma amfanin hakan? Wa yace sai lalle sun yi wasu shu’umce shu’umce a cikin addini? Alkur’ani ya riga ya ba mu hujja, dama Alkur’ani shine tushen dalilai da hujja. Alkur’ani shine hujjarmu a duniya, kuma shine hujja ga dukkan mutanen duniya baki daya. Mutum mai hankali da basira shine wanda ke rayuwa a kan koyarwar Alkur’ani. Mutum mai hankali da wayo ya kan kara samun hikima idan ya rungumi koyarwar Alkur’ani. Tabbas basira ta kan samu da sannu sannu. Ba a haifar mutum da basira, sai dai ya kan same ta ne bayan zuwansa duniya. Haka nan shi ma hankali a kan sa wa mutum ne sannu a hankali, ma’ana babu wanda ke zuwa da hankalinsa cif a dunkule. Sannan sai batun yin kalamai da wasu harsunan waje, kamar latin ko larabci. Alal misali, mutanen turkiya ba sa jin harshen larabci, kuma kadan ne daga cikinsu su ke jin yaren. To don haka, me ya sa dole wai sai harshen larabci za a rika amfani da shi koda yaushe bayan ba kowa ne  ke jinsa ba? Kuma da ma mutanen suna fahimta to da babu laifi, hasali ma ba don mutane su koya a ke yin magana da yaren ba. To tun da ba da manufar koyarwa a ke yin sa ba, ka ga a na yi kawai don alfahari da nuna sani. Ka ji a na cewa “Kai, wannan mai ilimi ne.” Mu kan yi mu’amalarmu ta yau da kullum a cikin harshen Turkanci, cikin gwaninta da nakaltar harshen. Amma in za mu rika cakuda harsuna kamar mu rika cudanya Turkanci da karin furucin larabci abin zai zama bambarakwai. Ya kamata mu fahimci gaskiya. Misali, da turkanci mu kan ce “Ikhlas,” wato mutum da ke bauta tsakani da Allah da kyautata ibada, wannan shine abin da kalmar ta ke nufi a turkanci. Amma da an ji mun furta ta da “Ikhlas” mutane sai su ga kamar mun bata furucin kalmar ne, mun fada ba daidai ba. A haka ta ke a larabci, amma in a ka cudanya ta da turkanci sai ta bada wata ma’ana daban. In kuma mutum ya kasa furta kalmar daidai, to wannan kuma wani abu ne daban. Kuma rashin gaskiya ne mutum ya rika kokarin nuna shi mai ilimi ne ta hanyar kakale. Ya kamata mu yi abu da gaskiya ba don riya ba. Ba a ce dole sai mutum ya yi larabci kamar malamin Islamiyya ba. Kamar mutum yana alfahari ne da cewa “Na fi ku ilimi, ku zo in koya muku.”

Babu wanda ya san komai a cikinmu, Allah ne ya kimsa sani ga mutane kuma Shine ya ke kaddara furucinmu da kuma jin mu. Allah ne ya ke yin komai, mu tamkar kayan aiki ne a hannunSa. Mutane holoko ne. Ya zama wajibi mutum ya yi amfani da sassaukar hanyar sadarwa in yana so a fahimci sakonsa. Kuma hakan ya shafi lamarin fassarar Alkur’ani, in da ba a son rikitattun bayanai marasa kan gado da rudarwa. Duk wayo da fasahar mutum, in ya yi zancen shirme dole za a gane.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar da tashar Kocaeli da Mavi Karadeniz ranar 26 ga Janairu, 2010.)

“Muminai maza da muminai mata mataimakan juna ne. Suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani da mummuna, sannan suna tsaida sallah, da bada zakka kuma suna bin umarnin Allah da manzonSa. Wadannan Allah zai yi musu rahama. Allah mabuwayi ne, mai hikima.” (Sura Tauba, aya ta 71)

“Su kan gaskata duk sharri ko kazafi da a ka yi wa musulmi ba tare da bincike ba”

“Gaskata karairayin kage na ‘yan kungiyar asiri ta masons, da ‘yan kwaminis, ko karairayin ‘yan kungiyar Ergenekon, zai iya jawo wa musulmi wahala a ranar alkiyama. Duba ka ga yadda Allah mai girma ya ke cewa “Idan fasiki (wanda ba ya aiki da dokokin Allah) ya zo muku da labari, ku bincika.” Ku binciki gaskiyar labarin, don ku gani da idannunku, ku ji da kunnuwanku. Don kada ku yi saurin gaskata shi. Sai dai yanzu ba haka ne yake faruwa ba. A yau idan a ka buga labari a kan musulmi a cikin jarida ko mujallun makiya musulunci sai ka ji mutane na fadin “Kai, kai,  kai, ka ji abin da ke faruwa.” Suna zaune a gida sun harde kafafu suna kurbar shayi, ba sa wani kokarin taimakon addini banda holewa da jin dadin rayuwa, da shagalta da harkokin kasuwancinsu da kuma kula da jin dadin ‘ya’yansu tunda suna ganin ba wata matsala da ke damunsu a duniya. A daya bangaren kuma mutane ne da ke sadaukar da duk abin da suka mallaka a tafarkin Allah, kuma sun kasance suna gudun duniya Da shiga cikin hatsari, kuma su ne a ke wa sharri da kage, a ke zaluntarsu tare da wulakanta su. Duk da haka, sun kasance suna biyayya da gaskata wa ga wadancan nau’in mutane da ke kwance cikin gidajensu suna karanta labarai a jaridun makiya ‘yan kungiyar asiri. Babban abu kuma shi ne yadda a ka bar shi ya kare kansa da kansa. Sannan sauran mutanen can da babu ruwansu da addinin ko yada kiransa su ne za su zo suna yanke hukunci a kansa. Saboda haka sai su baro wa musulmi mai aikin yada addini sabon aiki; a maimakon shagalta da aikin addini, sai ya koma yana kokarin wanke kansa daga sharrin da suka dora masa. Alhali. Abin da ya kamata su wadancan cima-zaunen mutanen su yi shine su ce “Abokina, kyale ni in yi addini, bari in binciki gaskiyar labaran da fasikin nan yake yadawa, kar ka yi saurin gaskatawa. Zan yarda ne kawai da abin da idanuna ko kunnuwa na suka tabbatar mini cewa gaskiya ne.” Amma ba su yin haka. To, me rashin yin haka ya ke haifarwa? Ladan da musulmi zai samu zai ninka daga goma zuwa miliyan. Ka ga kenan wadancan masu kagen su ne dalilin samun ladan musulmi. Kuma wannan shine hikima a cikin halittar su, domin da babu mutumin da ke gaskata labarai daga wajen fasikai, da ladan da musulmi zai samu ya takaita. Su ne ke kara nauyin ladan musulmi, saboda haka halittarsu ma hikima ce babba. Ina fadin haka don mutane su san ainihin gaskiya don su san abin da za su tarar a ranar lahira. Ko ba  komai, ta wata fuskar su ma wadannan mutane suna da na su amfanin!” (An ciro daga hirar da Adnan Oktar   ya yi da tashar Adiyaman Asu da Kral Karadeniz a ranar 25 ga Janairu, 2010.)

“Kafirai mataimakan juna ne. In ba ku aikata ba fitina za  ta afku a bayan kasa da barna mai yawa.” (Suratul Anfal, aya ta 73)

“Mata wadanda ke da irin wannan tunani ba ka ganin su cikin masu kokarin tabbatar musulunci ta hanyar gwagwarmayar ilimi”

“Abinda nake fada game da dankwali (marufin  kai) na mata yana da matukar muhimmanci. Akwai ‘yan mata da yawa masu kishin addini. Ran nan wata matashiya ta zo waje na, kanta a kasa cikin kunya da kamun kai. Na ce da ita “Shin wace rawa ki ke taka wa a jihadin addini da kokarin yada addinin?” Ta ce “A’a.” Shin tana cikin wata kungiyar addini? Shi ma ta ce a’a. Na tambaye ta na ce me ya sa? Ta ce tsananin kunyarta shi  ya sa haka. To me ye burinta a rayuwa? Ta ce aure. “Ina son nima in sami iyali nawa.” Wannan hakika abin haushi ne. Shin yanzu lokaci ne da mace za ta zauna kawai a gida tana zaman aure? Shin haka matan sahabbai suka zauna kawai a cikin gidajensu? Matan sahabbai sun fito sun taka rawa a fagen jihadi. Aisha (ra) uwar muminai ta kasance tana tara matan sahabbai tana koyar da su ilim, kuma ta kan fita ta yi aikin isar da musulunci ga mushirikai da yahudawa. Shin ko ita ba kyakkyawar mata ba ce? Ta yi soyayya da Ma’aiki (saas) kuma ta yi aure don Allah da cika bautarSa. Amma kuma ba ta zauna kawai a gida ba, ta kasance cikin jihadi koda yaushe. To ko shi Ma’aikin Allah (Saas) bai yi zaman dirshan a gida ba, kullum yana cikin tafiye tafiye a kan tafarkin jihadi da yada addinin Allah. Shin ba haka ya kasance yana yi ba ne? Irin haka ya kamata musulmi su kasance. Amma sai ga shi suna zaune dirshan a gidajensu cikin kabilunsu.” (An ciro daga hirar Adnan Oktar da tashar Gaziantep Olay a ranar 30 ga Janairu, 2010.)

“Suna aibata masu aikin yada addini”

“Yayin da daya bangaren na musulmi ke kokarin addini da yada kiran Allah su kan gamu da aibatawa da cin mutunci a shafukan jaridu, inda a ke cewa suna yada ta’addanci. Shin kanka daya yake kuwa bawan Allah? Ka  yi aure kawai ka tara ‘ya’ya, shi ne burinka! Su kan ce in wa’azi ne ka yi wa ‘ya’yanka mana. Su kan ce suna da ‘ya mace ko biyu. Wannan a gurin su shi ne wa’azi ga mutane. An san Annabi (saas) ya yi wa’azi, to amma kai ba kamarsa ba ne. Shin ina ka samo wannan ra’ayi naka na yada addini? Batun “Umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna,” bai dace ba a wannan zamani. Wannan aikin Annabi (saas) ne ba naka ba. Su kan ce aikin mutum shine ya zauna a gida yana cin shinkafa da fisgar cinyar kaza yana korawa da shayi ko lemo. Wannan kuwa ya fi yin kama da kaucewa daga sahihiyar turba. Koda yake, akwai mutane da ke da kyakkyawar niyya a zukatansu, amma dolanci ya dakushe su. Wadannan ba sa cikin wadancan da na bayyana halayensu a baya. Kuskurensu a nan shine su kan yaudari kansu ta hanyar fakewa da wani abu da ke shagaltar da hankulansu wai da nufin samun nutsuwa. (An ciro daga hirar Adnan Oktar da tashar Kanal 35 da Kanal Avrupa ranar 31 ga Janairu, 2010.)


Musulmi a musulunci cike suke da shu’urin soyayya, da aminci inda suke zaune cikin fahimta da son juna. Duk al’ummar da ke da irin wadannan dabi’u ta fi saurin habaka da samun ci gaba. Har ila yau, wani babban abu shine wadanda ke kokari  tare da karfafa hadin kai da son juna Allah ya yi musu alkawarin taimako da  karfafawa. Shi ya sa a ayoyi da dama na Alkur’ani Allah ya ke gaya musu kada su rarraba, in suka yi haka sai karfinsu ya tafi kuma rauni ya mamaye su. Daya daga cikin ayoyin ita ce:
“Ku bi Allah da ManzonSa kuma kada ku yi jayayya a junanku sai ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri. Allah yana tare da masu hakuri.” (Suratul Anfal, aya ta 46)

Kyawawan dabi’u da ya kamata a san musulmin kwarai da su

“Dabi’un Alkur’ani dole ne a gansu a aikace, ba kawai a karance ba”


“Maganar mayafi (lullubi) ta zo a cikin Alkur’ani a Suratun Nur da Suratul Ahzab, don haka ba abin da za mu kara a game da bayanin lullubi. Zan yi magana a kan wani abin daban. Don maganar lullubi ta fi shekara 1400 da samun umarninta. Irin mutanen da na ke ta magana a kan su suna sanya mayafi su rufe kansu, amma ba ruwansu da sallah, ko azumi ko kuma wani aikin addini. Sai dai an fi jin kan su wajen yada gulma da ayyukan batsa. Wadannan su nake suka, ka gane? Amma in banda wannan ba ni da wata matsala da sauran musulmi na kwarai. Akwai wani Hadisi inda Manzon Allah (saas) ya ke cewa “A karshen duniya za a sami mutane masu rawani dubu saba’in a tawagar Dujjal.” Ba wai ina kin rawani ba ne don kuwa Manzon Allah ya daura rawani a kansa.  Mun kasance ni da abokaina na tsawon shekaru muna sallah a masallatai da rawuna a kanmu, ko ban yi haka ba? Daga shekarar 1983 zuwa 87 mu kan daura rawuna mu sake su har gadon bayanmu don yin koyi da sunna, a haka mu ke sallolin jam’i a wancan lokacin, kowa ya sani. Ba ni da matsala a kan rawani in dai a masallaci ne, amma banda a cikin gari, tun da tsarinmu bai tafi a kan haka ba. Sa’annan tsaida gemu shi ma sunna ne, da ya zo daga Annabinmu (saas). Wasu mutane za ka gan su da dogayen gemuna, amma mutanen banza ne. Ba sa fatan tabbatar musulunci ko kokarin isar da sakon musuluncin. To me zan ce ga irin wadannan mutane? Kuma ta ya ya zan yi shiru bayan wadannan mutane suna ta tafka barna? Matan kuma za ka gan su da lullubi, amma ba abin da suka sa a gaba dare da rana sai gulma. Manufarsu a rayuwa su yi aure kawai. Su kan tsani ‘yan matan da ba sa lullubi, kamar su din wasu waliyyai ne. Amma watakila gara su ‘yan matan ma sau dubu da su ta fuskar tsarkin zuciya. Yarinyar da suke gani ba lullubi har suke tsanarta tana kasancewa ta shiga aljanna su kuma su fada wuta. Shi ya sa a addini ba a son alfahari da girman kai. Har sai mutum ya kasance mai kyakkyawar dabi’a da nuna soyayya, da tausayi da kuma yin rangwame ga mutane, kuma ya guji gulma da zunden jama’a.” (Daga hirar Adnan Oktar da tashar Gaziantep Olay ranar 30 ga Janairu, 2010.)

“Wadannan suna rigengeto zuwa ga alhairai, kuma za su tarar da su. Ba ma dora wa rai sai abin da za ta iya. A gurinmu akwai littafi wanda yake furuci da gaskiya. Su ba za a zalunce su ba.” (Suratul Mu’minun, aya ta 61 – 62).


“Wajibi ne ga mata musulmi su zama masu jarunta, mutunci da kokari a maimakon zaman dirshan da rashin katabus”

“Abu na biyu, shi ne matsayin mata musulmi tun da yake musulunci ya hada maza da mata ne, domin kusan matan ma sun fi yawa ko kuma rabi da rabi a ke. Tun ba yau ba a ke danne hakki da matsayin mata. A kan ce wai wacece ita? Ta ce ita ce mace. To me ye aikin ki? Aure. Sannan ki haifi ‘ya’ya, ki zama uwa, shi kenan! Ban da wannan ba ki da wani aikin kuma? Babu, shi ke nan. Sai dai ba haka ya dace ba, bai kamata mu rika takure rayuwar matanmu ba. Abu daya shine, wajibi ne ga mace musulma ta zama mai jarunta, mutunci da kokari. Wajibi ne ma mace ta fi namiji nuna juriya da kokari. Domin mata a bisa dabi’a sun fi kwarewa wajen iya sadarwa da isar da sakon musulunci. Don haka rawar da za su taka tana da matukar muhimmanci. Matar da ke maida kanta doluwa, ba ta amfanar al’umma da komai, me ye amfaninta! Dole ne matanmu su zamo masu lura da basira.” (Daga hirar Adnan Oktar da gidan talbijin na Adiyaman Asu da Kral Karadeniz ranar 25 ga Janairu, 2010).

“Wajibi ne mu guji rarraba a musulunci”

“Mafi yawan ‘yan matan musulmi ba sa shiri da junansu, inda har ta kai wasunsu ma ba sa yin magana da junansu saboda kawai bambancin kungiya da ra’ayi. Ita wannan tana cikin wannan kungiya, ita ma waccan tana da kungiyarta daban, don haka ba sa ma’amala da juna. Shin me ya sa haka? Saboda ra’ayinmu da nasu ba daya ba. Sai dai wannan ra’ayi namu da su din nan ba karamar illa yake kawo mana ba. Bari mu bada misali da daliban Suleiman Efendi; mazansu da matansu mutane ne masu gaskiya da kyawun dabi’a. Amma wani lokacin ba sa yin magana da junansu kawai saboda sabanin tunanni. Haka nan in muka dauki misalin daliban Nur, su ma wasu lokutan ba sa shiri da junansu. Su kan daukarwa kansu wani irin tsattsauran ra’ayi marar kan gado. Wannan kuwa sam ba daidai ba ne. Mu dauki misalin ‘yan mata daga cikin mabiya Fathullah Gulam – masu biyayya ta sau-da-kafa. Ko ba komai dai ‘yan uwanmu ne su. Amma kuma akwai wasu gungun mutane, wadanda saboda karatun jaridar Yeni Asya da su ke yi, suka daina magana ko gaisawa da junansu. Wannan wata baudaddiyar fahimta ce marar kyau. Alhalin an so ne da su rika son juna da taimakon ‘yan uwansu, a gansu har suna cin abinci tare. Kuskure ne mutum ya ce dole sai wani ya dauki irin ra’ayinsa. Kowa ya rike ra’ayinsa a girmama juna shine al’amarin gaskiya. Amma ka ce sai ka jawo wani ya watsar da ra’ayinsa ya dauki naka, sam ba daidai ba ne. Alal misali, bai da ce a tilasta wa kirista karbar musulunci. Hakkinka kawai shine ka yi masa wa’azi da cikakken bayanin samuwar Allah da dayantakarSa a tsanake. A na isar da sakon Alkur’ani ne cikin hikima ba da barazana ko karfi ba wadda za ta sa wanda a ke yi wa wa’azin ya kasa sakewa balle ya fahimci sakon. Kuma dole ka girmama na sa addinin, kuma ka saurari na sa bayanin. Babban laifi ne musulmi su shiga fada da gaba a junansu saboda sabanin ra’ayi kawai. Girmama juna shi ke jawo shakuwa har a sami fahimtar juna. Rashin tattaunawa shi ke jawo baraka da rashin hadin kan musulmi.” (Daga hirar Adnan Oktar da tashar Adiyaman Asu da Kral Karadeniz ranar 25 ga Janairu, 2010.)


“Ya ku wadanda suka yi imani idan kun  fita zuwa yaki a tafarkin Allah to ku bambance. Kada ku ce da wanda ya zo muku a musulmi ‘Kai ba mumini ba ne’ saboda kwadayin samun duniya. Allah a wajensa akwai ganima mai yawa. Kamar haka ku ka kasance a baya amma Allah ya yi muku tagomashi. Saboda haka ku bambance. Allah yana sane da abin da ku ke aikatawa.” (Suratun Nisa, aya ta 94)

“A maimakon neman ganin aibun juna, dole musulmi su rungumi hanyar hadin kai da son juna”

“Matsala ta uku ita ce yadda musulmi ke suka da cin naman ‘yan  uwansu. Matan kuwa su kan taru a gidajensu da sunan wani lamarin addini, amma sai su buge da gulma; wance ta yi kaza, su wane sun yi kaza... A maimakon bata lokaci a kan wadannan gumace gulmacce, me zai hana su yi tunanin kalubalantar zindikancin masu ra’ayin Darwin da ýan akidar zahiranci (materialists)? Ko su rika ilmantar da juna kan sha’anin addini da ya shafi imani, tsoro da kuma son Allah. Amma don me wasu musulmi za su taru suna cin naman ‘yan uwansu musulmi? Misali, akwai wani majalisi da a ka yi a wani wuri, inda bayan an karanta littafin Risalat Nur sai kuma a ka shiga gulma da zunde. Ba na ce kowa ne ke yin hakan ba, amma dai da dama haka a ke yi. Ba wanda ke son a rika yi da shi bayan idonsa. To in haka ne meye amfanin gulma, in banda hali ne na mutanen banza. Bai kamata mutane su rika cin naman junansu ba; zai fi kyau su so juna tare da girmama juna, ta haka ne Allah zai taimake su. Su kasance masu fadin “Ya Allah, ka haskaka duniya da haskenka, ka gaggauto da tabbatar musulunci a duniya, ya Allah a cikin wannan karni.” Irin addu’o’in da ya kamata su rika yi kenan don neman taimakon Allah da daukinsa. Shin a baya ka taba ji ana maganar soke bizar shiga kasashe ko batun hadin kan duniyar musulmi? Amma yanzu akwai muhimman ci gaba da a ka samu musamman wajen yunkurin kafa cibiyar hadin kan musulmi ta Turkiya. Lokacin da na fara magana kan wannan al’amari kimanin shekaru biyu da suka gabata, mutane sun yi ta mamakin abin da na ke fada, saboda ba su taba zaton haka ba. In da za ka duba jaridun wancan lokaci, za ka ga ba wani abu da suka buga game da wannan al ;amari don kuwa da niyya suka ki bugawa. Amma abubuwa sun canja yanzu.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar a tashar Gaziantep Olay ranar 30 ga Janairu, 2010.)

Musulmi ba sa gudun wahala a tafarkin Allah. Dole musulmi su sallama kansu gaba daya”

“Su kan ce kullum wuridin safe da na yamma ba sa wuce su. Mata kuma kan ce kullum ba sa rabuwa da dankwali. Kuma sallah, su kan ce a koda yaushe a kan lokaci suke yinta. Kwarai wannan abu ne mai kyau, sai dai  kowa ma yana yin haka. Mace tana iya daure kanta da dankwali a tsakar gidanta, ta kuma bada faralinta a dakinta. Matashi kan shiga makaranta, har ya kammala karatunsa, sannan ya yi aure,  ya maida  hankalinsa kan aiki da iyalinsa. To amma irin wannan ba ita ce siffar musulmin da Alkur’ani ya bayyana ba. Shi musulmi yana sallama kansa ne gaba daya ga Allah mahaliccinsa, kuma yana yin hakan ne ta hanyar nisantar jin dadin rayuwa mai rudi. Domin Manzon Allah (saas) ya gujewa dadin duniya ya sadaukar da rayuwarsa a hanyar bautar Allah. Shin ba ka jin da Annabi (saas) ya ga dama shi ma da sai ya yi zamansa a gida, amma ya fito zuwa hijira don bin umarnin Allah, har ya zauna cikin kogo? Ya yi tafiye tafiye masu yawa inda har Habasha sahabbansa sun je a tafarkin hijira saboda daukakar addinin Allah. Hanyoyin sun kasance masu hatsarin gaske, amma haka suka yi dogon zagaye ta sassan Afirka. Yara ‘yan shekaru 15 zuwa 16 duk sun amsa kiran Manzo suka yi hijira inda suka tafi suka bar iyalinsu don daukakar addinin Allah. Ga sauran matasa kuwa sai su ce “kun kyauta, kun cika masu wayo. Kun cika masu biyayya da soyayya ga iyalenku tunda ba ku bi Muhammad (saas) ba. Wannan shine matukar sanin hakkin iyali. Ga ki yarinya mai saukin kai, mai kawaici da tsaida sallah, ga ki mai ilimi, kuma ga aikinki kina yi, to me ye naki na shiga wata  harkar jihadi! Haka kuwa wasu suka zauna ba su bi Manzon Allah (saas) ba; gani suke sun fi kowa wayo. Su kuma sahabbai suka bi manzo suka yi hijira, kuma suka sami rabo a wannan duniya da kuma na lahira mai zuwa. Mu kuwa yanzu ai ko sawunsu ba ma ganowa, ko ba haka ba? Ladan su a lahira dauwamamme ne.” (An ciro daga hirar Adnan Oktar a tashar Talbijin ta Samsun Aks da Kayseri ranar 27 ga Janairu, 2010.)

Wajibi ne musulmi su tsare hakki da taimakon junansu. Dole ne su guji dabi’ar nan ta kiyayya da juna saboda dalilin kungiya, kabilanci ko bangaranci. Koda yake wannan ba zai hana in an ga wani bangare yana kan kuskure ko bata a dauki matakan gyarawa ba. Misali, nuna adawa da kokarin tabbatar tsarin musulunci babban laifi ne da ke bukatar daukar mataki a kai. Ko kuma in a ka ga wani yana  fassara ayoyin Alkur’ani bisa son rai, to abu ne da mmusulmi ba za su yi shiru suna kallo ba. Amma banda haka, zai yi kyau musulmi su riki harshe guda da zai karfafa soyayya da hadin kansu.” (An ciro daga hirar Adnan Oktar a tashar Adiyaman Asu da Kral Karadeniz ranar 25 ga Janairu, 2010.)


“Musulmi wajibine ya zama neman yardar Allah shine babban burinsa”

“Manufa da burin mutum  ya kasance neman yardar Allah da rahamarsa a birbishin kowace manufa. Musulmi kan je makaranta ko wurin aiki, ya nemi aure, har ya yi gudun hasara. Kamar dai in ce ne, duk daya gare ni, da na so sai in zauna gida abina. Ka ga kenan ba mai kama ni, balle a daure ni har labari ya bazu a jaridu cewa an kama ni. Haka nan ba mai kaini asibitin mahaukata, ko a tsaida ni gaban kotu in fuskanci hukunci. Ba wani abin ki da zai same ni. Ka ga sai in maida hankalina sosai a kan harkokin kasuwanci na. Amma kuma a karshe  ina iya shiga wuta a ranar lahira, Allah ya kiyaye. Saboda haka ba karamin wauta ba ce mutum ya zaci yin hakan wani wayo ne; wato mutum ya rika yi wa wadanda suka sadaukar da rayukansu a jihadin neman yardar Allah a matsayin wawaye, sannan ya rika daukar kansa shine wayayye, bayan kuma a hakika ba haka ba ne. Rayuwar wannan duniya takaitacciya ce. Ba mun zo duniya ba ne kawai don a haife mu mu haifa, mu ci mu sha kamar dabbobi ba. Shi mutum in an haife shi a na nufin ya taso da bautar Allah, ya kasance bawan Allah mai neman yardar ubangiji ta hanyar aiki da koyarwar Alkur’ani, sannan ya ke fatan dacewa da shiga aljanna a ranar gobe kiyama. Badiuzzaman Said Nursi (shahararren malamin musulunci) bai shafe shekaru talatin a gidan kurkuku wai don ba shi da wayo ko dabara ba ne. A daidai lokacin da yake garkame a kurkuku na tsawon wadannan shekaru talatin yana shan bakar azaba, musulmi da ke waje sun ci gaba da yin azumi, da harkokin kasuwancinsu, suna ci suna sha tare da jin dadi da matansu! Amma kuma wai suna ganin kamar matsayinsu daya da shi da ya sha wahala a tafarkin Allah. Sam ba haka ba ne. Allah zai tambayi kowanensu a ranar lahira. Ma’ana Badiuzzaman shine a kan tafarki madaidaici saboda kokarinsa na daukaka addinin Allah sabanin ‘yan zaman dirshan. Don haka, mutum mafi wayo da hikima shine wanda gaba daya ya mika wuyansa ga Allah mahalicci.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar a tashar Samsun Aks da Kayseri ranar 27 ga Janairu, 2010.)
 ]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/23126/kuskuren-da-wasu-musulmi-masuhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/23126/kuskuren-da-wasu-musulmi-masuWed, 21 Apr 2010 10:50:15 +0300
YADDA MOMINAI SUKE KALLON RAYUWAR DUNIYA
“Rayuwar duniya ba komai ba ce sai wasa da wargi. Lahira – wannan ita ce rayuwa ta hakika, in da sun san haka. (Suratul – Ankabut, aya ta 64)

Allah ya halicci wannan duniya a matsayin mazauni na wucin-gadi don ya jarrabi mutum, ya tsarkake shi daga munanan ayyukansa, ya sanya shi mai tsarkakakke kuma madaukakin ruhi wanda zai kai shi ga samun aljanna, sannan kuma don ya bayyana siffofin kafirai da ayyukansu. Sai dai ‘yan kalilan  ne daga cikin mutane suke yin tunani da lura har su fahimci manufar Allah a cikin lamarin duniya; wadannan kuwa su ne masu imani.

Saboda haka, mutum mumini wanda ya yi imani yana kallon duniya ne ta wannan mahanga wadda Alkur’ani ya bayyana. Bambancinsu da kafirai wadanda ba su da darsashin imani tare da su shine, shi mumini ba ya damfara kansa da rayuwar wannan duniya, sai dai yana kokarin nemarwa kansa kyakkyawar makoma a gobe kiyama. Da ya ke ya san an halicce shi ne “don ya bautawa Allah shi kadai,” don haka a koda yaushe ya ke tuna ayar nan da ke fadin “Ban halicci mutum da Aljan bs sai don su bauta min.”(Sura Zariyat, aya ta 56)Bautar Allah kuwa ba ta takaita ga aikata wasu nau’o’in bauta ba ne kawai kamar kiyaye salloli da yin azumi. Amma abin da ake nufi shine gaba dayan rayuwar bawa ta zama a cikin bautar ubangijinsa ya ke tafiyar da ita. Saboda haka, cikakken mumini shine mutumin da ya tafiyar da gaba dayan rayuwarsa a cikin bautar Allah. Ya san cewa wannan duniya gidan jarrabawa ce, kamar yadda a cikin Alkur’ani Allah ya jawo hankalin mutane ga wannan al’amari cewa: “Hakika mun halicci mutum daga gaurayayyen diyon maniyyi don mu jarrabe shi, sannan muka sanya shi mai ji da gani.” (Suratul Insan, aya ta 2)

Bugu da kari kuma, Allah yana jawo hankalinmu dongane da rudin rayuwar duniya in da ya ke gargadinmu da cewa:

“Ya ku mutane! Alkawarin Allah gaskiya ne. Kada rayuwar duniya ta rude ku kuma kar mai rudi ya rude ku a cikin al’amarin (bin) Allah.” (Sura Fatir, aya ta 5)

Muminai su ne wadanda kyawu da alatun rayuwar duniya ba sa rudar su, duk kuwa da tsananin kyawu da daukar rai da suke da shi. Dalilin wannan kuwa shi ne saboda littafin Allah ya yi musu bayanin sirrin rayuwar wannan duniya filla filla. Kamar yadda Alkur’ani ya ke bayyana mana, ita rayuwar duniya “wasa ce” da “shakatawa” “da ado” “da alfahari a tsakanin mutane” “da kuma gasar tara dikiya da ‘ya’ya.” A cikin wannan aya ta Alkkur’ani, Allah ya buga mana misali wanda ya fayyacce mana matsayin wannan rayuwa ta duniya:

“Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce, da shantakewa, da ado, da alfahari a tsakaninku da kuma gasar tara dukiya da ‘ya’ya. Kamar misalin ruwan sama ne (wanda a sakamakonsa) yabanya ta fita kyawunta ya burge manoma, sannan sai  ta bushe ka ganta ta koma ruwan dorawa sannan ta zama karmami (a warwatse). A ranar lahira akwai azaba mai tsanani da kuma gafara daga Allah da kuma yardarSa. Rayuwar wannan duniya ba komai ba ce face jin dadi na rudi.” (Suratul Hadid, aya ta 20)

Kamar yadda wannan misali ya nuna mana, babu wani abu a wannan duniya face sai ya gamu da tasirin shudewar zamani; komai inganci da kyawun gidaje, da tsala tsalan motoci masu daukar ido, ko lambunan debe kewa masu kyawu, ko kuma matasa masu zalaka a wurin aiki ko sana’o’insu, babu mai iya kubuta daga tasirin shudewar zamani. Komai sabuntar abu zai koma tsoho, matasa majiya karfi da shu’urin rayuwa su zama tsofaffi. Zamani ke hallaka abubuwa masu daraja a idon dan-adam ya maida su marasa daraja da muni. Lokacin da mutum ke ganiya da holewarsa nan da nan kuma sai ya shude ya zama tarihi kamar ba a yi shi ba. Bayan wani lokaci kuma duk wani abu mai daraja ko jin dadi sukan kasance an manta da su. A wata aya Allah yana sanar da mu irin shu’urin da ke sa wa mutum son rayuwar duniya:

“An kawata wa mutum tsananin sha’awa ga mata da ‘ya’ya, da tarin (dukiya ta) zinare da azurfa, da dawakai na kawa, da dabbobi da gonaki. Wadannan jin dadi ne na rayuwar duniya. Amma ga Allah kyawun makoma yake.” (Sura Al’Imrana, aya ta 14)

Muhimmin abin da za mu fahimta a cikin wannan aya da ta gabata shine, cewa ni’imomin duniya yankakku ne ba masu dorewa ba. Don haka bai kamata ga mutum ya kallafa rayuwarsa a kan wani abin cikin wannan duniya ba, domin kuwa ma a bisa al’ada da halittar mutum ta zahiri wadda ta kunshi kashi da tsoka, har sauran abubuwan duniya marasa daraja da dorewa, babu abin da zai sa su baiwa mutum damar kallafa rayuwarsa ga wannan duniya baki daya. Irin ni’imomin da mu ke gani a wannan duniya wani dan yanki ne daga ni’imomin aljanna da a ka gutsuro mana don tuna mana ranar lahira.Masu imani wadanda suka fahimci wannan manufa su kan ci ribar rayuwar wannan duniya. Amma akwai wani abu guda da ya bambanta su da sauran wadanda suka rudu da rudin duniya; saboda su muminai ba sa nuna hadama a kan ni’imomin duniya. A maimakon haka ma, a koda yaushe cikin godiyar Allah suke saboda baiwa da ni’imomin da ya yi musu, domin sun san cewa hakikanin mamallakin komai na duniya shine Allah.

Wadanda ke ganin wai sun mallaki dukiya, ko suna da halitta mai kyau, ko kuma suna da karfin mulki a hannunsu, to hakikanin gaskiya suna yaudarar kansu ne, tun da ba su ne suka halicci wadannan abubuwa da suke tinkaho da su ba. Hasali ma, ba su da ikon halittar koda abu guda daya daga cikinsu, haka  kuma ba su da ikon kare abubuwan daga lalacewa ko halaka. Su kan su ababen halitta ne da a ka halicce su.... kuma wata rana mutuwa za ta riske su, su tafi su bar duk abubuwan duniya da suka mallaka. In muka lura da wannan aya da ke cewa “Wadannan mutane suna kaunar rayuwar wannan duniya kuma suka sanya tunanin rana mai nauyi (lahira) a bayansu,” (Suratul Insan, aya ta 27) za mu gane abin da ya bambanta muminai masu yakini da kuma wadanda suka shantake a rayuwa, domin muminai a koda yaushe a cikin shirin fuskantar rayuwar gobe kiyama suke ba ta wannan duniya ba. Alkur’ani ya kawo mana irin addu’o’in da su ke yi:

“Daga cikinsu kuma akwai masu cewa ‘Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.” (Suratul Bakara, aya ta 201)

A sakamakon iklasinsu da addu’o’in da suke yi, sai Allah ya hada musu ni’imar duniya da ta lahira baki daya. A cikin Alkur’ani Allah ya yi albishir a kan haka:

“Saboda haka Allah ya ba su sakamako na duniya da kuma mafi kyawon sakamakon lahira. Allah yana son masu kyautatawa.” (Sura Al’Imrana, aya ta 148)

“Akwai bushara gare su a rayuwar duniya da kuma a lahira. Babu sauyi a maganar Allah. Wannan shine rabo mai girma.” (Sura Yunus, aya ta 64)


]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22592/yadda-mominai-suke-kallon-rayuwarhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22592/yadda-mominai-suke-kallon-rayuwarWed, 07 Apr 2010 07:38:53 +0300
RAYUWAR MUTUM JARRABAWA CE
Allah ya halicci kowane abu a bisa hakikanin ikonsa, kuma ya hore wa mutum sarrafa sauran abubuwan da ya halitta a duniya. A bayyane yake cewa halittar Allah da yawa a sararin wannan dunya, tun daga kan halittu irin su rana da wata, zuwa ga nau’o’i na iskoki da ke cikin sararin subhana, haka nan daga dabbobin ni’ima wadanda muke samun nama da madara daga jikinsu zuwa kan ruwa, duk an halicce su ne saboda jin dadi da kuma amfanin mutum. Idan har a ka fahimci hakikanin wannan bayani a matsayin hujja, to zai kasance kenan rashin tunani ne mutum ya dauka wannan rayuwa haka take kara zube ba ta da manufa. Tabbas kuwa akwai manufa a cikin wannan rayuwa, kamar yadda Allah ya fada:

Ban halicci mutum da Aljani ba sai don su bauta min. (Suratuz – Zariyat, aya ta 56)

‘Yan kalilan ne kawai daga cikin mutane suke fahimtar wannan manufa ta rayuwa har kuma su tafiyar da rayuwarsu a kan wannan manufa. Allah ya halicce mu a bayan kasa ne don ya jarrabe mu a kan shin za mu bi tsarin dokkin da ya tsara mana ko kuma za mu fandare. Tun a nan duniya a ke banbancewa tsakanin bayin Allah masu bauta ta hakika da kuma wadanda suka yi tawaye ga dokokinsa. Duk ni’imomin da Allah ya yi wa mutum (na halittar jikinsa, da sanya masa tunani da kuma sauran ni’imomi marasa iyaka) abubuwa ne da Allah ya ke jarraba mutum da su. A wata ayar Alkur’ani, Allah yana cewa:

Hakika mun halicci mutum daga digon maniyyi gaurayayye don mu jarraba shi. Kuma muka sanya shi mai ji da gani. (Suratul – Insan, aya ta 2)

Aiki ko nauyin da a ka dora wa mutum a rayuwar wannan duniya shine cewa ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya tafiyar da rayuwarsa a bisa koyarwar Alkur’ani, ya kiyaye iyakokin Allah, da kuma neman yardarsa. Jarrabawar da ke samun mutum a tsawon rayuwa ita ke bayyana wadanda suke tsaye a kan tafarki. Tun da yake kyakkyawan imani da iklasi – imani irin wanda ke ratsa jiki da zuciya amma ba irin wanda mutum zai furta da baki cewa “Na yi imani” kawai ba – shi Allah yake bukata daga bayinsa, don haka ya wajaba ga mutum ya tabbatar yana da imani sahihi, ta yadda babu ta inda yaudarar shaidan za ta ci galaba a kansa har ya kauce daga tafarkin addini. Har ila yau, wajibinsa ne ya tabatar ba ya bin hanyar kafirai batattu, ko kuma daukaka bin son  ransa a bisa neman yardar Ubangiji. Ayyuka da yanayin halayyar mutum a duniya sune za su tabbatar da haka. Allah yana jarraba mutum da halin kunci ko wata masifa, inda ta hanyar juriya da hakurinsa ne a ke gane matsayin imani da sadaukarwar mutum a sha’anin addini. Allah ya yi bayanin wannan a cikin Alkur’ani mai girma kamar haka:

Shin mutane suna zaton za a kyale su haka nan don sun ce “Mun yi imani” ba tare da an jarrabe su ba? (Suratul – Ankabut, aya ta 2)

A wata ayar kuma Allah ya gaya mana cewa wadanda suka ce “Mun yi imani” sai an jarraba su:

Shin ko kuna zaton za ku shiga Aljanna ba tare da Allah ya san wadanda suka yi kokari daga cikinku da kuma wadanda suka yi hakuri (juriya) ba? (Al’Imrana, aya ta 142)

Saboda haka, a bisa hakikanin lamari, yin bakin ciki ko debe kauna yayin tsanani ko jarraba abu ne da bai dace mutum ya yi shi ba. Wannan kunci kuwa ya kan kasance ta hanyar manyan bala’ai ko kuma matsalolin yau da kullum na rayuwa. Saboda haka wajibi ne ga wanda ya yi imani da ya dauki wadannan al’amura da kan same shi a matsayin wani bangare na jarrabawar da a ke yi masa, kuma ya dogara ga Allah da kuma neman yardarsa a koda yaushe. A wannan aya ta Alkur’ani, Allah yana bayyana mana irin kuncin da a ke jarrabar muminai da su kamar haka:

Tabbas za mu jarrabe ku da wani yanki na tsoro, da yunwa, da kuma hasarar dukiya, da rai da ta amfanin gona. Kuma ka yi bushara ga masu yin hakuri. (Sura Bakara, aya ta 155)

Haka kuma Manzo Muhammad (S.A.W.) ya tunatar da muminai da cewa, “Duk wanda ya yi hakuri da ita (jarrabawar da ta same shi) zai sami yardar Allah. Wanda kuma ya kasa yin hakuri da tawakkali zai gamu da fushin Allah.” (Tirmizi)

Ba da halin kunci ko wahala ne kadai a ke jarrabar mutum a wannan duniya ba, hatta halin ni’ima ko wadata su ma a kan jarrabi imanin mutum da su. Allah ya na jarraba mutum da kowace irin falala  ko ni’ima da ya yi masa don ya ga shin zai nuna godiya ko zai butulce ne. Kamar yadda Allah yake bijirowa da al’amura wadanda ke haifar da tasiri a tunani da ra’ayin mutum, saboda haka a halin jarrabawar da mutum ya sami kansa ya kan zama ko dai mai biyayya da dokokin Allah da neman yardarsa, ko kuma mai bin ra’ayin da ransa ya saka masa. Yayin da mutum har ya iya fahimtar halin da yake ciki cewa jarrabawa ce daga Allah, to wannan za a iya cewa ya yi nasara. Amma kuma in har lamuransa a wannan hali ya biyar da su ne a bisa sha’awa da rudin ransa, to ya jefa kansa cikin aikata zunubi wanda zai yi nadamarsa a ranar lahira, kuma zai kasance cikin yamutsi da rashin kwanciyar hankali a rayuwar duniya.

Tabbas, kamar yadda muka bayyana, Allah ya halicci komai a wannan duniya ne a matsayin jarrabawa ga mutum. Irin abubuwa da al’amuran da jahilai suke gani kamar suna faruwa ne a bisa katari ko tsautsayi, to a hakika al’amura ne da suke faruwa a bisa nufi da kaddarawar Allah ta’ala. Daga cikin wannan, Allah ya bada misali da Yahudawa da suka karya dokar hana su yin su (kamun kifi) ranar asabar, sakamakon bin son zuciya:

Ka tambaye su game da Alkarya (gari) wadda ke gefen kogi, yayin da suka karya dokar Asabar – yayin da kifayen ke zuwa musu a ranar da a ka hana su kamun kifi (asabar) amma ranar da babu dokar ba sa zuwa musu. Ta haka muka jarrabe  su saboda sun kasance masu kaucewa daga hanya. (Sura A’raf, aya ta 163)

Watakila yahudawan sun yi zaton zuwa musu da  kifayen suke yi a ranar asabar bisa “katari” ne, sai dai kuma lamarin ya kasance tsararre ne daga Allah a matsayin jarraba gare su. Kamar yadda wannan hikaya ta nuna karara, a cikin kowane yanayi ko al’amarin rayuwa da ke faruwa akwai manufar Allah da kuma jarrabawa. Duk abin da ya sami mumini abu ne da Allah ya hukunta zai same shi don ya fahimci hikima da manufar Allah a cikin lamarin, ya fuskanci jarrabawar da juriya da tawakkali, sannan ya dora dabi’a da rayuwarsa gaba daya a bisa dokokin da Allah Ubangiji ya shimfida masa.
]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22162/rayuwar-mutum-jarrabawa-cehttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22162/rayuwar-mutum-jarrabawa-ceSat, 27 Mar 2010 08:58:19 +0200
ALLAH YA YI BUSA A CIKIN MUTUM DAGA RUHINSA; ASHE ABIN DA MUKE CEWA RAI SHI MA MALLAKAR ALLAH NEA rayuwar bil – adama mutane suna ganin tasirin hikimar Allah ta irin baiwar daya sanya a kwakwalensu. Wannan kuwa wasu maganadison sadarwa ne da ke da ke isarwa da tara bayanai a zuciyar Dan-adam. Kuma koda yake akwai irin wannan al’amari na baiwa a zahirance, mutane kan lura ne kawai da wadanda aka sanya musu cikin kakwalensu. Don haka, a bisa tsarin Allah mai hikima, halayyarmu ta zahiri ta kasance fassarar abin da yake boye cikin kwakwalenmu ne, kuma muna fahimtar duk wadannan abubuwa da ruhin da Allah ya sanya mana; wato ta hanyar gain, da ji, da kuma tabawa da fahimtar su.

Idan mutum ya dubi duk wadannan dalilai na fahimta da Allah ya sanya a cikin ruhin mutum, to lalle zai san cewa muhimmanci ko sirrin hikimar kowane abin halitta yana ga ruhi ne amma ba abubuwan zahiri ba, domin hakan dalili ne da ke nuna ruhi shi ke tafiyarwa tare da sarrafa jiki. Ruhi ko rai shi ke ji da fahimta, yayin da gangar jiki da sauran abubuwan da ke kewaye da mu an tsara su ne a sakamakon abin da ruhi ya fahimta. A bisa dabi’a, naman jiki ko kasusuwa ba sa yin bakin ciki, murna, alfahari, yanke hukunci  kan abu ko yin tunani ba. Ruhi ko rai ne kadai ke iya ji, yin tunani, zabi da kuma yin amfani da hankali wajen yanke hukunci ko bayyana farin ciki da annashuwa. Shi wannan rai ko ruhi da mutum kan ce “rai na,” to a hakikanin gaskiya ruhin Allah ne, kamar yadda ya zo a wannan aya cewa:

(Allah) wanda ya halicci dukkan abu ya kyautata halittarsa, kuma ya fari halittar mutum daga yunbu (tabo). Sannan ya sanya asalinsa daga wulakantaccen ruwa da aka fitar; sannan ya siffanta shi, ya busa masa rai daga ruhinsa, kuma ya sanya muku ji da gani da zuciya (tunani).  Kadan ne ku ke godewa! (Sura Sajda, aya 7 – 9)

Allah ya busa daga ruhinsa, ya sanya idanuwa da zuciya ga mutum wanda ya yi wa baiwa da mafi daukakar halitta kuma ya sanya masa tunani da hankali. Don haka shi wannan ran da mutane suke  ta tutiyar nasu ne, mallakar Allah ne kuma daga ruhinsa ne. Allah, da faffadan iliminsa da ya game komai da kuma karfin kudirarsa mayalwaciya, ya halicci ruhi a mafi kyawun siga da ban al’ajabi don ya kasance a matsayin jarrabawa ga mutane, wadanda bayan mallakar wannan baiwa a gare su kan bugi kirji su ce “nawa.”

An baiwa bil-adama kwakwalwa da ta tattara komai da komai na bayanai da ilmuka. A hankali, mataki mataki, Allah ya ke gina tunani da sanya bayanai a kwakwalen mutane, kuma yana ci gaba da sabunta kaifin tunani da ingancin kwakwalen nasu a tsawon rayuwar kowannensu. Misali, yanzu ga shi kana karanta wannan bayani, kuma nan da ‘yan mintuna abin da ka karanta zai sami gurbin zama a cikin kwakwalwarka (kamar rikoda). Zai kuma ci gaba da kasancewa cikinta na tsawon kwanaki, ko watanni ko kuma na tsawon shekaru ma (ya danganta da karfin hardar kwakwalwarka) inda za ka rika tuno shi daga lokaci zuwa lokaci. Duk lokacin da ka yi amfani da baiwarka ta tunani za ka iya tuno al’amura masu yawan gaske da ke dankare a cikin kwakwalwarka. Wadannan al’amura kuwa sun hada da muhimmai da wadanda ma ba su da muhimmanci ko girma sosai, wadanda kuma ba su kirguwa. Misali, duk da shudewar shekaru masu yawan gaske, amma har yanzu ka kan iya tuno ranar farko da ka fara zuwa makaranta a rayuwarka; ta irin wasannin da ku ka rinka yi da abokanka, da kuma irin farin cikin da ka dinga yi a waccan  rana muhimmiya, duk yana nan daram a kwakwalwarka. Wannan kundin bayanai da ke cikin kwakwalwarka zai ci gaba da kasancewa tare da kai  har ranar da rayuwarka ta kare. Mutane, wadanda Allah ya halicci ruhi kuma ya sanya a jikinsu, sai suka dauka mallakar wannan ruhi a gare su kamar su ne suka kage shi da kansu, wanda kuma wannan babban kuskure ne. Duk yayin da suka tuno da wani al’amari a rayuwarsu, lokacin da za ka ji sun ce “Na yi farin ciki a waccan rana,” “Na yi matukar murna da annashuwa a waccan rana,”su kan yi zaton ikonsu ne ba ikon Allah ba ne ya sa suka iya tuno wa da lamarin.

Kamar yadda aka bayyana a sama, Allah ne ya halicci kwakwalwa da tunani ya sanya wa Dan-adam a matsayin jarrabawa a gare shi a cikin wannan rayuwa ta duniya. Kuma, bisa yalwar sani da iliminsa ya tsara wannan  jarrabawa cikin mafi kyawun tsari da hikima. Mutanen da ke fuskantar al’amura ta mahangar Alkur’ani su ne suke fahimtar sirri da hikimar Allah a halitta kuma suke la’akari da al’amuran rayuwa da a ke jarrabar mutane da su. Amma su kuwa irin mutanen da suka nisanta daga hasken koyarwar Alkur’ani suna rayuwa ne cikin duhun jahilci a kan hakikar wannan al’amari na halittar Allah.

Saboda haka, shi dai wannan rai da mu  ke jin namu ne to cewa ruhi ne na Allah. Sai dai kuma hatta yadda mu ke ji da da’awar cewa ran namu ne, to yana daga cikin al’amuran ban mamaki da ke nuna hikimar Allah a cikin halitta da tafiyar da al’amuran halittar, amma wanda ya ke da hankalin fahimtar hakikanin hikimar halittar shi ke iya gane hakan.

Duk lokacin da wani al’amarin dadi da farin ciki ya fado mana a rai, duk da yake mu kan ji kamar yin kanmu ne, bai kamata mu manta da cewa Allah ne ya sanya mana shi saboda son Sa gare mu ba. Duk wani tunani ko al’amari da ya darsu a zukatanmu to ya samo asali ne daga ruhin Allah wanda ya sanya a jikinmu. Allah ne ya so kuma ya hore mana har mu ke jin cewa mu ne ke da ikon rayukanmu. Mu kan yi kura kurai wajen fahimtar hakikanin al’amuran da ke kundin kwakwalenmu. Amma dai gaskiyar lamari shi ne, ruhi ko rai da Allah ya hura wa mutum shi ne tushen soyayya, tunani, jin tausayi, nuna kauna da son juna, son abu mai kyau da kuma gane kyakkyawar dabi’a da mu ke yi a halin rayuwarmu.

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22161/allah-ya-yi-busa-ahttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22161/allah-ya-yi-busa-aSat, 27 Mar 2010 08:38:33 +0200
HAKIKA RAYUWAR WANNAN DUNIYA TAKAITACCIYA CEMafi yawan  mutane sun dauki wannan rayuwa ta dunya matabbata, wato tamkar ba za su mutu ba, don haka ma ba su damu da bin ka’idojin addini ko su yi tunanin mutuwa da ranar lahira ba. Amma kuma ita wannan rayuwa ta duniya da suke shantakewarsu a cikinta, takaitacciya ce ainun kuma mai shudewa. Duk irin tsawon kwanakin da mutum ya samu a duniya wata rana mutuwa sai ta riske shi. Kai ko ban da wannan, rayuwar duniya ta saba yadda duk muke tsammaninta. Allah ya  yi bayanin wannan al’amari ga bil-adama a wurare da dama a cikin Alkur’aninsa mai girma:

(Allah) zai ce, “Tsawon shekaru nawa kuka zauna a duniya?” Za su ce,  “Mun zauna ne tsawon rana guda ko yankin rana. Ka tambayi masu lissafi!” Zai ce, “Kun zauna ne na dan lokaci, in har kun san haka!” Shin kuna zaton mun halicce ku ne don wasa, sa’annan kuna zaton ba za ku dawo garemu ba? (Suratul Mu’minun, aya 112 – 115)

Ranar da Alkiyama za ta tsaya, masu laifi za su yi rantsuwa cewa ba su zauna (a duniya) daidai da awa guda ba. Kamar haka suka kasance ana rudar da su.” (Suratu Rum, aya ta 55)

Abin da ya gabata cikin wadannan ayoyi da aka kawo a sama wata muhawara ce da za ta gudana tsakanin mutane in an taru a ranar hisabi. Kuma kamar yadda muhawarorin suka nuna, bayan mutuwa mutane za su gane cewa sun zauna a duniya na dan lokaci kalilan. Wannan kuwa shi ne tsawon shekaru sittin ko saba’in na rayuwar mutum a dunya, wanda a gajartarsa kamar kwana daya ne kawai ya yi a cikin duniyar, ko kuma kasa da kwana daya. Wannan kuwa daidai yake da misalin mutumin da ya shafe watanni ko kuma shekaru a cikin mafarki, amma bayan ya farka sai ya fahimci ashe mafarkin nasa bai wuce ‘yan dakikoki ba ne kawai.

Da mutum zai yi dogon tunani da nazari, da zai iya gano cewa hakika rayuwar wannan duniya ba matabbata ba ce. Alal misali, kowane mutum yana da buri da manufofinsa na rayuwa da yake tsarawa kansa, kuma an san mutum da yawan burace buracen duniya marasa iyaka da ba sa karewa matukar mutum yana numfashi. Kamar yadda yake, mutum ya kan kammala karatun babbar sakandare, daga nan sai ya shiga jami’a, sannan bayan ya gama ya kama aiki a kamfani ko wata ma’aikata. Ka ga wadannan duk suna daga cikin burukan dan-adam. A rayuwar kuruciya, za ga yayin da ba a zaton matashi ya riski shekaru talatin a duniya, amma kafin wani lokaci sai a wayi gari ya kai shekaru arba’in.

Kasancewar rayuwar duniya takaitacciya al’amari ne da Allah Ubangiji ya yi bayaninsa ga bayinsa a cikin littafinsa mai hikima ta yadda kowane mai numfashi zai iya fahimtar al’amarin. Don haka, ga wadanda suka fahimci wannan gaskiyar lamari kan rayuwar duniya, sun san cewa muguwar dabara ce mutum ya shagalta da wannan rayuwa ta duniya mai yankewa, har ya mance da rayuwa ta hakika da dauwama, wato lahira. Daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma wadanda a cikinsu Allah ya gargadi mutane a kan rashin dauwama da kurewar rayuwar duniya sun hada da:

Ya ku mutanena! Rayuwar wannan duniya jin dadi ne kalilan. Gidan lahira shi ne gidan dauwama. (Suratul-Gaahafir, aya ta 39)

Wadannan mutane suna kaunar rayuwar wannan duniya, sai suka mance da (tunanin) mashahuriyar rana. (Suratul- Insan, aya ta 27)
]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22160/hakika-rayuwar-wannan-duniya-takaitacciyahttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/22160/hakika-rayuwar-wannan-duniya-takaitacciyaSat, 27 Mar 2010 08:25:21 +0200
A KODA YAUSHE A KAN GA FARIN CIKI A FUSKOKIN MUMINAI WANDA KE BIJIROWA SABODA SANIN CEWA KOWANE ABU AN HALICCE SHI NE AKAN MANUFAAllah ya halicci kunci ko jarrabawa a rayuwar duniya ta yadda sai bayinSa da ke aiki da hankula da kwakwalensu ke samun rayuwar farin ciki. A cikin hikimar wannan jarraba akwai kyakkyawa kuma sassaukan tsarin manufa mai saukin fahimta da sabuntawa. Amma wadanda ba sa yin duba da idon basira, irin wanda Allah ya bayyana mana a cikin Alkur’ani, wadanda kuma ba sa lura da abubuwan da suka zo a cikin Alkur’anin, ba za su iya fahimtar wannan sassaukar manufa da ke boye cikin jarrabawar ba. Saboda haka suke shafe yawancin rayuwarsu cikin yanayin kunci da tashin hankali; wato rayuwa marar amfani mai cike da yawan damuwa da bakin ciki. Duk lokacin da wadannan mutane suka sami kansu cikin mawuyacin hali, su kan dube shi a matsayin bala’i da ba shi da magani ko mafita. Tabbas irin wannan tunani yana nuna fita daga hayyaci da toshewar basira, wanda tasirinsa kan sanya masu wannan siffa su debe kauna ta yadda ba sa zaton samun kansu cikin wani yanayi daban sabanin wannan mawuyacin da suke ciki.

Amma hakikanin lamari shine, duk wanda fahimtarsa ga jarrabawa da kunci na wannan rayuwa ta duniya tana bijirowa ne daga mahangar Kur’ani, to ba za ka taba ganinsa cikin rudu da daburcewar al’amura ba, ko ka gan shi kullum cikin kunci da tashin hankali irin na rashin nutsuwar zuciya ba. Akwai wasu al’amuran hakika wadanda duk mutumin da ya yi imani da Allah zai gaskata su kai tsaye. Wannan ilimi kan taimaka wa mai imani wajen yanke hukunci da ya dace da kyakkyawar koyarwar Alkur’ani ta hanyar yin amfani da tunaninsa. Bayanan hakika na Kur’ani su kan yi tasiri ga wanda ya gaskata su a dukkan al’amuransa na yau da kullum. Idan mutum ya ci karo da matsaloli ko wahalhalun rayuwa, to tunda kuwa ya gina rayuwarsa ne akan koyarwar Alkur’ani mai tsarki, babu wata jarrabawa, wahala ko kunci a fadin wannan duniya da zai hadu da su, duk kuwa tsanani da girmansu, face sai sun zo masa da sauki kuma ya sami maganinsu. Irin al’amuran rayuwar da ke haddasa mummunan bakin ciki, da bacin rai ko tashin hankali da kuma da-na-sani ga mutanen da babu darsashin imani a zukatansu, a hakikanin gaskiya su kan sanya nutsuwa da farin ciki ga ma’abota imani, da yake sun yi riko da kyakkyawar mahanga.

Kamar yadda a ka bayyana a sama, dalilin samun wannan sabanin fahimta ta mahanga a tsakanin muminai da  marasa imani shine saboda su muminai sun kasance masu ilimi da kuma bada gaskiya da abin da ke cikin Alkur’ani mai girma. Hakan kuwa ya kasance ne saboda sani da kuma imaninsu akan cewa:

• Allah iliminSa ya game komai,

• Allah mai matukar adalci ne,

• Allah shi ya halicci duk wani abu da ke bayan kasa, babba ko karami,

• Allah mai matukar jinkai ne, mai son bayinSa da yin gafara gare su

• Allah yana amsa dukkan rokon bayi a gare Shi da mafi kyawun sakamako,

• Allah yana fitar da bayinSa daga halin kunci da masifa,

• Mika al’amuranmu ga Allah Ubangijinmu, masani mai tsananin hikima da adalci, da rahama da soyayya ga bayinSa, it ace hanyar lumana,

• Mutane suna rayuwa ne kan abin da aka kaddara musu, kuma koda za su rayu a duniya marra dubu, ba za su wuce kadarinsu ba wanda Allah masanin halitta ya tsara musu,

• Duk abubuwan halitta da mutane suke gain a sararin duniya ba zaman kansu suke yi ba; komai nasu yana gudana ne da umarni da kuma ikon Allah da ya kage su,

• Allah shi ke azurta muminai ya kuma hore musu hikima da mafita a dukkanin al’amura,

• Kyakkyawan al’amari ko mummuna yana zuwa ne daga nufin Allah, mutane ba su da iko akan tunkude sharri ko jawo alheri akansu,

• Bai halatta ga mutane su rika gaba da junansu ba, domin cewa su kaskantattu ne kuma raunanan halitta wadanda ke rayuwa a bisa iko da kaddarawar Ubangiji, kuma ba su da ikon yin komai sai abin da ya nufe su da shi,

• Mika wuya ga Allah da bada gaskiya da hukuncinSa, da yin nazarin falala da kuma hikima a cikin al’amarin halittu, wajibi ne kamar yadda Alkur’ani ya bayyana,

• Haka nan kuma, babu batun bakin ciki, da kunci ko debe kauna a tafarki na koyarwar Alkur’ani,

• Tashin hankali da wahalhalu su kan kasance wata rahama ce ta fuskar samun lada a ranar lahira, kuma nuna juriya a halin wadannan wahalhalu alama ce ta karfin imani,

• Ya zo a cikin Alkur’ani cewa za a jarrabi masu imani da tsananin al’amura a rayuwa, saboda haka wahalhalun da mutum ya sami kansa ciki gaskatawar abin da ayoyin Kur’ani suka nuna ne,

• Gurace guracen duniya makiya ne da ke halakar da mutum. Don haka yakar son zuciya saboda imani da fifita son Allah akan komai yana samar da babban matsayi a gurin Allah,

• Shaidan ya yi alkawarin batar da mutum, don haka yake yin amfani  da alatun duniya don ya shagaltar da masu imani. Sai dai kuma Allah ya tsare musulmi daga fadawa tarkon rudinsa,

• Bala’i da wahalhalu da ke samun muminai a rayuwar wannan duniya su kan kasance wata dama ce gare su don jaddada soyayyarsu da kuma mika wuya ga Ubangiji,

• Yardar Allah ta fi kowace iri baiwa ko ni’ima da mutum zai samu a wannan duniya,  yayin da kuma Allah zai tabbatarwa da masu imani rayuwar farin ciki da nutsuwa wadda ta zarce duk wata ni’imar duniya da za su samu.

Koda mutum ya kasance mafi farin jini a duniya kuma koda ya mallaki komai na rayuwa irin wanda ransa yake so, duk da haka zai iya kasancewa  ya rasa kwanciyar hankali da jin dadi idan – Allah ya kiyaye – Allah yana fushi da shi. Amma kuwa in ya rungumi rayuwa da dabi’a masu kyau wadanda ya san Allah ya yarda da su, sannan ya dage a kan imani da mika wuya ga Allah da kuma sallama al’amuransa gareshi a cikin kowane irin yanayin rayuwa da ya sami kansa a ciki na kunci ko wahala, to wannan zai more rayuwar farin ciki da aminci da bai taba samun irinta ba a rayuwarsa, koda kuwa sauran mutane suna kin sa. Kuma a kan gane mutumin da ke cikin irin wannan rayuwa ta zahirinsa da kuma yanayin tunaninsa. Muhimmai daga cikin wadannan alamomin da a kan gane shi sun hada da:

• A kan ga alamun farin ciki da hasken imani a fuskarsa.

• A kan ga yanayin farin ciki, tunani da kuma babi’arsa ba sa canjawa a cikin halin ni’ima ko kunci.

• Ba a ganin alamun kasawa a magana da dabi’unsa. Ba ya furta kalaman da suka sabawa koyarwar Alkur’ani, ko nuna halayyar rashin imani da yin tawaye ga Allah mahalicci. Haka kuma ba a jin lafazan debe kauna da gushewar tunani wadanda suka sabawa Kur’ani, a cikin kalamansa.

• A kullum halayyarsa ta da’a ce ga Allah Ubangiji, kuma kyawawan dabi’unsa koda yaushe su kan nuna tsantsar imani da mika wuyansa ga Allah, kamar yadda ya  ke da imani a kan cewa akwai amfani da manufa a cikin halittar kowane abu, da kuma cewa mutane da gabadayan al’amura suna karkashin iko da kulawar Allah mahalicci mai taimakon muminai.

• Ya yi imani da cewa rayuwar wannan duniya takaitacciya ce (kamar cin kasuwa), inda kuma rayuwar lahira ita ce matabbata ga masu imani. Saboda haka ba ya damuwa ko ya yi bakin ciki saboda rashi ko hasarar wata ni’ima ko kayan alatun duniya. Sannan ya yi imanin cewa abin da ya rasa na ni’imar rayuwar duniya zai zame masa alheri ne a lahira. Sakamakon haka duk wani kunci ko masifa da ta same shi a nan, ni’ima ce gare shi a can.

• Duk irin tsananin hasara ko kunci da ya shiga, zuciyarsa tana cike da dangana da kyakkyawan fata na samun soyayyar Allah da kuma yardarsa, wanda samun wannan ya fi masa samun duk wata ni’imar duniya.

• Mutumin da ya san kowane abu da manufa a ka yi shi, kuma ya san cewa jarraba da kunci suna zuwa ne daga Allah, sannan ya fuskance su da imani da tawakkali zai kasance mai nuna soyayya ga sauran halittu. Tun da yake ba a raba mumini da adalci, tare da farin ciki da son daidaito, don haka ya kan kauda kai da yin afuwa ga wadanda suka cuce shi ko suka ci zarafinsa ta hanyar nuna kauna a gare su. Babu abin da ke kautar da shi daga kan koyarwar Alkur’ani, don haka fushi da kiyayyar mutane ba sa yin rinjaye a kansa. Ya san cewa kura kuran da mutane  ke aikatawa haka Allah Ubangiji ya kaddaro musu don a nuna musu su gane gaskiya. Shi ya sa ba a ganin mummunan nufi a cikin mu’amalarsa da sauran mutane. A sabanin haka ma, saboda zurfin imanisa a koda yaushe ya kan nuna soyayya da tausayawa a dukkanin mu’amalolinsa da sauran mutane.

]]>
http://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/21393/a-koda-yaushe-a-kanhttp://ha.evolutiondeceit.com/ha/Makalai/21393/a-koda-yaushe-a-kanFri, 05 Mar 2010 19:49:03 +0200
iddialaracevap.blogspot.com ahirzamanfelaketleri.blogspot.com ingilizderindevleti.net